← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 165

Sashe 112

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

+2347057607751✍🏻Husnah ce tayi zaman dirshan a kitchen din dake malale da ruwa, gaba daya ta jike jagab daga saman cikinta har xuwa ƙafafuwanta, ta wawwara hannu ta runtse ido cikin daga murya tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Wayyoo na shiga uku na lalace, gaba daya na kone a jiki... Don Allah a kawo min agajin gaggawa" daga gefenta tukunya ce dauke da ruwan zafi a ajiye, Khalil ya shiga kitchen din da sauri yace "Me ya faru haka?" Ta bude ido ta fashe da matsanancin kuka tana kallonsa tace "Don Allah ka taimakeni wallahi, ruwa me uban zafi ne ya kwaro min gaba daya tun daga cikina har kafa, taliya naje zan zuba ruwan ya kifo min, don Allah ka kawo min agaji kar jikina ya toye" Da mamaki Khalil ke kallonta, kuka kawai take tana jijjige kafarta da hannu tana cewa "Wayyo Allah na, wllh ruwan ya tafasa sosai, don Allah a taimakeni duk radadi jikina yake min" Khalil yayi ma kofar kitchen din kallon kasa kasa jin kamshin Nihad, ya ganta tsaye bakin kofar, bai yarda ya kalli fuskarta ba, ya kashe gas din ya karasa kusa da Husnah ya mika mata hannu yace "Taso" Karaf ta cafke hannunsa ya dagota ta mike tana kara sautin ihunta tana cewa "Wayyoo mamata, Wayyoo zafi, na shiga uku me za a shafa min ya daina min wannan radadin da nake ji..m" Hanyar kofar kitchen din ya nufa da ita still ya ki kallon Nihad, ita kanta Husnah bata kalli Nihad ba sai gunjin kuka take tana jijjiga kai tana yi tana runtse ido, ganin Nihad ta ki matsawa daga kofar kitchen din Khalil ya daga kai a karo na farko ya kalleta, rungume hannu tayi tana kallon su, yace "Matsa a hanya" Ta zabga masa wani ta juya da sauri ta bar wajen ta wuce dakinta, Husnah ta bi Nihad da kallon gefen ido tana cewa "Don Allah a taimakeni kar jikina ya kwaile in ma asibiti ne mu je" sai kuma ta zame hannunta daga nasa tayi dai dai a kasa ta kwanta tana birgima tana kuka, dakinsa ya nufa ta bi sa da kallo, sai ga shi ya fito da makullin mota yana kallonta yace "Mu tafi asibitin" tana girgiza kai cikin kuka tace "Wallahi baxan iya tashi ba" Yace "Toh kira kawarki" Daga haka ya fita ya je parking space ya tada mota, Mikewa Husnah tayi tana gunjin kuka ta tattale hannu ta bi bayansa, tuni ta isa gun motar tana cewa "Don girman Allah mu yi mu tafi asibitin kar na mutu, ko ina zugi yake min" Ya bude mata back seat ta shige ciki, Tun da ya tada motar Nihad ta fito parlor ta tsaya jikin window tana kallon su, sai da ya bude gate ta ga ya dawo zai shiga motar kawai ta fito ta nufi front seat ta shiga ta kulle, ya bude gefen mazaunin driver yana kallonta da kyau yace "Ina za ki?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Asibitin da za ku" Ya kalleta daga sama har kasa yace "Ohk, haka za ki je asibitin kenan" Fuska daure tace "Sai ka jira ni in dauko mayafina" Daga haka ta fice daga motar da Husnah ta cika da ihu kamar warce ake gunduwa gunduwa da namanta, tana ganin Nihad ta sauka tace "Don ya Rasulullahi ka ja motar mu tafi kar a rasa fatar jikina, wllh jin jikin nake kamar ba nawa ba, kar fatana ya karasa zagwanyewa" Bai ce mata komai ba ya shiga motar, amma bai ja motar ba, sai ga Nihad sanye da Hijab ta shige gaban motar, ya ja motar suka fita gidan ya sauka ya kulle gate. Wani asibiti da babu nisa daga anguwansu ya kai ta, duk nurses suka tattaso da sauri saboda tun daga Gate ihun Husnah ya cika asibitin, Nurse daya na kallon Khalil tace "Me ya sameta?" Khalil da ya koma gefe ya tsaya yace "Wai konewa tayi" Nan aka shiga da ita emergency aka dau scissors za a fara barke riga da wandon jikinta, Nihad dai na reception din hospital din ta zauna, babu wanda zai ce tare suke, Khalil kuma na kofar shiga reception din ya jingina da bango ya rungume hannunsa, wani ihu Husnah ta sakar ma nurses da Dr din tace "Don Allah a kira min yayana ya zo kila mutuwa zan yi, a kirasa ya zo kusa da ni" Wata Nurse ta fita ta kira Khalil, yana kallonta yace "Me xan yi a can din?" Rai bace Nurse din tace "Haba bawan Allah ko da baka santa ba ta bukaci ka je ai ko don saboda condition da take ciki zaka je, wai ko ba matarka bace?" Daga haka ta juya ta koma emergency ward din, Khalil ya bi ta da kallo kafin ya shiga asibitin ya bi bayanta, Nihad ta bi sa da wani kallo, bai ma san tana yi ba, yana tsaye bakin kofar ward din Husnah ta hangosa ta dinga miko masa hannu wai ya zo ya ceceta kar ta mutu, likitan da Nurse dai sun gama 6arke kayanta da scissors suna neman inda ta kone, Can likitan ya kalli Khalil da ya ki karasawa ciki yace "Wani irin ruwa ne ya zubar mata?" Khalil ya buda ido yace "Ban sani ba fa, ko kafin na fito ruwan ya gama kwararewa a jikinta" Nurse din na kallonta tace "Ruwan zafi ne ko dai ruwan dumi" Husnah ta hade rai tace "Ban gane ruwan dumi ba, sharrin zan ma kaina ince ruwa zafi ya zubar min a jiki bai zuba ba, kawai dai dama fata iri iri ce, amma Allah kadai yasan zugi da radadi da nake ji yanxu haka, har cikin raina nake jin wannan axaban wallahi" Tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka, likitan ya cire safan hannunsa yace "Nurse ki basu magunguna" Yana kai wa nan ya fice daga ward din, nan nurse ta fito reception ta harhada magungunan ta dawo ta mika ma Khalil Bill din dubu sha biyar, amsa yayi ya fiddo Atm card dinsa ya mika ma nurse din, daga baya ta sake dawowa ta bukaci pin dinsa sannan ta juya, Husnah dai sai gunjin kuka take tana kallon wata nurse dake mayar da kayan aikinsu mazaunin su tace "Aunty Nurses babu wani abu da za a shafa min?" Nurse din tace "An rubuta maki magani da za ki sha, Allah ya sauwake" Daga haka ta fita, Nurse din ta kawo ma Khalil magungunan tana kallon Husnah tace "Allah ya kiyaye gaba, za ku iya tafiya yanxu ga magunguna da prescriptions a jiki" Daga haka ta juya ta bar wajen, Khalil ya daga kai ya kalli Husnah, share hawayenta tayi ta sauko daga kan gadon da take a hankali kamar me gudun kar ta fama wani ciwo a jikinta, duk sun yayyaga mata kayanta wandon ne kawai basu karasa ba, amma daga saman cikinta duk a bude yake, Khalil zai juya ya bar wajen cikin kuka tace "Wallahi baxan iya tafiya ba ko Nihad ce ka turo ta kama min hannu" Har ya fara tafiya sai kuma ya dawo, da sauri ta karaso kusa da shi ta kama hannunsa, ya dake ya fara tafiya tana dingishi tana bin sa har suka fito reception din, har suka isa mota Husnah ta shiga baya ta zauna Nihad bata fito ba, Khalil na tsaye jikin motar for almost 5 mins ganin bata fito ba still ya koma reception din, hade rai yayi yace "Malama ke muke jira" Ko Kallonsa bata yi ba ta tsura ma Tvn dake aiki a reception din ido, yace "Ohk ga kudin mota duk sanda kika zaman sai ki dawo gida" Ya ciro dari biyar ya mika mata, zuwa lkcn nurses din sun fara kuskus ko kishiya da kishiya ne, can ta mike ta fice daga reception din fuskarta a daure, juyawa yayi ya bi bayanta sai yaga ta bude front seat ta shiga, ya shiga motar shi ma suka bar asibitin, suna hawa saman titi Nihad tace "Hostel za a kai ki ko ina?" Husnah tace "Wallahi kin bani mamaki Nihad har in kone a gidanki amma ki kasa budan baki ki min sannu? Sai yanxu ki wani bude baki kice hostel xa a kai ni ko ina?" Nihad tace "Saboda ai sai da nace ki bari in dafa kika ki, Yanzu idan wani abu da yafi wannan ya sameki su Mumy da Abba suka ji bayan sun hana in kawo kowa gidan fa? What did u want me to tell my parent? Ni yanzu dai hostel za a kai ki ko ina, kin dai ga dare yayi" Khalil yace "Kinsan dare yayi kike kira mata hostel yanzu? Ba kwana ta zo maki ba dama?" Nihad ta wani jefa masa kallo tace "Ni bata ce min zata kwana ba, salon mu koma gida wani abu da yafi wannan ya sameta in shiga uku? Kawai ta koma hostel ko gobe sai in kai mata jakarta can din" Kallon Nihad kawai Khalil ke yi, Husnah tace "To baxan wani je hostel ba jakana na gidanki kuma ID card dina na ciki, kuma ai soyayya ce tasa na zo gidanki ba wani abu ba, me yasa su Naf da Zully basu zo ba, amma ba komai Nagode da walakancin da kika min Nihad" Khalil dai ya nufi hanyar gida, bayan ya shiga ciki yayi parking Nihad ta bude motar ta sauka ta wuce ciki, Husnah ta sauka ita ma ta shiga gidan Khalil ya bi su da kallo, jingina yayi da motar ta ta6e baki. Husnah na shiga dakin Nihad ta fashe da kuka sosai tace "I never expect this from you, in wani yace min zaki min haka wallahi baxan yarda ba, saboda wannan mere Drivern ya taimakeni ya kai ni hospital kike jin haushi Nihad?" Nihad tace "Ya baxan ji haushi ba mutumin da ko magana bana yi masa za ki ja min raini a wajensa ya zata ya mana alfarma, ko kadan i am not happy with what happened da kawai kirawoni kika yi na fita waje na nemo mana taimako akan wannan yaron da kika kula, yaron da ya tsaneni nima na tsanesa shine har zaki yarda ya wani kai ki asibiti?"
Chapter 112 · 0% Book details