← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 156 OF 165

Sashe 156

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma tace "Ayya inna ai suna can garinsu da ita" a tsorace Inna tace "Garinsu? Ina ne garin nasu? Buzu ne fa, ba shi da wani gari da ya wuce Nijar, Nijar din ya kinkimi jikata ya kai kuna gani baku hanasa ba? ta ina zata fara da zafin saharar su, ga shi ance mana ana ta juye juyen mulki a can yau kwana da kwanaki, ni da Abubakar muna ta jimami" Umma tace "Aa Inna, garin zaria ya tafi da ita" Inna ta saki baki, can tace "Kan uba, ku ka bar sa ya tafi da ita wannan garin, ai duk ɗan kano yafi karfin zama a can, Sannan da xai kai ta can din wani shegen ya bi su a cikinku??" Umma tace "Haba Inna, ai sun je sun dawo ya fi a kirga, Nihad fa ta sake fiye da yanda kike tunani Inna" Inna tace "Kai nima dai wallahi da na tsaya nake biye maki kamar wata er wiwi, maganina ma kenan, matsa ki ban waje wajen Ibrahim na zo ba wajenki ba, kai kuma Ibrahim wajenka na zo ba wajen Sumayya ba" Abba yace "Toh ya kike son ince Hajiya? Dama ana zuwa cigiyar wanda kulawarsa da komai nasa ya fita daga hannun iyayensa? Ai ni tuni na mikata garesa, alaqarsa da ita ya fi namu yanzu, don haka duk inda ma ya kai ta dai dai ne, ba ruwana, ba ruwanki, ba ruwan kowa" Inna da ta saki baki tana kallonsa tace "Yau ba lafiya, kace ba ruwanka Ibrahim?" Yace "Toh hanasa tafiya da ita xan yi?" Umma na murmushi tace "Banda abunki Inna mata da mijinta ki zo cigiyarta a gidansu, ita da gidan nan kuma ai sai dai ta kawo mana ziyara, idan aka ganta gidan nan yanzu ai ba lafiya kenan, kuma wallahi ko sati ba ayi ba sun zo gidan nan da shi sun mana sallama kafin su tafi Zarian wai garin mamarsa ce, kawai dai ba ku da rabon ganawa ne, amma yace ba jimawa xa su yi ba za su dawo, suna dawowa kuma da kaina xan je can gidan in dauke ki in kaiki gidan nasu" Inna tace "Toh wai ni shikenan nuna masa ku ka yi bani da matsayi ne da tun da aka aura masa ita daga shi har itan babu wanda ya taka yaje inda nake yace min ci kanki? duk da dai naje Bauchi kwanan nan na dawo" Umma tace "Au ashe dai kinyi tafiyar dai, to ki dai yi hakuri Inna, sun je ne baki nan, ki tambayi yan gidan kilan basu gaya maki bane da kika dawo" Inna tace "Kai Ibrahim fito za mu yi magana" Daga haka ta juya ta nufi kofa tace "Don ban ga xan iya magana gaban kwaɓeɓiyar nan ba" Abba ya mike ya bi bayanta suka fita, Umma ta bi ta da harara, can ta ja tsaki tace "A haka dai" Ranan alhamis Aunty Maryam suka fara shirye shiryen barin Nigeria tare da mai aikinta da yaranta mata biyu da ke wani boarding school a nan Abuja, duk sai jikin Nihad yayi sanyi, the present of Aunty Maryam use to make her feel strong, it's making her move on with life, tana kara samun kwarin gwiwa har ta mance duk wata damuwar da take ciki and now she is leaving her, Aunty Maryam na lura da sanyin da Nihad tayi, and she felt really sorry for her, she wish she could do something about it, she wish xata iya tafiya da ita inda xa ta, daren Thursday Aunty Maryam ta idar da sallahn da take a sama ta sauko kasa ta karasa sauran kintse kintsen da bata yi ba a gidan don ranan Asabar za su tafi, har xata koma sama sai kuma ta tafi ta bude dakin Nihad duk da taga jiya bata yi tashin daren ba da ta leka ta, zaune ta ganta kan darduma ta hade kai da gwiwa, ta dago kai jin an bude kofar dakin, Aunty Maryam ta shigo dakin ganin idonta tace "Kukan me kuma kike Nihad?" Wasu sabbin hawayen suka ciko idonta ta kasa cewa komai, Aunty Maryam tace "Talk to me, why are you crying?" cikin rawar murya Nihad tace "Aunty you are leaving me... idan kika tafi kika bar ni i don't have anybody here" tana fadin haka ta fashe da kuka, Lokaci daya jikin Aunty Maryam yayi sanyi ta dagota ta zaunar da ita gefen gado tana kallonta cikin sanyin murya tace "Ke da zaki fara makaranta Nihad, sannan wajen yayata fa za ki zauna, she is also nice, you will like her so much, and Khalil is also there for you always" kuka kawai Nihad take don tasan idan Aunty Maryam ta tafi shikenan she might go back to her former self, there will be no one to encourage her anymore, har ranta bata son gidansu Khalil, she don't think she can cope staying there, ganin yanda take kuka Aunty Maryam ta jawota jikinta cike da tausayinta tace "Kiyi hakuri Nihad, bana son kina wannan kukan, ni ma ina son mu zauna dake kawai bani da yanda xan yi ne, but even with my absence baxa kiyi lacking komai ba" Kai kawai Nihad ta daga mata hawaye na sauka idonta, Aunty Maryam tace "Je ki wanke fuskarki ki zo ki kwanta" Tashi tayi a hankali ta tafi bandaki ta wanke fuskarta ta fito ta hau saman gadon amma wasu hawayen ne ke zuba idonta, mikewa Aunty Maryam tayi jikinta a sanyaye ta fita daga dakin, ita kanta tasan in dai ba khalil na gidan ba zaman gidan ba lallai yayi ma Nihad sauki ba, duk excuses da Mami ta kawo a kan dalilin da baxata riketa ba gaskiya ne, amma saboda babu wani option yasa Aunty Maryam duk tayi shunning excuses din. Washegari friday tana dakinta tayi dialing number Khalil, yana fara ring ya daga bayan sun gaisa tace "Baxa ka dawo weekend ba?" Yace "Ina airport yanzu haka, in sha Allah yau xan dawo" Aunty Maryam tace "Toh kana sauka ka daure ka fara biyowa ta nan gidana" Yace "Ohk, hope all is well?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Yaushe ne tafiyar Aunty?" Tace "Gobe in sha Allah" Yace "Ohk, sai na dawo in sha Allah" Sallama suka yi ta katse wayar, gaba daya ta kasa sauka gun Nihad don har ranta bata son ganin kukanta. Wajen karfe biyu zeenah ta shigo wajenta a daki tace "Ummi why is ur visitor crying since morning?" Aunty Maryam ta kalleta tace "Go and mind ur business please dear" Ta zaro ido tace "No i was only trying to show concern" Aunty Maryam tace "Je ki kira min ita" juyawa tayi ta fita daga dakin, Bayan wani lokaci sai ga Nihad ta shigo parlon Aunty Maryam tana tafiya a sanyaye, bata yarda sun hada ido ba ta zauna kasan Carpet, Aunty Maryam ta dinga kallon idanuwanta da suka kumbura, can ta sauke ajiyar zuciya tayi kasa da murya tace "Wajen yayata ne baki son zama Nihad?" Girgiza mata kai kawai Nihad tayi bata ce komai ba, Aunty Maryam tace "Toh ki gaya min inda kike son zama" cikin sanyin murya Nihad na wasa da gefen gyalen jikinta tace "Bani da inda zan zauna" Aunty Maryam tayi shiru tana kallonta cike da tausayinta, irin wannan yarinya karama haka ace wai an koreta daga gida, why? to yanxu da ba don Khalil din ya taho da ita ba da ya zata yi kenan, sai da ta shiga duniya kenan tunda gashi wai dangin mamarta basa nan, what a cruel world we are in, how comfortable is this her step mum now da tasa aka kori yar teenager haka daga gida saboda selfish interest dinta, lallai duniya abun tsoro, bayan few seconds Aunty Maryam tace "Je ki zuba abinci ki ci" Tashi Nihad tayi ta nufi kofa ta fita daga parlon. Karfe hudu saura Khalil ya shigo gidan ya tarar da Aunty Maryam dake parlonta a zaune, tayi welcoming dinsa ya zauna sannan ya gaisheta tace "Ya hanya?" Yace "Alhamdulillah" Kallonta kawai yake yana jiran ya ji kiran da take masa, Ta sauke ajiyar zuciya tace "Kjay, ina tunanin halin da Nihad xata shiga idan na tafi na bar ta a kasar nan, she's been crying since 2 days ago, i feel really sorry for, she is too young to be passing through all this, tana bukatar tausayawa da soyayya irin ta uwa, ban san yanda xan yi ba...." Kallonta kawai khalil yake, can a hankali yace "Aunty ba wajen Mami za ki bar ta ba?" Aunty Maryam ta girgiza kai tace "Kai ma kasan mun banbanta da Mami ta ɓangarori daban-daban, yanda na jawota jiki har ta sake ta buda min cikinta Mami baxata yi haka ba, sanyinta baxai bari tayi hakan ba, ko me xa ayi mata a gidan kuma nasan iyaka Mami tace tayi hakuri, toh da wanda ya dameta zata ji ko da na yan gidanku KJay?" Khalil dake ta sauraronta yace "Toh meye shawararki Aunty?" Aunty Maryam tace "I am thinking of telling Abu Zeenah sai mu tafi tare da ita ƙasar da za mu" Khalil was speechless at first, can yayi karfin halin cewa "Aunty karatun nata fa?" Aunty Maryam tace "Sai a samar mata a can ta fara" Yayi kasa da murya yace "But i have paid all the fees, kuma kinga ai na kashe kudi da yawa, ni kuma baxan wani iya bin processes din refund ba" Aunty Maryam tayi shiru tana kallonsa, ya kwantar da murya yace "Kar ki damu Aunty in sha Allah she won't be uncomfortable as you are thinking, beside Mimi na gidan, nasan baxata bari ana ci mata fuska ba, sannan nima next week zan gama abinda nake a can in dawo Nigeria gaba daya" Aunty Maryam still ta kasa cewa komai but deep down her tausayin Nihad kawai take ji kawai tana jin da kawai ya bari sun tafi da ita, shi dai kallonta kawai yake hoping she is convinced, daga karshe tace "Shikenan, Allah yayi mana me kyau, Allah ya bata ikon kwantar da hankalinta a gidan naku" a hankali Khalil yace "Ameen" Aunty Maryam tace "Ba komai, ka tafi gida kawai, gobe da safe za mu hadu
Chapter 156 · 0% Book details