← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 165

Sashe 52

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yana nan Hajiya" Inna tace "Toh saboda me? Shi Ibrahim din ne ya bar sa ya ci gaba da zama a gidan ko ko? Yau naga fitina" Aminu yace "Ae ba shi da matsala fa Hajiya, kowa a gidan ya shaida, kullum nan muke yini tare da shi" Inna tace "Aa rufe min baki Aminu, wllh in nice a gidan nan da ido daya zan dinga bacci" Tayi kasa da murya tace "Irinsu ne fa ke aikata mugayen abubuwa a duniya yanxu Aminu, ko kai baka ga siffarsa ba, wannan idan cacan baki ya hadaka da shi sai dai ya daga ka ya nana shege da kasa, to bai cuceka ba? Da nayi niyyar kwana amma gaskiya baxan iya ba da wannan mutumi a gidan nan, ina dalili" Dariya kawai Aminu yake, Inna tace "Bari in shiga mu gaisa da su kawai inyi fitowata in wuce" Daga haka ta wuce cikin gidan, tana zaune parlor da Mumy dake ta sauraronta Khalil yayi sallama bakin kofar, Inna tayi kasa da murya tace "Kaddai shi ne? Har nan ku ke bari ya xo maku??" Mikewa Mumy tayi ta nufi kofa, Khalil ya gaisheta da ladabi ta amsa tana tambayarsa ya aiki, yace "Alhamdulillah" ledan hannunsa ya mika mata yace "Sakon Hajiya ne" Mumy ta amsa ta juya ta koma cikin parlon, inna ta hangame baki ganin leda shake da manyan apples tace "Meye wanan din? a ina naga kudin biyan wannan apple cike a leda, amma dai wawa ne wannan yaron, maza ciro kwara biyu ga dari biyu ki basa, sauran kuma ya mayar yace ance baxa a siya ba" Mumy na kallon Inna tace "Wai da na nawa kika ce ya siyo inna?" Inna tace "Aa ni ban aikesa ya siyo ba, kawai cewa nayi yaje ya tambayo nawa nawa ne, ni ban aikesa ya kwaso min ba wallahi" Mumy tace "Atoh ina amfanin mayar da abinda aka riga aka karbo Inna" ko rufe baki Inna bata jira Mumy tayi ba ta mike ta fixge ledan tace "Ai ba sata nake yi ba da xan siye duk apple din nan, kuma 'ya yana ba kudin banxa suke samu ba" Tana gama fadin haka ta fita waje da sauri, can bakin gate ta hango khalil a zaune tace "Yau naga gantalallen mutumi, wa ya bamu kudin siyan wannan uban apple din, ko don ya ga makeken gida ya zata sata ake yi" Tana isa kusa da su tayi kasa da murya tace "Ɗan nan cewa nayi ka tambayo nawa nawa ne, bar ganina haka, wllh rufin asirin Allah kawai nake takama da shi, bani da komai, maza ka maida masu kace biyu aka aiko ka kaji" Khalil yace "Aa Hajiya na siya maki ne kawai ki ci" Inna tace "Ka siya min? Ko dai lemo ka kwaso min?" Tana fadin haka ta kara bude ledan da sauri tana lekan ciki, ai ko taga apple ne ya fi goma, Inna ta gwalo ido tace "Albashin naka ka kwashe ka siyo min apple din?" Khalil yayi murmushi kawai, Inna ta rike ha6a tace "Kaii amma wallahi nagode, Allah yayi maka albarka, ko jikokina babu wanda ya ta6a min haka cikinsu, dari uku uku fa ake siyar da duk guda daya" Shi dai khalil murmushi kawai yake, Tace "Amshi ledan mu shiga Maryam ta maka godiya" Da sauri yace "Aa Hajiya" Inna tace "Amsa kawai mu tafi nace" Amsan ledan yayi tana gaba ya bi bayanta har main parlor, tana ganin ya tsaya bakin kofa tace "Aa shigo kanka tsaye" Still yaki shiga, Inna tace "Wai ba ni nace ka shigo ba, ni fa na haifi me gidan" Mumy dake kallonsu tace "Ka karaso" Shiga parlon yayi da sallama, Inna ta kulle kofa tana nuna ma Mumy ledan tace "Wllh Maryam ashe siya min yayi da albashin sa, kin dai ga bare ne fa amma yasan kyautata ma tsohuwa" Mumy tace "Toh Allah ya saka da Alkhairi, maa sha Allah" Inna tace "Allah sai naji ya fiye min Hamid da su Farooq sau dubu" Mumy dai bata ce komai ba, Inna ta rike ha6a tace "Allah yayi maka albarka ka ji" Yace "Ameen Nagode" Bude kofar parlon aka yi Nihad ta shigo, still tayi bakin kofar tana kallon Khalil da mamaki, sai kuma ta kalli Inna da Mumy tace "Me wannan kuma yake yi har cikin parlor?" Mumy tace "Uwarki yake yi" Nihad ta hade rai tace "Mumy parlon mu fa, privacy dinmu, this is uncalled for gaskiya, ko su Aminu da suka yi shekara da shekaru a gidan nan xa a bari su shigo nan balle wannan driver din..." Mikewa Mumy tayi tana ganin haka tayi hanyar stairs da sauri, Mumy bata fasa bin ta ba, Inna tayi kasa da murya tana kallon Khalil tace "Wallahi duk hakuri muke da ita, duk ta fi karfin kowa in gaya maka, shi yasa kwanaki da ta je ta kai karar ka gu na wai in sa a kore ka nace waa? Me ka min xan maka sanadin aikin ka, wllh naki biye mata shine ta kullace ni har yau, dama dai bansan mugun halinta bane shine xan biye mata amma ai kaga ban biye mata ba gashi har yanxu kana aikinka cikin rufin asiri har da siyo min apple, ni duk inda harkar rashin gaskiya take ba ni a ciki, Nihad kam bata da gaskiya wllh" Khalil dai kansa na kasa, Inna tace "In ji suna baka abinci isasshe dai?" Yana murmushi yace "Ehh ana bamu" Inna tace "Toh shkkn, can gidan Habubakar din ma ka iya dinga xuwa kullum, ai yanxu kam ka zama ɗan gida" Murmushi yayi yace "Nagode Hajiya" Tace "Yauwa je ka" Juyawa yayi ya fita daga parlon. Da daddare Nihad na kitchen tana pancake da xata ci kafin ta kwanta Sudais ya shigo kitchen din, cup din hannunsa ya ajiye a sink yana kallonta yace "Lahh Aunty Nihal ma tace mana tayi pancake ta ci yau a makaranta" Nihad na juya pancake dinta ba tare da ta kallesa ba tace "Did u spoke with her today?" Yace "Yess, Uncle driver ne ya kira mana ita, muna ta magana da ita for long" Juyawa Nihad tayi ta ajiye spatula din hannunta tace "Who is uncle driver?" Yace "Wannan da yake kai mu school" Ta bude baki, sai kuma tace "Yaushe ya kira maku ita?" Sudais yace "After magrib prayer" Sake baki Nihad tayi tana kallonsa, jin kaurin pancake dinta ta kashe gas din da sauri ta fita daga kitchen din, sama ta tafi bangaren Umma, har bedroom ta shiga ta sameta tace "Umma kinsan da wa Nihal ke waya yanxu?" Umma tace "Wa?" Nihad tace "Wai driver, yanxu su Sudais suke ce min ai ya kira masu ita, ranan da xa mu je shopping ne fa ya amshi numberta, toh a ranan da xa mu kai ta school ma ya kirata ya fi a kirga, sai ga yanxu su sudais suka xo suna gaya min ai driver ya kira masu ita" Da wani expression Umma tace "Driver? Wani drivern ni Sumayya?" Nihad tace "Driver dae da kika sani" Umma tace "Ko dai Nihal ta fara hauka ne?" Nihad ta kyabe baki ta zauna gefen gado, Umma ta dau wayarta ta hau kiran Nihal, yana fara ring Nihal ta daga, Umma tace "Nihal kiran me ku ke yi ke da drivern gidan nan?" Nihal tace "Driver kuma?" Umma tace "Ban sani ba" Nihal tace "Wallahi ba komai Umma kawai wani lkcn yana ba su Sudais ne mu yi magana da su" Umma ta kunduma mata zagi tace "Kanin uwarki ko na ubanki? Banda xubar da aji meye na wani waya da drivern gidanku? Sa'anninki na waya da mutanen arxiki ke kina waya da driver, ke wace irin yarinya ce? to wllh xan ci kaza kazanki idan baki kama kanki kin goge number tasa ba, kaji min gantalalliya dai" Nihal dai tayi shiru, Umma tace "Na dai gaya maki tun wuri ki goge number nan ko in ci maku ke da shi" Umma na kai wa nan ta katse wayar, sosai ranta ya baci, ita kam wace irin yarinya ce Allah ya bata, duk abun kaskantar da kai ta iya shi, banda haka meye ya kai ta dinga waya da driver, Nihad tace "Wllh Nihal is so annoying, how comfortable is she making call with that wretched man" Umma tace "Ki kyale mahaukaciya mana" Nihad ta mike ta tabe baki ta fita daga dakin, Zaga dakin Umma ta dinga yi. Nihad na gama pancake din ta shiga bangaren Abbanta, bayan ta gaishesa tayi shiru saboda Mumy dake zaune a parlon, Abba ya kalli Mumy, murmushi kawai tayi ta mike ta bar masu parlon, Abba na kallonta yace "Ya aka yi daughter?" A hankali tace "Abba na tambayi wata kawata gyaran screen din wai 150k ne" Abba yace "Har 150k?" Ta marairaice tace "Eh Abba" Shiru yayi, can yace "Ohk gobe zan tura maki, amma baxa ki wajen gyaran ke kadai ba, ko ku je da farooq?" Da sauri tace "Aa Abba ba kace driver ba?" Abba yace "Ohk, no problem sae ku je tare, kin gyara account din naki ne?" Tace "Aa sae next week, I'm busy with lectures throughout this week" Abba yace "Ohk xan sa kudin a account din Farooq sae ya baki" Ta hadiye abu da kyar sai kuma tace "Abba driver din bashi da account?" Abba yace "No I don't know" Tace "Abba idan yana da shi kawai ka sa mashi tunda tare xa mu, ba sae ka tura ma ya Farooq ba" Yace "Ohk, Allah ya kai mu goben" tace "Ameen" mikewa tayi bayan ta ma Abba sae da safe ta fita tana Murmushi, tana da kusan 70k a account dinta, ga kuma dala dari biyu da Aliyu ya bata, now with additional 150k from her father, latest iphone is sure gobe. Washegari Nihad na ta kallo ta window har Khalil ya tafi ajiye su Amina a makaranta, Hijab ta saka har kasa ta sauko, gun Aminu ta nufa yace "Barka da Safiya Hajiya" Tace "Aminu ina son tambayarka ne don Allah" Aminu yace "Toh Allah ya sa na sani Hajiya" Tace "Yaron nan Driver yana da account number ne?" Aminu yace "Anyaa, gaskiya ban ta6a jin yace xai
Chapter 52 · 0% Book details