← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 165

Sashe 71

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

tana kallon Abba, sai kuma tace "Haba Alhaji, Haba Alhaji...." Dakatar da ita Abba yayi a fusace yace "Bana son jin komai daga gareki, ki tashi ma ki fita" Umma ta ja bakinta tayi shiru, cike da bacin rai Abba na kallon Nihad yace "U think i brought u here to ask for ur opinion? Is that what u think?" Abba ya girgiza kai cike da takaici yace "You are nothing but a disappointment to me Nihad, i regret having u as a child...." Kuka kawai Nihad take tana jin kamar a mafarki wai ita Abba ya mara kuma yake gaya mata wannan maganganun, wanda ko fada bai ta6a mata ba tunda aka haifeta, Strictly Abba ya ci gaba yace "Kuma in har ba so kike inyi disowning dinki ba baki da miji da ya wuce Ibrahim, kuma dolenki kiyi masa biyayya ki bisa, idan ko ba haka ba ki nemi wani uban ba ni ba, sannan idan ba shi ya dauko ki ya kawo ki gidan nan ba bana son in ga kafarki a nan ko da kuwa xa ayi shekara ne bai kawo ki ba, ki sa a ranki baki da wani a yanxu banda shi, shine gatanki, shine komai naki, samun kwanciyar hankalin ki a rayuwa ki bi sa, ko mu da muka haifeki yanxu bamu da iko da ke sama da shi" Kuka kawai Nihad take xuciyarta na mata xafi, ita fa she still can't believe Abbanta ne ke gaya mata wa ennan maganganun, Abba na kallon Khalil da ya sunkuyar da kansa yace "Kai kuma Ibrahim ina me baka umarni in har Nihad xata kawo maka iskanci ko raini ka zaneta, ni na baka wannan umarnin ba wani ba" Khalil dai bai dago kansa ba, Abba yace "Shikenan kiran dama, xa ku iya tafiya" Da kyar khalil ya iya dago kai yace "Nagode Abba, Allah ya kara girma" Abba yace "Ameen" mikewa yayi yana kallon Umma yace "Sai anjima" Umma ta dinga harararsa, shi dai ya nufi kofa, ganin Nihad ta ki tashi sai kuka take kamar ranta xai fita Abba ya daka mata tsawa yace "Tashi ki bar min gidana, useless girl" Tashi tayi da sauri tana kuka sosai ta nufi kofar ita ma, sai kuma ta juyo cikin rawar murya tace "Abba makaranta na fa?" Abba yace "Sai abinda mijin ki yace, don shi ke da iko dake yanxu, don in xai dau shawarata ma babu ke babu makaranta har abada, maza bi sa ku bar min gidana" Khalil dake jin Abba ya fita daga parlon ta bi bayansa tana kuka sosai, shi dai ko kallonta bai yi ba ya fita xuwa gun mota, Aminu sai wage ido yake yana jiran fitowar Khalil, yana ganinsa ya fito kuma ya shige mota, Nihad ta bude bayan motar ta shiga ta hade kanta da gwiwa tana shessheka tana jin kamar numfashinta zai dauke, Khalil na isa gate Aminu yace "Ina ta jiranka" Khalil yace "Xan zo da daddare" Aminu ya washe hakora yace "Toh toh sai ka zo" Da gefen ido ya dinga lekan Nihad dake bayan mota, khalil ya ja motar suka bar gidan. Sai kusan karfe shidda suka isa gida, Khalil na parking ya sauka ya tafi ya kulle gate sannan ya dawo ya kashe motar, har sannan Nihad bata dago kanta da ta kife a bayan motar tana kuka ba, tana jin ya kashe motar ta bude side dinta ta sauka, gaba daya ta jike hijab dinta da hawaye har a sannan kuma ba daina kukan tayi ba, ta fara tafiya towards the building of the house, ji tayi ko ina na juya mata a ido, Rufe motar khalil yayi da sauri ya nufeta ganin abinda take, amma kafin ya isa inda take tuni ta kai kasa, ba karamin faduwa tayi a wajen ba, ya zura makullin hannunsa cikin aljihu da sauri ya durkusa gabanta ya dagota amma tuni tayi pass out, daukarta yayi ya nufi cikin gidan da ita.
Chapter 71 · 0% Book details