← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 164 OF 165

Sashe 164

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

don wai ya mata magana ba, hijab dinta ta dauka har kasa ta saka sannan ta dau nikab ta daura, baka ganin komai sai fararen hannunta da manyan idanuwanta with long lashes ta cikin nikab din, dama kuma Aunty Maryam tace mata ta dinga yawan saka Nikab in xata fita, tana fitowa ta sauko main parlor da sauri, Aunty Hassana da ke kokarin haurawa sama ta dayan stairs din ta bi ta da kallo, tadai san duk gidan babu me saka Nikab, sai kuma tace "Keee" Da sauri Nihad ta juya amma bata tsaya ba, Aunty Hassana ta sauko daga matakala biyun da ta hau ta nufota, hakan yasa Nihad ta tsaya gabanta na faduwa tana kallonta, Aunty Hassana ta isa har gabanta ta fizge Nikab din tace "Ke wa ya kawo ki gidan nan?" Nihad ta sunkuyar da kanta, a fusace Aunty Hassana tace "Baki jin ina maki magana ne" cike da karfin hali Nihad tace "Karatu nake yi" da mamaki Aunty Hassana tace "Karatu a ina? Wa ya kawoki kiyi karatu? Ke yar uwarsu Maman Mimi ce?" Nihad ta daga kai da kyar alamar eh, Aunty Hassana ta dinga kallonta daga sama har kasa, Mimi ce ta shigo parlon jin shiru shiru Nihad bata fito ba, Mimi na kallon Aunty Hassana tace "Good morning Aunt" Aunty Hassana tace "Wace makarantar take?" Mimi tace "Makarantar mu daya?" Aunty Hassana tayi shiru tana nazarin anya ba yayanta bane aka daura ma biyan kudin makarantar? Anya ba kawota gidan aka yi don yayanta ya dinga biya mata kudin makaranta ba, Aunty Hassana tayi mitsi mitsi da ido tace "Daga wani garin take?" Mimi ta buda hannu tace "Nima ban sani ba Aunty, Mami ce ta sani" Aunty Hassana tace "Ke baki ta6a saninta a er uwarku ba?" Mimi tace "Yan uwanmu suna da yawa wa enda ban sani ba, so she might be among them" Aunty Hassana ta gama nazare nazarenta sannan ta kara kallon Nihad ta juya ta bar wajen, Mimi ta kama hannun Nihad suka fice daga parlon. The day was so hectic for Nihad don ta mance rabon da ta fita, NUN ya wuce yanda take tunaninsa, and it has always been one of her dream school don shi ta gaya ma Abba tana so amma yace Abuja yayi nisa sai yayi suggesting mata Maryam Abatcha and yayi assuring dinta she will like the school, though babu wanda ya san sunyi hakan, amma sai da taje ta gaya ma Umma which she is regretting right now, sai gashi yau she is going to be a student of her dream university amma kuma bata farin ciki da hakan, Ayman really whiled away her time a makarantar kafin Mimi ta gama lectures, sun dade suna magana da shi a waya tun bata son amsawa har dai ta fara amsa masa, shi ma saboda teasing dinta da yake ne sai tace sai ta rama, and she really enjoyed conversing with him caused he is so friendly and jovial, still tana makarantar Aunty Maryam ma ta kirata, sun kusa minti sha biyar suna waya, Aunty Maryam ta kara jaddada mata kada dai tace xata ma Ayman walakanci ta basa chance baxa kuma tayi da na sanin hakan ba, Nihad tace "Toh nagode Aunty" Daga haka Aunty Maryam tayi mata sallama, Nihad tace "A gaida min Mus'ab" Aunty Maryam tace "In sha Allah" Daga haka ta katse wayar. Sai bayan la'asar suka koma gida, tun da drivern motar yayi parking a parking space Khalil dake zaune karkashin wasu bishiyu da suka kawata makeken compound din yake kallon motar, Mimi ta sauka daga motar ta nufesa tana murmushi tace "Yayanmu good evening" Yace "How are you" tace "Alhmdlh, we are done with the registration, nan da sati biyu ne exam din ma ashe" Khalil yace "Ohk..." Juyawa tayi tace "Let me go in and take a shower" Daga haka ta juya taga har Nihad ta isa entrance din shiga cikin gidan, ta bi bayanta da sauri. Sai da suka fara shiga parlon Mami su gaisheta, kallo daya Nihad tayi ma Nadeeyah dake zaune parlon da Noor, ta dauke kai ta juya ta fita daga parlon, Nadeeyah ta kalli Noor da mamaki tace "Who is she?" Noor was speechless and astonished, ke baki yi sallama ba, kin shigo kin tadda mutane a parlor ba gaisuwa ba komai kin masu kallon tara saura quarter kin juya kin fita, Mimi ta sauke ajiyar xuciya tace "She is tired, yanzu muka dawo, it's an hectic...." Noor ta daka mata wani tsawa ta dakatar da ita tace "Pls get lost, ke da kika shigo baki yi mana sallama ba? Ko baki gaishemu ba? How dare she? Who did she think she is?" Mimi dai bata sake cewa komai ba, Noor ta ci gaba da jaraba kamar xata ari baki, Nadeeyah ta sauke ajiyar xuciya tace "Calm down Noor, kilan kamar yanda Mimi ta fada ta gaji ne, so kiyi mata uzuri...." A fusace Noor tace "Baxan yi ba, kuma wallahi na sake ganin ta shigo inda nake tayi repeating nonsense din nan da tayi i won't take it likely with her" Mimi dai ta karasa ta leka bedroom din Mami, ganin bata cikii ta juya ta bar masu parlon, Noor was still fuming with rage, Nadeeyah tace "Easy pls Noor, ya riga ya wuce ko? Stop the nagging pls" Noor tace "Nahhh bai wuce ba, i could slap her if she should repeat such kuma ba abinda xai faru" Nadeeyah tace "But who is she? Ranan na ganta gidan Aunty Maryam" Noor tace "How will i even know who she is, ni ban ma damu insan wacece ba tunda ba gabana take ba, i hate nonsense, na dai ji Aunty Maryam na ce ma Mami ai gidan iyayenta Yaya Khalil ya zauna when he was in kano, they were kind to him, they did that, they did this, bla bla bla, ita kuma tana so ta fara karatu ba a son ta zauna hostel, shine wai zata zauna nan gidanmu, cause at first Mami bata amince da zamanta a nan ba, but Aunty Maryam insisted, ta dinga kawo silly backups har sai da tayi forcing Mami yarinyar ta zauna gidan nan" Kallonta kawai Nadeeyah take babu ko kiftawa, can tayi karfin halin cewa "But who brought her here?" Noor ta karyar da kai tace "We saw her a day after yayanmu came back, which means tare kenan suka zo gidan, yes tare ma suka zo" Nadeeyah ta hadiye abu da kyar tace "Tare??" Noor tace "Yeah, and you know what?" Nadeeyah ta girgiza kai, Noor tace "You remember the video of a lady with undies that went viral last month?" Nadeeyah tayi shiru, Noor tace "Wani video that's all over social media na wata yarinya babu kaya jikinta?" Nadeeyah tace "Yeah, i heard about the video amma i didn't bother watching, so ban ta6a gani ba" Noor tace "Toh yarinyar ce" Nadeeyah ta zaro ido with surprise tace "Wace yarinya?" Noor tace "Yar rainin wayon da ta fita yanzu, ita ce a video din sure" Buda baki Nadeeyah tayi tace "Wai da gaske?" Noor tace "I mean it, bani da video din da na nuna maki, su Sajidah da Hanan ne ke da shi a waya" Nadeeyah was over shock, tayi karfin halin cewa "Kuma gidansu Kjay ya zauna a kano?" Noor tace "Yes, she was once a student of Maryam Abatcha" Nadeeyah ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh Allah ya kiyaye" Noor tace "Waow its been long i hala this way, har kaina ya fara ciwo wallahi, shi sa bana son magana da yawa amma wannan yar kauyen ta sa ni magana, As i was saying...." Nan ta ci gaba da ba Nadeeyah labarin da take bata cikin nutsuwa irin na big babes, but gaba daya Nadeeyah was absentminded, Nihad ta tsaya mata a rai sosai, abinda ta mata ranan da suka hadu gidan Aunty Maryam ya fado mata, ita kuma a ranan bata dauka as komai ba, sai yanzu brain dinta ya tunatar da ita cewa warce suka hadu a mall a can kano ce fa da Kjay, mamaki da fargaba ya cikata, but why did he have to bring her all the way from kano to his parent house, sannan even for once bai ta6a ce mata tare suka dawo ba gashi yau satinsu uku, Noor dake ta magana ta lura gaba daya hankalin Nadeeyah baya wajen ta kai hannunta fuskarta tana waving, da sauri Nadeeyah tayi blinking idonta, Noor tace "What are you thinking of?" Nadeeyah bata ce komai ba amma kana ganinta kasan there is something bothering her, she looks so disturbed, Noor ta kamo hannunta tace "Tell me plss, me ya faru" Lkci daya Nadeeyah taji hawaye ya kawo idonta ɗon saurin kuka ke gareta, tana kokarin ganin bata fashe da kuka ba tace "He neva told me he came all the way from kano with her, even for once bai gaya min ba" Noor ta zaro ido tace "Ohh that? Meye abun damuwa a nan bayan dai kinsan aurenki zai yi? In 3 days time fa xa a kai kudin aurenku da shi, and baxa a sa ya wuce sati biyar ba, so why bother ur self about one filthy lady that's all over social media half naked? ke sai kace baki san halin KJay ba? Ba abinda ya hada sa da yarinyar banda gidansu da ya zauna don ni tunda ta dawo gidan nan ma ko magana bana ganin yana hadasa da ita, you know he have class" Nadeeyah ta sauke ajiyar zuciya bata dai ce komai ba tana share idonta, Noor tace "C'mon chill plss, wannan bata kai ta sa ki shiga damuwa ba har ki zubda hawayenki a banza, me xai yi da ita? Da akwai wani abu tsakaninsu ma ai baxai fara kawota gidan nan ba, kuma saboda mugun abinda tayi shi yasa ma ba a son ta zauna hostel may be parent dinta suka yi requesting ta zauna a nan, shi sa ma kika ganta a nan" Nadeeyah ta gyada mata kai kawai, Noor ta ci gaba yi mata hiran da take mata a nutse..... Har karfe biyar khalil na zaune inda yake a cikin compound din
Chapter 164 · 0% Book details