Sashe 151
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Yace "Ya kike Nihad?" Tace "Lafiya lau, ina yini" yace "Alhamdulillah, hope you are doing fine, babu matsala dai ko?" Ta sunkuyar da kai cikin sanyin murya tace "Eh" yace "Ohk are you still using ur account?" Tace "Bani da atm card ne" yace "Toh ya kaiki banki ki amsa wani" Tace "Toh" Yace "Xan maki transfer a ciki yanzu" a sanyaye tace "To yaya Nagode" Katse wayar yayi, hawaye ya cika idonta ta rufe fuskarta jikin kujera hawayen na zubo mata, bata son taji tana jin haushinsu a rai sbda Umma because she love all of them, basu ta6a nuna mata ubansu ne kawai daya ba, shi dai Khalil na tsaye don bata basa wayarsa ba, bayan few minutes ta dago tana goge idonta ta mika masa wayar ba tare da ta kallesa ba, kallonta yake, zata ajiye masa kan kujera ganin yaki amsa yace "Kee" Sai a sannan ta kallesa babu yabo babu fallasa, yace "Da xan baki wayar saman kujera na ajiye maki?" Ita dai bata ce masa komai ba, ya amshi wayar ta mike ta bar wajen, ya bi ta da kallo har ta bace sannan ya fita daga parlon, washegari kuma ya bar Nigeria for Zanzibar in the morning. Ranan Talata Mami ta kira Aunty Maryam, bayan sun gaisa Mami tace "Maryam bakuwar nan ta tafi kuwa?" Aunty Maryam tace "Ehh ta tafi jiya" Mami tace "Toh maa sha Allah, banda dai yace a gidansu ya zauna ai yarinyar nan bai kamata a gansu tare ba balle har ya kawota nan gidan" Aunty Maryam dake sauraronta tace "Saboda me Mami?" Mami tace "Kika ce saboda me?" Aunty Maryam tace "Au... Toh Allah dai ya kyauta, Allah ya tsare mana zuri'a" Mami tace "Ameen" Aunty Maryam tace "Ai ko yan gidansu suna ta godiya" Mami tace "Allah sarki, yanzu hostel din zasu kama mata ta zauna kenan?" Aunty Maryam tace "Toh ban dai sani ba" Mami tace "Toh idan ba nan din ba suna da yan uwa a Abuja ne? In basu da kowa ai sai dai hostel din dama" Aunty Maryam tace "Haka ne" sallama Mami tayi ma Aunty Maryam ta katse wayar, Aunty Maryam ta fara tunanin ta ina za a fara convincing Mami?? Tun bayan tafiyar Khalil Zanzibar duk sanda Mami taje gidan Aunty Maryam a daki Aunty Maryam ke sa Nihad ta zauna har sai Mami ta bar gidan, idan kuma ita ke son xuwa gidan yayartata ita kadai take xuwa da Mus'ab ta bar Nihad da mai aikinta a gida, unlike before da har da mai aikinta take zuwa gidan, a cikin wannan kwanakin kuma mijinta ya sanar mata nan da kwana biyar xa su taho kasar da yake, ta rasa ta inda xata billo ma yar uwarta a kan Nihad. Ranan friday ta shirya taje can gidan, bayan sun gaisa da Mami a bedroom dinta, it took her like five minutes kafin ta samu kwarin gwiwan yi ma yayartata magana, Mami tace "Wani magana kuma ke tafe da ke? To Allah ya sa lafiya, ina jin ki" Aunty Maryam tace "Mami dama iyayen yarinyar nan ne suka kira jiya, suna neman alfarman ta zauna wajenmu don basu son xamanta a hostel, and i think lectures will be commencing in 2 weeks time" Mami dai kallon Aunty Maryam kawai take, Aunty Maryam tace "Toh ni kuma gashi nan da kwana biyar xa mu yi tafiya" Mami tace "Ikon Allah, to Maryam ke ko da ba tafiya xa kiyi ba ina ke ina rike yarinyar nan dama? Kuma ma da suka gaya maki haka ai sai kice barin kasar ma xa ki yi, sannan ni kuma da kika zo nan kika gaya min me kike son ince maki? Meye nawa a ciki?" Aunty Maryam tace "Amma Mami ke kam ba me mance alkhairi bace, bansan ki da manta alkhairi ba komin kankantarsa, ko albarkacin xama da suka yarda Khalil yayi a gidansu har na shekara daya ai bakya ce haka ba" Mami tace "Yanzu ya kike son ayi Maryam, ni dai kinsan baxai ta6a yiwuwa ince yarinyar nan ta zo gidan nan ta zauna ba, tsangwama da hantaran yan gidan ma kadai ya isheta balle aje ga shi matsalar da Khalil din xai shiga in har Abbansa ya samu labarin shi ya kawota gidan nan, a ina ya santa da har xai kawota gidansa, ku na lura yin abu ku ke kanku tsaye duk wani abun magana bakwa gudunsa, ke kinga da sararin zamanta nan gidan, kwana daya kadai da tayi kina ganin abinda ya faru" Aunty Maryam tace "Ni wallahi idan kina nuna shakkan matsiyatan gidan nan a fili abun kona min rai yake yaya, ita tsinanniyar Hasanar kike tsoro ko kuma Aminar? Haba Mami ko sau daya ke baxa ki kwatar ma kanki yanci ba, ke kenan baki son fitina ke kenan gudun abun magana, A haka rayuwar xai ci gaba? Yo Abun magana na nawa? Dubi tuggun da suka hada ma danki suka sa ya bar gidan nan kina ji kina gani baki iya buda baki kin tsaya kinyi defending dinsa ba shi da gidan ubansa, nima kika hanani magana a sannan, wannan wace irin rayuwace? Toh wallahi mu ba butulu bane, kuma ba mu mance alkhairi komin kankantarsa, in sha Allahu yarinyar nan bata da wajen zama tayi karatunta da ya wuce nan gidan, kuma wajenki tunda har iyayenta suka nuna mu ma sun yarda damu, sannan da iyayen nata basu rike shi khalil din ba Allah kadai yasan depression din da xai fada a lokacin, kana ji kana gani a kwace duk wani abu naka da ka mallaka, a amshe takardunka akan laifin da baka aikata ba, a toshe duk wani hanyar samun kudinka, sannan ace ka bar gidanku ba a son ganinka, infact garin ma gaba daya kada a samu information din kana ciki, ka tafi duk inda xaka tafi, me kike tunanin zai samu mutumin da aka ma hakan idan bai fada hannun na gari ba? Ni nasan zamansa gidansu really contributed wajen rage masa damuwarsa banda haka da baki gansa a yanda kika gansa ba yanzu, ai Allah ya tsine ma Hasana da Amina, ya walakanta su dai dai gwargwado, wato tunda ta kashe aurenta yau shekara kusan ashirin to bari naki ma ta kashe maki, ga agololinta ta cika gida da su suna ta baza mulki son ransu, wani abun ma sae ayi masu ba ayi ma naki yaran ba, to ai ni da xata burgeni ta auri Janar din kawai mana mu ga, for 20 good years kina daukan cin kashin matan nan kin kasa ta6uka komai, don dai kawai ni xamana ba steady bane a Nigeria amma wani abun da ba ayi ba wallahi, to gaskiya it's high time kema ki kwaci kanki ki daina shirun nan Mami, yarinya kuma duk shegiyar da tace Khalil ne ya kawota gidan nan kice karya take, bai santa ba bai ma ta6a ganinta ba, babu sa hannunsa a zuwanta gidan, dama ai kowa ya sanki da taimako to wannan ma duk cikin taimakon da kika saba yi ne, amma babu ta inda khalil ya santa, kawai haka za ki ce masu, sannan hantara da tsangwama da kika ce baxa ma su ganta ba balle su yi mata, dakin baki na nan bangaren xata zauna, da safe ta tashi ta tafi makarantar ta, ta dawo da yamma to a ina za su ganta? Duk sanda na shigo Nigeria yin wani abu ta dawo wajena har sanda xan koma, ba shikenan ba?" Mami dai kallon Aunty Maryam kawai take ta kasa cewa komai, sallama aka yi a parlon duk suka daga kai.