← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 165

Sashe 22

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

uwarki ke yi ba" Nihad ta hade rai tace "Wannan wawiyar me ta sani, ko bai mata magana ba ma ai washe masa hakora xata yi ita tayi masa, baxa ma ta jira ya gaisheta ba ita xata fara gaishesa sbda bata da hankali, pls mumy ki daina sa Nihal a cikin mutane" Mumy tace "Ki bi duniya a sannu Nihad, babban matashi irin wannan sbda yana aiki karkashin Abbanki kice baxa ki gaishesa ba sai dai ke ya gaisheki, me yasa baxa kiyi koyi da Nihal ba, me yasa kika dau duniya da xafi haka" Nihad tace "Ni dai Mumy kiyi hakuri ki bani makullin motar ki yau wllh ina da lectures karfe goma, Ni kuma baxan juri shiga mota daya da shi ba" Mumy tace "Toh xa mu gani kuwa, kuma wllh kika sake xuwa gun Hajiya kika amshi makulli sai na 6abbalaki a gidan nan" Nihad tace "Shikenan ni baxan je makarantar ba kawai" Mumy tace "Ohk ni kike gaya ma wannan ko" Ta fashe da kuka sosai tace "Toh Mumy ya kike son inyi, ni naga kamar ma kin fi son driver din nan a kaina kawai" Mumy tace "Ehh na fi sonsa a kanki, kuma wllh kar ki kuskura ki bari karfe goma yayi maki a gidan nan, sannan shi din xai kai ki, idan kuwa ba haka ba xaki sha mamakin abinda xan maki, tunda ke kin dau girman kan duniya kin daura ma kanki" Daga haka Mumy ta fice daga dakin, Nihad tayi kukanta ma'ishi, taji ta tsani wannan bawan Allah, ta tsanesa... Babu yanda ta iya haka ta tashi ta shirya, karfe goma saura minti biyar ta fito compound, atamfa ce jikinta da wata mitsitsiyar mayafi da ta rataya a wuya, hannunta rike da laptop dinta da jaka, fuskarta a daura ta nufi can inda ta hango Driver din a xaune da Aminu, tana masa wani matsiyacin kallo, cike da isa da gadara tace "Tasowa xaka yi kayi dropping dina a school idan ka ga dama, kai kuma Aminu sai ka gaya masa makarantar tamu" Daga haka ta juya ta bar wajen ta tafi can gun motar, murya can kasa kasa Aminu yace "Iko sai Allah" Mikewa Khalil yayi ya nufi motar, Har xata bude back seat sae kuma ta fasa ta xaga ta bude seat din gaba ta shiga, yanda ta hade rai sai kayi xaton ko dariya bata ta6a ba, shi ma ya shiga motar, suna fita compound Aminu ya daga masu hannu, AC din motar Nihad ta kunna, shi dai bai nuna yasan abinda tayi ba, suna hawa saman titi tayi connecting phone dinta ta kure waka a motar, shi dai driving dinsa kawai yake, bayan kusan minti talatin suna tafiya, ganin tafiyar tasa babu direction, ta wani juya ta kallesa tace "Wai malam baka san inda xaka kai ni bane, ko Aminun bai gaya maka ba?" Tafiyarsa kawai yake pretending he didn't know she is talking duk da yana jinta, rage volume din wakan tayi can kasa, a fusace tace "Malam da kai nake" Ya kalleta yace "Ohk magana kike, wakar ki ce ta hana inji" Ta yi masa wani kallo tace "Da yake kai kurma ne ba dole waka ya hanaka ji, Aminu wai bai gaya maka inda xaka kai ni ba?" Yayi slow down sannan yayi parking yace "Ina ta sauraren kice ga inda xaki ne ai" Buda baki tayi tana kallonsa, Cikin daga murya tace "Aminu bai gaya maka bane?" Yace "Toh ai ban ga Aminu cikin motar ba" She couldn't stop looking at him, ita ba abin ta sauka ba, dakewa tayi tace "Saboda ba kai ke xuba fetur a motar ba shi yasa kake ta yawo da ni a cikin garin kano ba tare da kasan inda xan je ba ko?" Bai bata amsa ba, bata kuma ga alamar xai ce komai ba, wani dogon tsaki ta ja, ta gyara xama tace "Dama harka da ɗan kauye ya gaji haka, idan kaga dama Maryam Abatcha American University of Nigeria xaka kai ni" Without looking at her yace "Ohk sai kin dinga min kwatance" Tace "Ban gane sai an maka kwatance ba, kai dama babu inda ka sani a kanon ka xo ka nemi driving a gidanmu?" Yace "Ehh idan aka ci gaba da nuna min wajajen xan sani ai" Tace "Amma wllh baka da amfani" Tsaki ta ja tace "Ai sai ka juya kan motar idan dai ba garinku xa mu je ba" yace "In kince aje can din ma ai sai aje" Bude baki tayi, sai kuma tace "Wallahi yaron nan ka raina ni" Sai a sannan ya juya ya kalleta jin abinda tace, ta galla masa wani harara tace "Malam kana bata min lkci xan je makaranta" Yace "Na xata garin namu xa mu" Daga haka ya juya, rai a bace ta dinga gwada masa inda xai bi har suka iso makarantar, ganin yayi parking a waje tace "Malam tada motar nan ka shigar dani ciki, ko duk nan akwai wanda kaga anyi dropping a titi?" ya ci gaba da driving din slowly, dai dai gate din makarantar ya tsaya ya sauke glass din motar, gaishesa security din suka yi, ya amsa ya amshi pass ya shiga cikin makarantar yace "Ina?" Rudely tace "Duk inda ka ga wancan jan motar ta bi kai ma ka bi, bani da lkcn yi maka wani kwatancen" Bai ce mata komai ba, ya ci gaba da driving dinsa, Dai dai wajen da motar ta tsaya ya samu waje yayi parking shi ma, ta ciro wayarta ta kira Husnah, Husnah na dagawa tace "Kin shigo school?" Husnah tace "Ehh, ke kina ina?" Nihad tace "Ku fito parking space ke da su Naf ku sameni yanzu yanzu, ki tabbatar har da Zully xa ku taho" Husnah tace "Ke kika yi driving din yau ma?" Nihad tace "Ke dai nace ku zo sharp sharp" daga haka ta katse wayar, ta zuge zip din jakarta ta fiddo chewing gum ta jefa cikin bakinta tana tauna a hankali, Shi dae gabansa kawai yake kallo, Bayan few seconds ya kashe motar ya zare makullin ya ajiye nan kusa da ita without looking at her, ya bude motar xae sauka, da mamaki tana kallonsa tace "Heyy, meye hakan kake yi? Waye xaka bar ma motar?" Still bai kalleta ba yace "Masu shi" Daga haka ya kulle motar ya juya ya bar wajen, kasa cewa komai tayi sbda mamaki, can ta sauka motar tana bin sa da ido baki bude, sae ga Husnah da Naf with Zully da wata kawar Zully, Husnah ta karasa kusa da ita da sauri tace "Nihad what happened, ya da bude baki haka" Nihad ta kalleta tace "I don't think this guy is okay, ji tafiya yayi ya bar min motar fa Husnah" Husnah tace "Wa??" Nihad tace "New driver din, kiranku fa nayi wai ku gansa, mu yi masa tijara..." Husnah tace "Wai wancan me bakar rigar dake tafiya?" Kasa bata amsa Nihad tayi don da gaske mamaki ne kawai ya cikata, Naf tace "Kawai haka nan ya kama ya tafi babu magana?" Nihad tace "Not at all, ajiye min makulli yayi kusa da ni, nace wa xai bar ma motar, wai masu shi.... kawai ya saka kai yayi tafiyarsa" Lkci daya Husnah da su Naf suka kwashe da dariya har da kyakyatawa, Nihad ta hade rai, Husnah tayi dariya me isarta sannan tace "Gaskiya wannan drivern dan duniya ne, ni ko na so in gansa wllh, ya iya bada amsa dai dai da tambaya" Nihad ta hade rai tayi locking motar ta bar su wajen a tsaye ta wuce aji, bin ta suka yi har sannan suna dariya, a lecture room suka sameta, Husnah ta xauna kusa da ita tace "Anya ba ajiye aikin yayi gaba daya ba" Nihad tace "Toh ni ya kamata ya ba makulli? Ko dama ni na basa makullin?" Husnah ta fashe da dariya har da kife kai.
Chapter 22 · 0% Book details