← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 165

Sashe 122

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

baxan iya kwana a dakin ni kadai ba" Sai kuma ta hade kai da gwiwa tana rera kuka, bai kuma ce mata komai ba ya kulle kofar ya karasa cikin dakin. A hankali ta mike ta shiga bandaki ta dauro alwala ta fito ta tada sallan isha, yana kwance daya side din gadon waya kare kunnensa, duk da can kasa kasa yake magana amma lkci daya ta gane da warce yake wayar, ta ja tsaki ta mike ta dauke darduman ta linke ta ajiye ta nufi saman gadon ta fizge duvet da ke kai ta dau pillow daya ta shimfida duvet din a kasa sannan ta ajiye pillon ta kwanta, tana ta juye juye kan duvet din can ta kara jan wani tsaki ta tashi ta tafi ta kashe wutan dakin ta dawo ta kwanta, shi dai bai daina wayar da yake ba kuma duk maitarta baxata ce ta ji abinda yake cewa a wayar ba, for almost one hour bai gama wayar ba, ya mike sabida iska da aka fara alamar hadari, kunna wutan dakin yayi Nihad da tayi lamo a kasa tana jin iskan ita ma ta mike zaune da sauri ta bi sa da kallo sai kuma ta tashi ta bisa parlon, ya juya ya kalleta, sai kuma yace "Zan kwanta yanzu kinsan nace maki bani da lafiya, za mu yi magana gobe" Daga haka ya katse wayar yace "Lafiya kike bi na?" Kin cewa komai tayi tana kallonsa, haka kawai tayi masa rashin kunya ya ki yarda ta kwana a dakinsa, shi sa ma taki ce masa komai juyawa yayi ya tafi ya kulle duk windows din gidan, duk inda ya nufa sai ta bi sa har dakinta sai da ya shiga ya kulle windows sannan ya fito tana biye da shi suka koma dakin nasa, kulle nasa windows din yayi ya kashe wutan dakin ya kwanta daya side din, ba a wani dau lokaci ba aka fara yayyafi, Nihad dai duk a tsorace take a kasa da take kwance, can ta mike zaune a hankali tana kallon saman gadon, sai kuma ta turo baki ta mike ta dauke pillown da duvet ta koma saman gadon ta kwanta, yana jin ta bai ce komai ba sai ma juya mata baya da yayi ya rufe ido, Nihad na jin sauwkan ruwa ta mirgina a hankali ta koma bayansa tayi lamo, ta dade a hka ta kasa bacci, kamar yanda shi ma ya kasa baccin, da taji anyi tsawa sae ta kara matsawa gun sa, a haka har bacci ya dauketa daga karshe.... Can cikin bacci ta ji ana ta6a ta, ta bude ido a tsorace, xata bara ihu ya rufe bakinta da Palm dinsa.
Chapter 122 · 0% Book details