Sashe 159
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
And you show ur evidence via 07087865788Mikewa Nihad tayi bayan ta tuna wayar da Aunty Maryam ta bata, ta sauko daga kan gadon ta tafi inda empty bags din suke ta duba wanda wayar ke ciki bata gani ba, mamaki ne ya cikata ta dinga kallon jakar, ta duba second bag din nan ma taga babu wayar babu alamarsa, Knocking aka yi a kofar dakin ta mike tsaye da sauri tana kallon kofar, can ta karasa ta bude taga Mimi a tsaye, Mimi tace "Ki fito mu ci abinci" Nihad tace "Toh" Mimi tace "At Mami's parlor" Nihad ta gyada mata kai, Mimi ta bar bakin kofar, komawa dakin Nihad tayi ta dau mayafinta tana kallon agogo, karfe sha biyu saura ake cin abincin rana kenan a gidan, ta dai nufi kofa ta fita zuwa parlon Mami tana tafiya a hankali, Mimi na zaune with 3 different foods a gabanta, Nihad ta karasa tana kallon abincin, Mimi ta nuna mata wajen da zata zauna, Nihad ta zauna, Sai ga mai aikin Mami ta shigo da ruwa me sanyi da drinks a hannunta ta ajiye masu tana kallon Mimi tace "Za a kawo fruit Salad din ne?" Mimi ta kalli Nihad tace "Will you take fruit Salad?" Nihad ta girgiza kai alamar a'a, Mimi ta kalli Bilkisu tace "No need" Bilkisu ta juya ta fita, Mimi ta zuba abinda xata ci a abincin gabansu, tayi ma Nihad alamar ta diba, Nihad ta dau plate ta debi shinkafa da miya, daga Nihad har Mimi cakalkala abincin kawai suke yi, ita Mimi sae danna wayarta take, daga karshe ta mike tana kallon Nihad dake mamakin wai har ta gama cin abincin kenan, Mimi tace "Let me go and brush My teeth" Nihad ta gyada mata kai kawai, Mimi ta fita daga parlon, ba a dau lokaci ba Noor ta shigo parlon kallo daya tayi ma Nihad ta dauke kai ta nufi dakin Mami ganin Mami bata nan ta juya ta nufi kofa zata fita, Nihad ta bi ta da ido har ta fita, Mimi na dawowa parlon ta kira Bilkisu ta waya ta zo ta fitar da sauran abincin daga parlon.... Har yamma Nihad na parlon Mami, wayar da bata gani ba yayi mugun tsaya mata a rai, kuma ta ma san wa zai dau wayar, Lokaci lokaci Mimi ke shigowa wajenta a parlon, seems basa wani zama nan bangaren sae Mami ta kirasu ko kuma sun shigo gaisheta, shigowar Mimi na karshe tace "Pls mu je ki rakani saloon xan yi gyaran gashi" Nihad tace "Toh" Mimi ta jirata har ta dauko Hijab dinta sannan suka fito Main parlor din gidan, Nihad sai estimating uban tafiyar da suka yi kafin su shigo ainahin parlon gidan wanda girmansa ya wuce misali take, the house is really huge, Tun da suka shigo parlon Aunty Hassana dake waya ta bi su da ido, can ta katse wayar da take tace "Ke Mardiyya zo nan" Mimi ta dawo tana kallonta, ko kadan Nihad wasn't comfortable at the way the woman was looking at her, Aunty Hassana tace "Wacece wannan?" Mimi ta kalli Nihad da tayi tsuru tsuru tace "Aunty bakuwa ce" Aunty Hassana tace "Bakuwar wa?" Mimi ta buda hannu tace "Bakuwar Mami" Nihad tayi karfin halin cewa "Ina yini" Aunty Hassana na kallonta daga sama har kasa tace "Lafiya" Mimi ta jawo hannun Nihad suka bar parlon, Sajida da shigowarta parlon kenan ta kalli Aunty Hassana tace "Wallahi Mama she is the one" Aunty Hassana tace "Anya kuwa? Naga wannan fara ce sosai fa" Sajida tace "I am telling you the fact, ita ce, bari in dauko wayata ki gani" Daga haka ta tashi da sauri ta tafi ta dauko wayarta ta shiga video tayi playing ta mika ma Mamarta wayar, Aunty Hassana tace "Toh ba cewa ku ka yi tare da wannan ɗan iskan suke ba? Kun ce shi ya kawota gidan" Sajida tace "We are not sure, kawai muna shiga parlon Mami muka ganta a zaune, kilan er uwarsu ce saboda yau da Aunty Maryam xata tafi ne ta sake dawowa gidan nan, all those while tana gidanta" Aunty Hassana tace "Kaiii, da yar uwarsu ce xan santa, da kyar dai in ba shi ya kawota gidan nan ba, idan kuwa ba shi bane ya aka yi sai da ya dawo ita ma muka ganta a gidan, amma ba komai xan samu yaya anjima idan ya dawo, ae dai baxa a kawo masa yarinya gidansa bai sani ba, xai min bayanin ko wacece" Nihad ta dinga kallon motar da wani mutumi sanye da camouflage yayi parking dai dai inda Mimi ke tsaye, ya sauka ya bude masu back seat, kana ganin shigar da Mimi tayi na English wear ga baƙin shade dinta a ido sannan ga wani jaka da ta rataye xaka san ba karya, she looks so cute and beautiful, Nihad bata ta6a jin da akwai wanda xata ji ya fita komai a rayuwa ba sai yanzu, ita da ganin kanta take babu ya ita, har University da take zuwa ma kallon kasa kasa take masu ba kowa take ma magana ba ko da kuwa an mata, don tana ganin ba class dinta bane su, sai gashi yanzu kawai taji ta raina kanta, Mimi na kallon Nihad ganin yanda ta ja gefe ta tsaya tace "Shigo" Nihad ta shiga motar ta kulle a hankali, mutumin ya ja motar aka bude gate suka fita daga gidan, Mimi ta ajiye wayarta da take dannawa tana kallon Nihad tace "Here is a question for you Nihad" Nihad ta dinga kallonta ba ko kiftawa, Mimi tace "How did u come to know my broda?" A hankali Nihad tace "Wanne?" Mimi ta ɗan yi jim tace "Yayana fa nake nufi, wanda ku ka dawo tare da shi dazu da safe" Nihad tace "Ohk, Yayanki ne?" Mimi ta buda ido tace "Yea he is my senior brother, we are having same father and same mother, Mami is our Mum, Noor is my senior sister, she is his immediate but ya girmeta sosai, ya bata 12 years, xan nuna maki ita idan mun koma gida kilan baku hadu ba har yanzu" Nihad sai kallonta take don truly Mimi na nugun kama da shi, both the nose and eyes, a hankali Nihad tace "Pls ki gaya min gaskiya gidansu ne wannan gidan da muka fito?" Mimi ta wara manyan Idonta tace "That's funny, he is the first and only male child of our father, did he tell you ba gidansu bane?" kallonta kawai Nihad take tana jin ita fa yanzu da ta ga ainahin cikin gidan da irin girmansa da kyau ta kasa yarda gidansu Khalil ne, ita kawai yanxu gani take kamar rikonsa ake a gidan ko kuma gidan ɗan uwan babansa ne, abinda ta saka a ranta kenan don she is beginning to get confuse ta yaya ma xa ace wannan gidan nasu ne, mutumin da yaje gidansu yake driving ana biyansa for almost a year, sannan har kauyensu ya kai ta, to me yasa xai kawota irin wannan gidan yanzu ta yarda nasu ne, Mimi da ke ta kallonta ta katse mata tunaninta tace "What are u thinking about?" A takaice Nihad tace "I am finding it hard to believe, and I don't think i will believe" Mimi tayi murmushi tace "Now i understand, he acted like he is a nobody right?" Nihad tayi shiru tana kallonta, Mimi ta shiga gallery dinta taje inda take ajiye hotunan yayan nata, wanda sun fi dari ta shiga ta mika ma Nihad tana kallonta, farkon hotonsa da Nihad ta gani ta dinga kallo babu ko kiftawa, sanye yake da farin labcoat with stethoscope round his neck, ta tafi next hoton, ta gansa cikin private jet an masa unaware picture, yayi crossing kafa yana danna waya with a serious face, ga tsadadden non-alcoholic wines a gabansa, designers ne kayan jikinsa, irin kyan da yayi kuwa a hoton ba ace wa komai, Nihad ta dinga kallon hoton don karya ne mutum ya kalli hoton bai sake kallo ba, bata san sanda tayi zooming ba still wanting to confirm and be sure shi din ne dai, taga wallahi shi ne, da zaka shiga zuciyarta kaga mamaki da shock da ya cika sa, a hankali ta tafi next picture din ta gansa a Newyork, then another in Los Angeles, Paris and another in United kingdom, infact duk yawanci hotunan a kasashen waje ne, wasu hotunan da turawa, wasu larabawa, she is really shock at all what she is seeing, sai kuma ta fara ganin hotunansa da Nadeeyah, a hotonsu na uku tare ta ki ci gaba da kallon, ta ɗan kalli Mimi dake danna second phone dinta giving it all her attention, tayi tapping dinta ta mika mata wayarta, Mimi tace "Are you done?" Nihad ta gyada mata kai, amsar wayar Mimi tayi ta mayar cikin jaka ta ci gaba da abinda take da dayar wayarta, har suka isa saloon din Nihad bata sani ba don tayi nisa tunanin da take, Mimi ta kamo hannunta tace "Dear" Firgit Nihad ta dawo, Mimi tayi murmushi tace "Mun iso" Nihad ta kalli mutumin da ya bude masu motar yana jiran su sauko, ta sauka daga cikin motar, sannan Mimi ma ta sauka, kallon wajen Nihad ta dinga yi tana imagining duk nan saloon ne? How big and beautiful, ganin yanda ta tsaya Mimi tace "Mu je" Nihad ta bi bayanta ta kasa daina kallon saloon din har suka shiga ciki, nan taga fararen mata ne masu gashi har gadon baya ke zuwa gyaran gashi wajen, har turawa da larabawa, kana ganin cikin saloon din kasan ba karya, Mimi tace "Ke ma kiyi gyaran gashinki" Nihad dai bata ce komai ba, da Mimi ta sake mata magana tace "Ohk" sai da suka 6ata kusan awa daya da rabi a saloon din daga karshe suka fito, har sannan kuma wanda ya kawosu na jiransu a motar, har suka isa gida Nihad na duniyar tunanin da ta fada, mamakin Khalil kawai take.... why then did he disguise himself and come to their house as a driver? What might be his mission? And who were those villagers he took her to and claimed they are his parent? Tambayoyin da take