Sashe 139
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maminsa yana tafiya a hankali, gaba daya ya rasa tunanin da xai yi, Mami ta dinga amsan gaisuwan da securities din cikin gidan ke mata, Nihad dai sai binta take tana satan kallonsu, back seat Mami ta bude tana kallon Nihad tace "Shiga" Nihad ta shiga motar a hankali, Mami ma ta shiga sannan ta kulle motar, bayan few minutes Khalil ya ja motar ya fita compound din bayan an bude masa wagegen gate din gidan, slowly khalil ke driving din har suka fita anguwan, sai a sannan yana kallon Maminsa ta madubi cikin sanyin murya yace "Where are we going Mami?" Mami tace "Take me to Maryam's house" Ya d'an sauke boyayyen ajiyar zuciya sannan ya nufi gidan Aunt dinsa, Nihad sai kallon anguwanni masu kyau take, amma kana mata kallo daya zaka san she is worried, suna shiga estate din su Aunty Maryam basu dade suna tafiya ba suka isa gidan, Khalil yayi horn bayan an bude gate din ya shiga yayi parking, Mami ta sauka tana kallon Nihad tace "Sauko" Nihad ta sauko, ta bi bayan Mami zuwa gidan, Aunty Maryam ta rungume Khalil tana welcoming dinsa cike da farin ciki tace "Idon son dina kenan nake gani haka?? Alhamdulillah ya Allah, Alhamdulillah" Murmushi kawai yayi ya gaisheta, ta amsa tana kallonsa daga sama har kasa, Lokaci daya er fara'ar fuskarta ya bace tace "Welcome son, Allah Ubangiji ya saka maka abinda aka maka" Murmushi kawai shi dai yake, Aunty Maryam na rike da hannunsa ta nufi parlor tana gaida Mami da ladabi, murmushi dauke fuskarta tace "Har kinyi Kumari yar uwa, Allah Ubangiji ya raba mu da mugun ji da mugun ganin" Murmushi kawai Mami tayi, Nihad dai sai kallon Aunty Maryam take don ita ma kana kallonta kasan halfcast ce, fara ce kal kamar Mamin khalil, sannan ita ma ga gashinta da tayi packing har kusan gadon baya, Aunty Maryam ta kalli Nihad don sai sannan ta lura da ita tace "Sannu da zuwa yan mata, shigo ki zauna" Nihad ta sauke kanta ta zauna kasa a hankali ta gaisheta, Aunty Maryam ta amsa tana Zaunawa gefen yayarta, tuni mai aikin Aunty Maryam ta cika gabansu da ruwa da lemo da kayan maqulashe, Aunty Maryam ta kasa daina kallon Khalil tana murmushi, she is so happy seeing him, can dai ta kalli Mami tace "Ya gida Aunty?" Mami tace "Alhamdulillah, kira mai aikinki ta shiga da bakuwar nan ciki ta bata breakfast naga bata wani yi a can gida ba" Aunty Maryam ta kalli Nihad tace "Ayya, to bari in kirata ta zo" Aunty Maryam ta kira mai aikinta a waya sai gata ta taho tace "Gani Hajiya" Aunty Maryam tace "Ki shiga da bakuwar nan guess room ki hada mata breakfast yanzu" Yarinyar tace "Toh Hajiya" Aunty Maryam ta kalli Nihad tace "Tashi ku je yan mata" Nihad ta mike a hankali ta bi bayan mai aikin da tayi wani bangaren daban da ita. Mami na kallon Khalil tace "Ko da za ayi sati admission letter din bai fito ba xata zauna nan har ta karba sannan ta koma gidansu" Khalil ya dinga kallonta ya kasa cewa komai, Aunty Maryam tace "Who is she Aunty?" Mami tace "Tare ya zo da ita" Aunty Maryam ta kallesa tace "Wacece ita din" yayi kasa da murya yace "Yarinyar mai gidan da na zauna a kano" Aunty Maryam tace "Allah sarki, Admission take nema nan din?" Ya gyada kai kawai, Aunty Maryam tace "Lallai ya yarda da kai tunda har ya bar ka da yar sa har ku ka taho tare, Allah Ubangiji ya saka masa da alkhairi" Khalil dai bai ce komai ba, Mami tace "Ameen" Mami ta kalli Aunty Maryam tace "Yaushe tafiyar naku, naji shiru baki ce komai ba" Tace "Ohh wllh yace sai yayi settling a can kafin mu bi sa, may be nan da sati biyu in sha Allah" Mami tace "Toh Allah ya kai mu" Aunty Maryam tace "Ameen" Khalil yayi kasa da murya cike da karfin yace "Mami about that video.... yan dakinsu ne a makaranta suka mata bata sani ba, sannan suka saki a social media... the Case is silently in court now, mahaifin nata yayi sueing dinsu gaba daya, so that's why zai canza mata makaranta yanzu, since the incident yake processing admission dinta a nan garin so coincidentally xan taho sai yace mu taho tare da ita" shiru yayi cause he him self knows he sounds so stupid, there is nothing making sense in what he is saying, Mami tace "Toh ni ka ji nace wani abu Khalil? Allah dai ya tsare mana zuri'a gaba daya, kawai ta zauna nan har sanda xa ta amshi abinda ta zo amsa sai ta koma gida, ae shikenan ko...." Aunty Maryam dake ta kallonsu tace "Wai me ke faruwa?" Mami ta sauke ajiyar zuciya briefly tayi mata bayanin abinda ya faru daxu da safe da yara suka shigo, Aunty Maryam ta saki baki da mamaki looking speechless, can ta kalli Khalil tayi kasa da murya tace "Wai kana nufin wancan ita ce yarinyar da video dinta yayi trending weeks ago?" Khalil bai iya yace komai ba, Aunty Maryam ta girgiza kai hankali tashe tace "Amma ta bata wayonta, tayi tarnishing image dinta a idon duniya, ta kuma yi ma kanta ta6on da goguwansa sae wani ikon Allah, duk yanda aka yi bata ji, banda bata ji meye zaki zauna daga ke sai skimpy inner wears a daki har maki video kina dariya, kai ai abun nan bai min dadi ba wallahi, Allah Ubangiji ya tsare mana zuri'a, amma wannan ta6on ai baxai gogu ba har tsawon rayuwarta sai ma ta tashi aure zata gane hakan barin idan tana da mahassada" Kallonta kawai Khalil yake baya cewa komai, Aunty Maryam ta rike ha6a cike da jimami tace "Kaii, sai kawai naji bata burgeni ba don bana son yaro mara kamun kai, don da tana da kamun kai da babu yanda xa ayi tayi abinda tayi, babu yanda xa ayi hakan ya faru da ita, wallahi ranan da naga videon ta sai da nayi tashin dare nayi addu'a Allah ya kare mana xuri'a da al'ummar Musulmi baki daya, abun sam babu dadi, gashi babu inda wannan videon bai je ba, kuma kun ga wllh ban ganeta ba ni banda kun yi magana, to ma banda abun uban nata ai aurar da ita kawai ya kamata yayi a yanzu ba wai ya sake biya mata makaranta a wani wajen ba, tana kanon ma a gabansu tana shakiyanci ina ga ta hadu da yan matan garin nan ai kuma sai abinda hali yayi, gata wata sumu sumu kamar bata magana... To kai garin yaya kasan mahaifin nata?" Khalil ya sauke idonsa kasa, Mami dai sai kallonsa take, Aunty Maryam tace "Kayi shiru" Ya dago ya kalleta a hankali yace "A sanda na sauka a kano bani da kowa bawan Allahn ya rike ni tamkar dan sa, yayi accomodating dina, yayi feeding dina without knowing who i am, mahaifiyarta mace ce mai kirki warce saboda ita nayi dadewar da nayi a tare da su, ina jin ta kamar ke da Mamina a gidan, yayyinta maza kuwa zaman mutunci da girmama juna muka yi da su, basu ta6a nuna min ni ba dan gidan bane, haka sauran yan uwanta mata dake gidan, abinda nake so ku gane, ba wai na je masu da real identity dina bane, i went der as a nobody, babu wanda yasan wanene ni har yanzu da nake maku magana banda ita yarinyar yanzu, amma suka min karamci a irin wannan zamanin da muke ciki, i know i can never repay them their good deeds, kuma yace in taho tare da yarinyarsa ta amshi admission letter saboda wani mistake nata sai in ki?" Aunty Maryam ta sauke ajiyar xuciya tace "Baxa ka ki ba kam, amma surutun yan gidan nan naku ake gudu" Mami ta kalli Aunty Maryam tace "That is it dear, abinda na guda kenan na kawota nan gidan har ta gama abinda ya kawota ta koma, banda mu da muka san wannan labarin da ka fada a kan gidansu yarinyar waye ya sani? Nobody, kai ko sun ji cewa xa su yi karya kake, don haka duk abun magana gudunsa nake nan da ka gan ni, daxun ma da suka shigo ba saboda Allah bane, gulma ce ta kawosu, yarinyar kawai suka zo gani, ita kuma wannan yarinya ta bata wayonta don waje daddaya ne xata je aki ganeta, Allah dai ya kiyaye ya tsare mana zuri'a, ya bata mijin da xai aureta yayi overlooking mistakes dinta ya rufa mata asiri duniya da lahira, da da mijin ma da auren kawai yayi mata ta ci gaba da karatun nata a dakin mijinta don hakan zai fi mutunci, Allah dai ya takaita mata gori a duk inda xata kasance" Khalil dai kallonsu kawai yake, Aunty Maryam tace "Ameen, da ganin wannan lamari kasan influence na bad friends ne hade da rawan kai irin na yaran yau, saboda haka ne ya kamata mu kara sa ma yaranmu ido sosai" Wayar Mami ya fara ring ta daga ta kai kunne, bayan sun gaisa tace "Lahh ai gani a gidan Maryam, kin fito ne?" Mami tace "Yauwa to, kawai ki taho nan din idan kin fito, shima yana nan ai" Daga haka ta katse wayar, Aunty Maryam na kallonta tace "Wacece?" Mami tace "Hajiya Safeenah ce" Aunty Maryam tace "Allah sarki, taji sauki kenan" Mami tace "Aa da sauki sosai, 3 days ago ma ai taje can gida wajena" Aunty Maryam ta mike tace "Bari inje in sanar ma mai aikin can tayi mata wani abun kafin ta iso" Daga haka ta bar parlon, Mami na kallon Khalil tace "Wai fasa tafiyar kayi yau Khalil?" khalil na danna wayarsa yace "Sai na shirya Mami" Aunty Maryam ta ɗan tsaya kitchen din tayi assisting mai aikinta bayan da ta gama hada komai ta bar mata ta fito parlor, duk bata tarar da su a parlon ba, har zata wuce sama sai kuma tayi bangaren guess ta kara ganin Nihad, don kawai abun ya tsaya mata a rai tun daxu, bude kofar dakin tayi ta shiga ta ganta zaune kasa ta jinginar da kanta da