Sashe 49
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
mata? To wllh ka shiga hankalinka, ba ruwanka da harkana ko lamarina a gidan nan ina sake ja maka kunne" Farooq dai sai kallonta yake, can ya juya a fusace ya bar wajen, Umma ta bi sa da harara, Hafsah ce ta shigo parlon da leda a hannunta, Umma tace "Makira sai yanxu kika ga dama kenan, to kin kyauta kin ji ko? Ki tafi can parlona a sama ki jirani in xo in sameki ki gaya min gidan uban da kika je" Hafsah tace "Zan kai ledar kitchen" Umma tace "Aa wuce da shi sama, xa mu hade da ke a can" Hafsah bata ce komai ba ta wuce sama xuwa bangaren Umma, Nihad ta kai masu abincin da Mumy ta gama hadawa, wani tray kuma ga meat pie, samosa, spring rolls da doughnuts da Aunty Jamila ta kawo bayan Mumy tayi mata waya ta gaya mata tayi ta kawo, da yake tana da ma'aikata cikin kankanin lokaci suka yi suka gama, wani bowl me dauke da apples kusan goma ta kai masu a karshe ta ajiye, sannan tayi serving dinsu abincin. Bayan sun gama cin abincin, Nihad ta shigo parlon tare da Ya farooq, bayan ya gaisa da su ya fita, Mujahid ya mike yana kallon Aliyu yace "Bani makulli in dauko wayata a mota, they might be plenty of calls i missed" Aliyu ya mika masa makullin ya amsa ya fita, Nihad dai kallonsa kawai take, wayarsa ya ciro a aljihu ya shiga gallery bayan few seconds ya mika mata, ta amsa tana kallon screen din wayar, sosai gabanta ya fadi, ta dai yi shiru bata ce komai ba, yace "You promised kin daina dukka ire iren outing din nan, so where did this come from?" Nihad ta marairaice tana kara kallon hoton, 4 weeks ago ne suka je wani babban restaurant da su Naf da Husnah da samarin su, shine aka yi hoton a can, wando ne a jikinta sai crop top me shegen kyau da tsadadden sneakers a kafarta, sannan ta daura baƙin dankwali a kai ta xubo dogon gashinta, su Husnah ma duk ire iren shigar suka yi a hoton... jin tayi shiru Aliyu yace "Why are u quiet?" Ta daga kai ta kallesa a hankali tace "Hoton nan ai ya dade" Yace "Karya kike, this is a recent pix, jiya da daddare Naf ta daura a status na gani nayi saving" Nihad tace "Am serious ba kwanan nan muka yi ba, kuma ai kafin in maka alkawarin daina fita tare da su ne muka yi hoton nan, ka tambayi Naf din ma" Yace "Nihad!!" Shiru tayi tana kallonsa gabanta na faduwa, yace "Saboda ina sonki da aure ya sa ki ka ga har nake hanaki abubuwan nan da kike, banda haka i have no business with ur life style, quite alright kinsan i have other babes wa enda muke tare da su har yanxu, but ban ta6a daga kai na hana yarinya yin abinda tayi niyya ma rayuwarta ba, ban ta6a hanasu holewarsu yanda suke so ba, but ke saboda intention dina a kanki daban shi yasa nake hanaki duk wannan shiriritar da kike, Upon how wealthy my parents are, baxa su ta6a yarda in kawo masu mace mara kamun kai ince xan aura ba, baxa su ta6a amincewa, kuma ya kamata ki kara yarda yanxu tunda har na tako tun daga Abuja na xo gidanku to da gaske aurenki nake son yi, i will neva do that for any lady, sai sai idan dama ina da wata sabgar da xanyi a kano.... Nihad this should be ur last warning!!!" A hankali tace "Toh kayi hakuri, in sha Allah hakan baxai kara faruwa ba, i am promising u this" Yayi shiru yana kallonta, tace "Wllh da gaske nake baxan kara ba" Yace "Toh Allah ya sa..." A hankali tace "Ameen" Yace "Kince min driver din a nan yake zama" Nihad ta gyara xama tace "Ehh wllh, yanxu haka ma yana nan, ai yana kofar gida sanda ku ka shigo layin shi ne ya shiga cikin gidan" Aliyu dake ta kallonta yace "Da muka shigo layin ne ya shiga ciki?" Tace "Aa ai sannan baku karaso ba" Yace "Ohk where is he now?" Nihad tace "What will happen now, kawai mu fita sai ka xauna a compound ni kuma xan je in samesa a can boys quarters da yake zama, ince xan je karbo sako ya xo ya kai ni, daga nan idan ya fito compound xaka gan shi" Aliyu yace "Kamar wasan yara... But i urgently wants to see him" Nihad tace "Noo, ta haka kadai xai fito compound har ka gansa, so now let's go outside" Tashi tayi ta dau bowl din apples tace "Bari in kai maka wannan ka dinga ci" Daga haka ta fita, ya mike ya bi bayanta suka fito compound din, can karkashin thatch dake dauke da kujeru ta kai masa apples din ta ajiye saman table, ya xauna yana kallonta yace "Kin yi kyau" Tayi wani blush tace "Thank you, bari in je in samesa yanxu" Yace "Ohk" Hanyar Chalet ta nufa ya bi ta da ido har ta bace, ya kalli agogon wrist dinsa dake nuna hudu saura, Nihad na isa chalet din ta hade rai tana lekan parlor, isiya ta hango yayi dai dai kan kujera yana ganinta ya mike da sauri ya fito yace "Kaya xa a amsa Hajiya?" Tace "Ina wannan yaron?" Yace "Wani yaro?" Tace "Halilu" Isiya ya ɗan gwale ido a ransa yana kara nanata yaro da tace, can yayi saurin cewa "Yana can daki" Tace "Toh kaje ka kirasa Mumy ta bada sako a basa" Juyawa yayi yace "Toh Hajiya" Ya fi minti daya yana kwankwasa kofar dakin da Khalil yake ciki amma bai bude ba, shi dai yasan baya baccin rana balle yace, to ko kila yana bandaki, bai yi gigin bude kofar ba tun ranan da Saminu yayi masa haka yayi cutting din masa warning me lafiya, Bude kofar aka yi khalil na kallonsa yace "Ya aka yi?" Isiya yace "Aa dama mamarsu Sudais ce ta bada sako wai xa a gaya maka a waje" Khalil yace "Ohk" Fita yayi tun daga cikin parlor ya hangota, yana fitowa ya tsaya bakin kofa yana kallonta, Tana yatsine yatsine tace "Yauwa xaka yi dropping dina in amso sako yanxu, kaje ka dauko makulli ina jira" Juyawa yayi ya koma ciki ba a dau lkci ba ya fito rike da makullin motar, yana kallonta ya mika mata, ta hade rai tace "Meye kake mika min makulli cewa nayi ajiye ni xaka je kayi in amso sako ko kai kurma ne" Ya ajiye makullin saman matakalan chalet din yace "Toh baxan je ba, wanda ya daukeni aikin ma ya daga min kafan aiki yau...." Ya juya xai koma cikin parlon yace "Shi saurayin naki ya kai ki ki amso sakon...." Kasa cewa komai Nihad tayi ta bi sa da kallo, ta fi minti daya tsaye a wajen kafin ta juya ta koma gun Aliyu rai a bace.... Murmushi Aliyu yayi bayan ta sanar masa yanda suka yi da Drivern yace "Ohk, there is next time, xan kuma sauke masa girman kan da ke yaudaransa" Nihad tace "Toh wai dama talaka na irin wannan girman kan? Wllh sai ka xata fa gidan Ubansa ne nan din yanda yake abubuwansa" Aliyu dai bai ce komai ba, but all his thought is with the driver, he seriously want them to meet. Sai kusan karfe biyar Aliyu ya bar gidan tare da Mujahid bayan sun shiga sun ma Mumy da Umma sallama, Dollar dari biyu ya ba Nihad, yana tafiya dakin Umma ta fara shiga ta nuna mata kudin, Umma ta ja tsaki tace "Meye haka, ko dubu dari da hamsin bai kai ba, amma ya bani kunya duk wannan girke girken da ya kwasa?" Nihad tace "Umma fa a ko da yaushe cikin yi min kyauta yake, wannan ma cewa yayi inje saloon inyi gyaran gashi da shi fa" Umma tace "Toh Allah na tuba ina laifin ya baki dubu dari biyu da hamsin ma, duk kudin ubansa sannan kuma shi ma yace min yana business nasan baxai wuce exportation and Importation yake ba" Nihad bata kuma cewa komai ba, ta bude karamin jakarta dake hannunta ta saka kudin. Bayan magrib Khalil da Aminu na xaune kofar gida Aminu sai basa labarin samarin Nihad yake da irin shigar da suka yi, Khalil dai yana ta sauraronsa amma ba kallonsa yake ba, Aminu yace "Ina gaya maka wllh turarensu har bakin titi, kai kaga wani rantsattsen takalman da suka saka kuwa, kana ganin yanda suke tafiya kasan 'ya yan wasu shegu ne a kasar nan, wato barayin kasar nan" sai a nan Khalil ya daga kai da sauri yana kallonsa, Aminu ya kwashe da dariya yace "Allah kuwa, barayin gwamnati kenan" Motar da ke tahowa yasa Aminu yayi shiru suna kallon motar gaba daya don ta hasko su, Khalil ya mike kamar xai shiga gate, sai kuma aka yi kasa da fitilar motar....