← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 165

Sashe 28

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nihad na shesshekan kuka tace "Wllh shi inna, kawai an bar sa yana ta abinda ya ga dama a gidan kamar gidan ubansa, duk ya gama rena ni, ko gaisuwa bata hadani da shi" Inna tace "Duk ba wannan ba, yanxu kin kira Aliyun??" Nihad ta daura kanta gefen gadon inna hawaye na sauka idonta tace "Bayan ya ki dagawa" Inna ta dauko wayarta ta mika mata tace "Kirasa da nawa" Nihad tace "Ae idan ba shi da numberka baxa ka iya samunsa ba, ya sa layinsa a Private" Inna tace "Wai ko ba dai Aliyu ɗ'an wajen janaral Habubakar jikamshi ba?" A hankali Nihad tace "Shi..." Inna tace "To wannan dreba duk yanda aka yi tsinanne ne, ko don nace masa ya saki jikinsa yasa ya sake kamar gidan ubansa? to ai ni na xata yaron arxiki ne" Salati inna ta saki tayi tagumi tace "Yau naga dreban jaraba, ashe duk ni na ja komai da nace ya saki jikinsa, to a kira min Ibrahim din tun yamma bai yi ba ya sallamesa" Nihad ta dau wayar inna da sauri ta fara neman number Abba tayi dialing, Inna ta bude baki ta rike ha6a tace "To shi kuma Aliyun banda abunsa garin yaya xai ce sai yayi ma dreba magana mutumin da ba ajinsa ba, ai abinda bai sani ba talakawan nan haka suke da dacin rai kamar mutum ne ya doro masu talaucin, ina shi ina wani basamuden buzun dreba can? To ko a almajiri dai baxa su yarda su ajiye wannan mutumi a gidansu ba balle dreba, su da tun daga titin da ya yanka unguwarsu xaka fara ganin dirka dirkan sojoji har da motocinsu...." Nihad ta turo baki tace "Abba bai daga ba" Inna tace "Ina xai daga, ya tashi ya kawo wani kato gansameme kamar mutanen farko ya dau mota ya basa, ni wllh ranan da na fara ganinsa sai da na tsure, sai fa ya daga mutum ya nanasa da kasa sau biyar bai gaji ba, irinsu ai gadin dogon banki ya kamata a basu ba wai motar mutane ba" Nihad dai tayi tagumi don abinda ya dameta daban, ita yanxu ta ya xata fara shawo kan Aliyu, da yaya ma suka dawo soyayyar, Inna tace "To ko kin san inda ya sauka ki rakani mu je in basa hakuri" Nihad ta kalleta tace "Ji ki kuma, kawai don ki ja min raini?" Inna tace "Wani raini mutumi na nema ya kubuce, wa ke ta wani raini Nihad, idan ma baxa ki shiga ba ni ki rakani ki nuna min hanya in je in samesa" Nihad tace "Aa ke dai kawai duk yanda xa kiyi kiyi Abba ya kori driver din nan kawai" Inna tace "Yo sai ma kin fada, abu har ya kai yana korar ma jikokina samari" Hamid ne ya bude kofar dakin ya shiga yana kallon Nihad yace "Ke don uwarki ni sa'anki ne xaki wuce ni da abokina baki gaishemu ba" Nihad ta turo baki ta koma gefen Inna, Inna dai bata ce komai ba, Yace "Mahaukaciya kawai, uban wa xaki dinga daga ma kai?" A fusace Nihad tace "Kina dai gani babu abinda na masa ya xo ya fara xagina ko inna, ni fa shi yasa bana son xuwa gidan nan wllh, kowa yaje yaji da mugun halinsa" Cikin xafin nama ya nufeta, Inna ta mike ta wangale hannu tana tare Nihad tace "Dokeni to, Hamidu nace ka dokeni" Huci yake yana kallonta, Inna tace "Ai dama ka saba dukan nawa yanxun ma ka duka, ranan da ka biyo Bilkisu ai ni ka jibga ba ita ba" Nihad ko kallonsa bata yarda ta sake yi ba, Yayi wani kwafa ya fice daga dakin, Inna ta kulle dakinta tace "Kinsan korosa aka yi daga can kasar wajen wai wa'adinsa ya kare a can, to kuma sai kayi ta hucewa kan ya yan mutane" Nihad bata san lkcn da ta kyalkyale da dariya ba, Inna tace "Allah haka uban yace min, duk a booth din jirgi aka kwaso su aka dawo" Nihad dai bata ce komai ba, Inna tace "Yanxu ko kin boye number ki baxai daga wayar ba?" Nihad ta mike tace "Ni dai xan tafi inna dama anjima da daddare kice Hamid din ya kawoki nan gidanmu ki samu Abba da kanki" Inna tace "Toh shkkn ma, kawai bari inje in riskesa a gidan ba sai mun yi waya ba, idan ma ya kama ko shi sai ya kira Aliyun ya basa hakuri" Bude baki Nihad tayi, can ta kyabe bakin tace "Ni dai sai kin zo" Daga haka ta fita daga dakin, A bakin gate abokin Hamid ya tare ta da ya faki idon Hamid ya biyota, yana fara magana ta dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu tana yatsine fuska tace "Ina wasa da kai ne malam?" Daga haka ta ja tsaki tayi ficewarta daga gate din, ya bi ta da kallo baki bude, dama Hamid ya gaya masa ya ki ji. Nihad na komawa anguwansu ta yi ido hudu da Khalil dake xaune kan dakali a kofar gida wayarsa na kare kunnensa, yana ganinta bai sake cewa komai ba a wayar da yake kuma bai cire wayar a kunnensa ba, har ta isa dai dai inda yake, tayi masa wani harara ta ja tsaki ta shige cikin gida tayi banging gate din. Abba na tsaye balcony bayan magrib Khalil ya karaso da ladabi yana kallonsa yace "Gani Alhaji" Abba yace "Yauwa pharmacy xan aikeka ka siyo min magani yanxu" Khalil yace "Toh, ya sunan maganin?" Abba na duba wayarsa yace "Yanxu likitana ya turo min ta message bari dai in duba" Abba na shiga message din har ya fara pronouncing sunan maganin kawai ya fasa kar khalil yaje ya masa shirme, yace "Bari kawai xan rubuta maka a takarda kaje ka siyo, idan ka siyo sai...." Abba ya dakata ganin mai gadi na bude gate, sai ga motar Hamid ya shigo compound din, Abba yace "Je ka xan rubuta sunan maganin a kawo maka yanxu" Yace "Toh Alhaji" daga haka ya nufi boys quarters, Inna ce ta sauka daga motar ta nufo balcony, Abba dai na tsaye yana ta tunanin ko lafiya, Tana isowa ganin yanayinta yace "Lafiya inna?" Tace "Ina fa lafiya, mu je parlor baxan iya tsayuwa ba" Sai da ta fara shiga parlon Abba ya bi ta, kanta tsaye ta tafi parlonsa duk yana biye da ita, ta nemi waje ta xauna shi ma ya xauna yace "Ina yini Inna?" Tace "Ibrahim a ina ka samo wannan gansamemen dreban naka?" Abba yace "Wani abu ya faru ne?" Tace "Meye baxai faru ba, ya kora ma Nihad saurayi, d'an wajen Janaral Jikamshi, har yaron ya goge numberta yanxu haka da nake maka magana" Abba yayi shirui yana kallonta as if confused don ya kasa fahimtar xancen nata, Inna tace "A kara min Ac, xafi ya isheni" Abba ya dau remote ya kunna Ac din, yace "Ban fahimta ba Inna" Nan inna ta xauna tayi ma Abba tsari da abinda Nihad ta fada mata da ma wanda bata fada mata ba duk ta dire ma Abba, Abba yace "Ikon Allah, ke yanxu wa ya sanar maki wannan?" Inna tace "Har gida ta sameni tana kuka kamar ranta xai fita, hankalina yayi mugun tashi shine nace da kaina xan taho da daddaren nan, sannan a kira min dreban in ji uban da ya aikosa wajenmu, ni dama ina ganinsa na sha jinin jikina ban yarda da shi ba kawai nayi shiru ne, wa yasan adadin binne binnen da yayi maka a gidan nan yanxu? Huhuhu kana wasa da buzun mutum, Ai irinsu xuwa suke su tarwatse gida kai har ma su talauce mai gidan su saci abinda xa su sata su gudu su koma Nijar, to Ibrahim ko motar nan ma ya gudu maka da shi ai ya cuceka, to yanxu ni dai a kira min shi ko in tafi in samesa da kaina" Abba yace "Aa ba sai kin samesa ba, ai sallamarsa kawai xanyi ya tafi ba sai anyi wani tashin tashina ba" Inna tace "Aa ko xagi ne a bari in masa kafin ya tafi ai" Abba yace "Ke dai nace ki bar komai a hannuna, bari Hamid ya xo ya maida ki gida dare yayi" Tace "Ai Habubakar ne ya sa ya kawoni banda haka waye ubana Hamid xai kawoni, tun fa da aka korosa daga kasar wajen yake jin haushin kowa, to ni nasan sanda ya koma can da xama balle sanda aka korosa, kawai gani nayi ya dawo da manyan jakunkuna, ji yake kamar duk ya kashe mu yanxu haka" Abba yace "Ke wa yace maki an korosa, don Allah ki bar fadin wnn magana a xata da gaske ne" Mikewa yayi ya fita daga parlon ya kira Hamid dake main parlor yace "Zo ka maida Hajiya gida" Yace "Toh Abba" Har mota ya rakata, bata ce xata shiga wajen matansa ba shi ma bai ce ta shiga ba, don da suka fito parlor ma yace Nihal ta kirasu su gaisheta ta hana, yana tsaye compound din har motar ta fita, yana kallon mai gadi dake kulle gate yace "Kai ina Ibrahim?" Aminu bai kai ga bada amsa ba sai ga khalil da mota, Aminu ya kara bude gate din Khalil ya shiga compound din da motar sannan yayi parking a parking space Abba dai ya bisa da kallo, yana sauka daga motar ganin Abba a tsaye, ya nufesa da ledan pharmacy a hannunsa ya ɗan risina yace "Ga maganin Alhaji" Abba yace "Wani Magani?" Khalil ya kallesa yace "Da kace a siyo" Abba yace "Na gaya maka maganin da zaka siyo min ne?" Khalil ya kalli ledan hannunsa da sauri, kawai sai ya rasa abinda xai ce, Abba ya amshi ledan ya bude maganin sannan ya bude wayarsa ya shiga message din da Dr dinsa ya turo masa yaga maganin ne Khalil ya siyo, Abba ya daga kai yana kallonsa daga sama har kasa, kafin yace komai khalil yayi saurin cewa "Ai ka fada min sunan maganin, rikewa nayi a kai" Abba dai bai ce komai ba sai kallonsa yake, Khalil kam ya kasa barin su hada ido, Can Abba yace "Ban gaya maka sunan maganin fully ba"
Chapter 28 · 0% Book details