← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 165

Sashe 129

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya nufa ba tare da ya hadu da kowa a hanya ba, ya bude kofar parlonta na farko a hankali, babu kowa ciki sai sanyin Ac da kamshi me dadi dake tashi a parlon, ya karasa daya parlon ya shiga, nan ma ba kowa ciki..... Dai dai nan ta fito daga bedroom dinta da Mai aikinta, tsaye tayi with shock tana kallonsa baki bude, ko kwakkwaran motsi bata yi sbda shock, ya karasa a hankali ya rungumeta ya lumshe idonsa, cike da karfin hali tace "Khalil??" Mai aikinta ma haka ta koma gefe ta rufe baki da hannu tana kallonsa, kasa ce ma Maminsa komai yayi, ta dago kansa tana kallonsa hawaye cike idonta tana girgiza kanta, yayi mata murmushi cike da karfin hali yace "I have missed u soo much Mami" Ta kara rungumesa ta fashe da kuka sosai tace "How did you get here? Who allowed you in? Ta ina ka shigo?" Ya kasa ce mata komai lkci daya idanuwansa suka kada, Mai aikin ta nufi kofa ta fita ta kullo masa kofar a hankali, Mami ta ja sa zuwa bedroom dinta tana kallonsa hawaye na sauka idonta tace "How did you get here son?" Sauke idonsa kasa yayi ya tafi gefen makeken gadonta ya zauna, tafiya tayi da sauri ta zauna gefensa ta kamo hannunsa tana kare masa kallo, ba ainahin haskensa ba kenan, sannan ba haka ya bar gidan nan ba, ta fashe da kuka sosai ta dafe kanta ta kasa ce masa komai, yayi karfin halin cewa "Kiyi hakuri Mami, surely everything that has beginning will definitely have an end" Ta dago kai cikin kuka sosai tace "Amma ta yaya ka shigo gidan nan Khalil?" Kallonta kawai yake, Bayan few seconds a hankali yace "Abba ne ya kirani" Mami ta zaro ido tana kallonsa da kyau tace "You mean da kansa ya kiraka??" Khalil ya gyada mata kai yace "Yea Mami, i don't know what he is seeing me for" Hankalin Maminsa ya kara tashi, ta hadiye abu da kyar tace "When did he call you?" Khalil ya sauke idonsa yace "Jiya...." Mami tayi tagumi with different thought running her mind, can ta tashi tace "Ohk, but u are not moving an inch from here today, ka bari sai nan da jibi, babu wanda xai san kana gidan nan, you just remain here for now, ok?" Kallonta Khalil ya dinga yi ya kasa cewa komai, ta mike ta dau wayarta da sauri tayi dialing number mai aikinta, tana dagawa tace "Bilkisu kada ki ce ma kowa khalil ya dawo yana gidan nan, make sure babu wanda xa ki gaya ma har su Mimi" Bilkisu tace "Dama babu wanda na gaya ma Mami" Mami tace "Good" Daga haka ta katse wayar, Khalil dake ta kallonta yace "But i have to go out before Magrib Mami" Mami ta zaro ido tana kallonsa tace "Out to where? u are going nowhere for now Khalil, ko nan da second parlor dina baxa ka fita ba i am telling you, u will remain here for now" Kasa ce mata komai yayi ya dinga kallonta, ta juya da sauri ta fita daga dakin, ba a dau lokaci ba sai ga Mami da tray me dauke da different fruits ta ajiye masa, Mai aikinta dake biye da ita ta ajiye nata tray din, before 5 minutes duk aka cika masa gabansa da abinci iri iri da natural drinks, bayan mai aikin ta fita Mami ta kasa daina kallon ɗan nata, tana yi tana share hawayen da ya ki tsaya mata, har sannan gani take kamar a mafarki ne, gani take xata farka taga babu shi, dawowa tayi kusa da shi cike da karfin hali tace "Tell me what u want to eat in zuba maka son, fried rice? Jollof rice, tuwo da miyar taushe, sinasir? Cous cous? Is it the pepper chicken u are taking first or the cow leg pepper soup?" Kallonta kawai yake ya kasa cewa komai, lkci daya jikinsa yayi sanyi, he knows he missed all this, ta fashe da kuka ta rungumesa tace "My prayers was always with you son, i know i have missed u a lot, i just had nothing to do about it" Kuka take sosai, ya runtse ido yace "Pls ki daina kukan nan Mami, i was fine and comfortable all through, kawai dai na kan yi kewanki da kannena sosai hakan ne kadai ke samin damuwa" Mami ta sake sa ta sauka ta fara zuba masa abincin iri iri a plate, shi dai kallonta kawai yake, bayan ta gama zuba masa tace "Ka ci duk abinda kake son ci sai kayi wanka son, let me get u what to change" Daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, fadawa yayi saman gadon, gaba daya hankalinsa ya tafi kan Nihad da ya bari ita daya a dakin hotel, from where will he start convincing his mami har ta hakura ta bar sa ya fita?? Not even that, don kuwa wannan me sauki ne, now!! from where is he going to start explaining to Mami cewar ai an masa aure? Ta yaya zai fara mata wannan gagarumin bayanin and how will she even take it balle uwa uba Abbansa, tunanin hakan scent cold all over his body, ya mike zaune a hankali yana jin wani sanyi na shigarsa sosai, tun barinsu kano hankalinsa bai tashi haka ba sai yanzu, ta ina zai fara wannan bayanin yace ai an masa aure wanda shi ma ba da son ransa ya amshi auren ba, Yaya iyayensa da relatives dinsa da ma yan uwansa gaba daya za su dauki wannan babban lamarin, aure without his parents consent, this now is his biggest challenge so far, rike kansa yayi bayan yaji kansa ya wani tsara masa, After some minutes Mami ta dawo dakin da kayansa da ta saka a leda don ma kada wani ya gani, kannen Khalil kuwa duk ta hanasu zuwa ɓangarenta a sunan she is not okay and she needs privacy, da sauri khalil ya dago bayan Maminsa ta shigo dakin, ganin bai ta6a abincin ba da damuwa tace "C'mon pls ka sauko ka ci abinci Khalil kar ya huce, ko dai akwai wani abun dake damunka har yanzu..." Khalil ya dinga kallonta yana tunanin ta inda zai fara, can dai yayi karfin halin cewa "Mami na ji kince baxan fita ba, kuma fitan da xanyi yanxu is very urgent" Mami ta zauna kusa da shi cikin rawar murya tace "I am afraid baxan sake ganinka ba kuma Khalil, kilan idan ka fita baxa a sake barin ka shigo gidan nan ba, i can't..." kawai sae ta fashe da kuka tana girgiza kai cikin tashin hankali tace "Haka jikina ke bani, i can't endure loosing u for the second time son, ban san me zai faru da ni ba idan hakan ta kasance, me xaka fita kayi Plss?" Ya sauke idonsa da ya kada, bayan few seconds cikin sanyin murya yace "Mami gidan da nake zama a garin kano da nace masu zan taho Abuja yau sun hadani da er su muka taho tare da ita, zata karbi admission letter dinta a wani makaranta da tayi applying a nan, she knows nobody in here Mami, kuma har yanzu tana makarantar tana jirana" Mami tace "Oh my God, is that so?? Allah sarki, bari in kira driver sai ka bani numberta in tura masa yaje ya daukota yanzu" Khalil was shocked at what she just said, Mami ta mike da sauri xata dauko wayarta ya bi ta da kallo, can sai gata ta dawo kafin ta kira Drivern yayi saurin cewa "Mami she is just a young girl, bata da waya a hannu, dama sai xata fara karatun ne za su bata waya, kawai ce mata nayi zan zo in dauketa a makarantar later" Mami dake kallonsa tace "Toh ka fadi inda kace ta jira ka a makarantar mana in kira Drivern in sanar masa yaje ya daukota, why are you making this a big deal son??" Khalil ya kamo hannunta a hankali yace "Mami tsoronki kada in fita a hanani shigowa a bakin gate ko? but trust me ya sanar masu zan zo ya kuma masu izinin barina in shigo shi yasa har suka barni na shigo, idan da ba haka bane da baxan ta6a shigowa gidan nan ba" Mami ta fashe da kuka tace "Bana son kowa yasan ka dawo Khalil" Khalil ya girgiza kai a hankali yace "Mami, surely in dai yan gari xai tambayesu ko na zo kuma za su sanar masa na zo ina gidan, kiyi hakuri in je in daukota yanzu in dawo Mami, i promise you ko awa daya baxa ayi ba zan dawo" Mami dai tayi shiru tana goge hawayen dake ta sauka idonta, sosai zuciyarsa ya karaya ganin yanda Maminsa ke kuka, ya rungumeta ya runtse ido yace "Kiyi hakuri Mami, kowa a rayuwar nan da irin tasa kaddarar, and Alhamdulillah so far" Mami ta gyada kai tace "Haka ne son" Yayi kasa da murya yace "Ni kaina bana son ganin kowa na gidan nan a yanzu, don haka ki kwantar da hankalin ki, i will follow the back door idan xan fita..." Cikin sanyin murya tace "Toh mota fa?" Yace "I will order Bolt" Mami bata kuma cewa komai ba, yace "In sha Allah idan na dawo zan ci abincin Mami" Yana fadin haka ya lumshe ido yayi pecking dinta a forehead sannan ya mike, ta bi sa da kallo hawaye na zuba idonta har ya fita daga dakin.
Chapter 129 · 0% Book details