← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 165

Sashe 140

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

gado, Aunty Maryam na kallon abincin dake ajiye tace "Baki yi breakfast din ba?" A hankali Nihad tace "Na koshi" Aunty Maryam tace "Toh fito parlor kiyi kallo, yara sun jogane kayan kallon nan din sai an gyara" Nihad dai bata ce komai ba ganin Aunty Maryam ta juya ta mike a hankali ta bi bayanta, har suka fito parlor tare, nan din ma a kasa ta zauna, Aunty Maryam ta tafi ta kulle kofa sannan ta wuce sama wajen Mami, Khalil na kwance saman kujera Mami na basa labarin abubuwan da suka faru baya nan, Aunty Maryam ta zauna kenan aka kira Mami, Mami ta daga tace "Kin iso ne?" Sai kuma Mami tace "To bari a bude" Katse wayar tayi tace "Kin kulle kofar parlon ne Maryam?" Aunty Maryam ta kalli Khalil da sauri tace "Dr ka bude mata kofa, yanzu kuma na kulle kafin in hauro" Ya mike ya fita daga parlon ya sauka downstairs, Nihad na zaune ta k'ura ma Tv ido duk da ba fahimtar abinda ake yi a ciki take ba, kallo daya yayi mata ya nufi kofar parlon ya bude, Da ladabi ya gaisheta yayi mata sannu da zuwa, da fara'a tace "Maa sha Allah, ka dawo lafiya Khalil?" Yace "Alhmdlh mum" Tace "Toh Alhamdulillah, sannu, Allah Ubangiji yayi maka albarka" Yana murmushi yace "Ameen" Sannan ya koma gefe ta shigo parlon, ya juya ya nufi inda remote yake ya dauka don rage volume din Tvn, a hankali Nihad ta gaisheta ta amsa da fara'a, Khalil Yace "Suna sama Mumy" Upstairs ta nufa, Kamar ance ya juya ya ganta ta jingina da kofar parlon tana kallonsa tana murmushinta me kyau, wara ido yayi kafin yace komai ta taho da sauri ta rungumesa ta lumshe ido a hankali tace "I have missed you so much" Daga kai Nihad tayi ta kalleta, shi kam yayi stiff a wajen da yake duk ya daburce cause she took him unaware, Lokaci daya ta lura da Nihad dake wajen da sauri ta sakesa ta koma baya tana mata murmushi tace "Sannu, sorry i just badged in, Assalamu alaikum" Nihad dake kallonta daga sama har kasa ta dauke kai kawai, Khalil ya bude palm dinsa with surprise yace "But you didn't say u are coming with Mum" Ta langwabar da kai smiling at him tace "Surprise" Kallonta kawai yake, a hankali hawaye na taruwa idonta tace "I missed u so much..." Ya mata wani kallo yace "Come off it dear" Lokaci daya Nihad ta mike ta fice daga parlon zuwa guess room da take ciki daxu, Nadeeyah ta bi ta da kallo, sai kuma ta kallesa tace "Dear Wacece ita? Ko dai taji haushin yanda na shigo ko? Wallahi i was just overwhelmed" Khalil ya daga kafada yace "No, kece dai kika ga haka...." Tace "Ohk, tayi hakuri in ma taji haushina ne, where is Mami?" Ya nuna mata sama tace "Let me go and greet her" yace "Ohk dear" Tana barin wajen ya bi ta da kallo har ta haura sama.....
Chapter 140 · 0% Book details