← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 165

Sashe 143

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kallon Aunty Maryam dake ta kallonsa ya mata alamar yana zuwa sannan ya tafi inda Nihad take, saman gado ya sameta kwance, ya karasa ya mika mata wayar, ta mike zaune tana kallon Iphone da yake mika mata, ta kai hannu ta amsa tana kallon screen din taga number ya farooq don a haddace yake a kanta, ta kai kunne cikin sanyin murya tace "Ya farooq" Daga daya bangaren yace "Na'am Lil sis ya kike" Lkci daya har hawaye ya kawo idonta tana goge idonta cikin rawar murya tace "Lafiya lau" Yayi shiru, sai kuma yayi kasa da murya yace "Yanzu kukan me kike? Ko akwai damuwa ne?" Ta kasa ce masa komai, yace "Nihad" Tana goge idonta tace "Na'am" Shi dai khalil na tsaye yana kallonta, Ya Farooq yace "Bana son wannan kukan naki Nihad, shi yasa ko na kirasa bana cewa ya baki, kukan nan yana damuna idan kina yi" A hankali tace "Toh na daina yaya" Yace "Good girl, kiyi hakuri in sha Allah komai xai wuce, komai yayi farko xai yi karshe in sha Allah, don haka ke dai ki zama me biyayya ku zauna lafiya da mijinki, sannan ki rike Ibada sosai, may Allah guide and protect you for us" Cikin sanyin murya Nihad tace "Ameen yaya" Yace "Har yanzu baki da atm card ko?" Ta gyada masa kai kamar yana ganinta, yace "Hello" Tace "Ehh bani da shi" Yace "Toh shikenan, in sha Allah on Saturday xan zo, na gaya masa ma" Nihad tace "Ina zaka zo yaya?" Yace "Wajenku idan Allah ya kai mu, be a good girl always, Allah ya maki albarka" Tace "Ameen yaya" yace "Give him the phone" Mika masa wayar tayi ba tare da ta bari sun hada ido ba, shi dai kallonta kawai yake, bai kuma amshi wayar ba, ita kuma taki yarda ta kallesa, ganin still ya ki amsar wayar ta ajiye masa nan gefen gado ta koma tayi kwanciyarta ta juya masa baya, ya shafa beard dinsa, sai kuma ya dauki wayar ya juya ya fita ya kulle mata kofa. Wajen karfe tara da rabi Aunty Maryam ta bude kofar dakin da Nihad ke ciki, zaune ta sameta saman darduma ta jinginar da kanta da gado, Aunty Maryam tace "Sai yanzu kika yi isha'in? Nihad ta girgiza kai tace "Aa tun daxu nayi" Aunty Maryam tace "Toh baxa ki kara abinci ba ko?" Nihad ta gyada mata kai tace "Ehh Aunty nagode" Aunty Maryam tace "Toh shkkn, tunda ga kayanki ya kawo ki yi wanka sai ki kwanta, ga zani kiyi amfani da shi don towel din bandakin ba a wanke yake ba" Nihad ta nufeta ta amshi zanin da take mika mata tace "Nagode" Aunty Maryam tace "Ni xan tafi daki, Allah ya tashe mu lafiya" Nihad tace "Toh sai da safe" Juyawa Aunty Maryam tayi ta rufo mata kofar ta bar wajen, Nihad ta koma gefen gadon ta ajiye zanin, sannan ta cire Hijab din da tayi sallah ta linke ta ajiye don a dakin ta gani. Ta kalli jakar da ta shigo da shi daxu dakin, can ta nufi gun jakar ta durkusa ta bude zip din a hankali tana kallon ciki, Hijab da aka yi packaging a leda ta ciro har guda hudu, sai kuma Abaya kala biyar da undies masu yawa, sai kayan shafe shafe with perfumes kala biyar, da nighties su ma biyar, kulle jakar tayi ta mike ta bar wajen. Duk da Nihad felt secured a gidan Aunty Maryam amma wannan daren ma ta nemi bacci ta rasa, for almost 4 days now bata bacci da daddare ko tayi a firgice zata farka bayan wasu mintuna, or is she been traumatic, bata taɓa jin tana kewar Mahaifiyarta yanda take ji yanzu ba, maganganunta na karshe ya kasa fita daga ranta da zuciyarta, she could vividly remember every single word shi told her a rananta na karshe a gidansu, and she wish she could hear more of such from her, Magana da tayi da Ya farooq daxu shi ma yayi contributing a rest of mind dinta but she still couldn't sleep, gaba daya idanuwanta sun kekyashe daga jin bacci, daga karshe ta tashi a hankali ta kumna switch din dakin ta ga karfe biyun dare, cike da karfin hali ta nufi bandaki tana jan kafa, har kusan karfe uku da rabi Nihad bata yi bacci ba tayi sallan har taji bata da sauran strength kawai ta jinginar da kanta da gado tana daga zaune kan darduman, sai a sannan taji hawaye na sauka idonta, cikin rawar murya tace "Ya Allah duk wanda yayi min wannan abun ka tona asirinsa cikin gaggawa, come to my aid ya Allah, Allah ka kawo min mafita alfarman ma'aiki" Kuka take sosai tana roƙon Allah, wanda tun faruwan abun yau ne ta kwantar da hankali take kai kukanta wajen Allah cikin nutsuwa, ko jin sanda aka bude kofar dakin bata yi, cause she is really hurt, sae yanxu take ganin she needs to know who is this that betrayed her, she needs to know who did this to her da ya tarwatse farin cikinta ya rabata da Abbanta ya bata mata suna yayi tarnishing image dinta a idon duniya, Aunty Maryam dai sai kallonta take tana tsaye bakin kofa, dama ka'idarta ce duk in Allah ya farkar da ita cikin dare ko dab da asuba ko da baxata yi sallah ba sai ta fito ta dudduba condition din yaranta idan suna gidan, har dakin mai aikinta takan bude ta dubata, in ma da wani bako gidan in dai ba babba bane xata bude dakin ta duba, sai in Allah bai farkar da ita ba wanda hakan ma ya zame mata jiki dole ko yaya sai ta tashi saboda ta maida shi daily routine dinta a gidan.... (Yana da kyau iyaye mata su sa ido su yi kokarin dinga yin hakan ko da ba kullum ba barin idan kana da yara yan mata teenagers, kai har ma da yara mazan, its very very important, i have this aunty that kullum da daddare sai ta leko ku taga halin da ku ke ciki a daki, ya ma riga ya zame mata jiki, da Mumyn Nihad na kokarin yi ma Nihad haka ko da ba a bangarenta take ba da abubuwa da yawa basu faru ba kamar zuwa night parties da take, wasu yan matan sai su kai har karfe daya ana video call da saurayi kasa kasa, ko chatting din banza, wasu kuma a wannan lokacin xa su samu daman shiga internet su yi kallace kallacen banxa, wasu masturbation da dai sauransu, duk kina can kin shanya baki hangangan kina bacci, Allah Ubangiji ya kare mana zuri'a ya raba mu da mugun ji da mugun gani) Duk abubuwan da Nihad ke fada Aunty Maryam na jin ta don daga karshe ma kulle kofar dakin tayi a hankali, wanda hakan ne yayi distracting Nihad ta juya da sauri, sai da gabanta ya fadi ganinta tsaye bakin kofar, ta hau goge idonta da sauri, Aunty Maryam ta karaso cikin dakin tana kallonta ta zauna gefen gado tayi kasa da murya tace "It's okay dear, tunda ki ka kai kukanki wajen Allah kika hana kanki bacci a wannan lokacin, to in sha Allah addu'arki baxata tashi a banza ba, ta yanda baki yi zato ba Allah xai maki sakayya ya kuma tona asirin koma wanene yayi maki wannan abun" Hawaye ya dinga sauka idon Nihad ta kasa ce ma Aunty Maryam komai, Aunty Maryam da taji tausayinta ainun tace "Kiyi hakuri ki daina wannan kukan, tunda kika ambaci Allah ai an wuce wajen kuma, amma me yasa kika yarda da kawaye har zaki zauna cikinsu half naked?" Nihad ta girgiza kai cikin rawan murya tace "Wallahi Aunty ni ban taɓa zama ko a gidanmu haka ba, sannan ni ba a hostel nake ba kawai zuwa nake, lokacin da xa mu fara exams din first semester level 3 ne na koma hostel kuma ni ko da zani bana zama cikinsu wallahi" Aunty Maryam na kallonta da mamaki tace "Toh a ina aka dau video din?" Nihad ta buda hannu tace "Nima wallahi ban sani ba, yanda kowa ya gansa haka na gansa" Aunty Maryam ta dinga kallonta dumbfounded, can tace "Ban gane baki san a inda aka maki video din ba" Nihad ta fashe da kuka tace "Wallahi da gaske Aunty, ni ban san ta yaya aka yi hakan ba, kuma ban ma san ko wani waje ne ba" Aunty Maryam ta kasa cewa komai don mamaki, can dai tace "Toh kenan ba ke bace a video din" Nihad na goge idonta tace "Ni ce Aunty, amma ban san ta yaya ba, because under wears dina ne a jikina" Sosai wannan lamarin ya rikitar da Aunty Maryam, can dai ta sake cewa "Kuma ba a hostel din bane?" Nihad tace "Ba nan bane wllh" Aunty Maryam tace "Ba kuma gidanku bane?" Nihad ta girgiza kai tace "Ba gidanmu bane" Aunty Maryam tace "Ikon Allah, kin tabbata bayan gida baki zuwa wani wajen ko da kawaye haka?" Shiru Nihad tayi, Aunty Maryam tace "Kin yi shiru" Nihad ta hadiye abu da kyar amma tana tsoron ce ma Aunty Maryam ai sun kan je hotel da guess lodge da friends dinta, Aunty Maryam tace "Kina zuwa kenan?" Cikin sanyin murya tace "Ina bin kawayena duk inda xa su wani lokacin" Aunty Maryam tace "Toh su suka maki, ki gaya min tsakaninki da Allah baki shan komai?" Nihad ta dago da sauri tana kallon Aunty Maryam tace "Aunty kamar me" Aunty Maryam tace "Kayan maye, gaya min tsakaninki da Allah, kar ki min karya don kina min ma zan gwada ki kuma zan gane, don ni Nurse ce" Nihad na girgiza kai hawaye na sauka idonta tace "Wallahi Aunty bana shan komai kin ji har na rantse, idan ina shan wani abu Allah shine shaidata, ki gwada ki ga Aunty" Aunty Maryam tace "Toh kawayen naki fa?" Nan Nihad ta fara lissafo ma Aunty Maryam abubuwan da su Husnah suke sha Innocently, haka Aunty Maryam ta saki baki tana kallonta cause taga babu alamar karya a tare da ita, iya gaskiyarta kawai take fada, can Aunty Maryam tace "Ikon Allah, to kuma a gida
Chapter 143 · 0% Book details