Sashe 43
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
ya fito duk suka shiga motar, Mumy na tsaye balcony bayan tayi ma Nihal addu'ar Allah ya kai ta lafiya Allah ya tsare, Ummu ma na balcony din a tsaye, a duk sanda Nihal xata koma makaranta sai ta ji kamar xata yi xaxxabi, duk cikin yaranta babu wanda take ji har ranta kamar Nihal, a haka har farooq ya gama warming motar ya fita, Aminu ya daga masu hannu yana cewa "Allah ya bada sa'ar karatu, ku kuma Allah ya maido ku gida lafiya" Nihad da ke xaune back seat ita da Nihal ko kallonsa bata yi ba, Farooq da Nihal kadai suka amsa da Ameen.... Bayan sun dau hanya wayar Nihal dake jakarta ya fara ring, Nihad ta juya tana kallonta, bude jakar tayi ta fiddo wayar tana kallon screen din ta ga Khalil, Nihad ta kikkifta ido don ta kara tabbatar da sunan da ta gani a jiki, bata san sanda ta bude baki ba don mamaki, Nihal ta daga kiran ta kai kunne, Dubara Nihad tayi ta matsa dab da ita ko xata ji abinda xai ce, daga daya bangaren Khalil yace "Kin tashi lafiya Hajiya?" Nihal tace "Alhmdlh, ina kwana?" Yace "Lafiya, ban samu damar kai ki ba, kuma kin tafi ba mu yi sallama ba, Allah Ubangiji ya tsare hanya, ya kai ku lafiya, ya baki sa'ar abinda aka je nema" Ta sauke idonta kasa tace "Ameen nagode" Yace "Sai anjima" Tace "Nagode" Katse wayar yayi, Nihad ta matsa tana kallonta da kyau tace "Nihal ba driver din nan bane ya kira ki?" Nihal ta ki cewa komai, Nihad ta saki baki tana kallonta, Farooq dake jin su yace "Wani Driver?" Da sauri Nihad tace "Ji fa yaya, driver din gida fa, meye hadinta da shi har ma zai kirata yanxu??" Farooq dai sai kallon Nihal yake ta madubi, Nihal ta hade rai tace "You have problem Nihad, komai ke sai kin san yanda kika yi kika canxa masa ma'ana, what's wrong with me having the drivers number, naga har number Saminu ina da shi me yasa be xama laifi ba? Ke lkcn da Habibu yake nan baki da numbersa? Waye yafi communicate da Habibu a gidan banda ke?" Nihad tace "Noo, ae Habibu daban wannan daban, kuma Habibu sai ta kama muke magana da shi a waya...." A fusace Nihal tace "Toh wannan din ma kamawa yayi muka yi maganar a waya" Farooq yace "Toh wai ke Nihad ina ruwanki??" Kallonsa Nihad tayi, lkci daya ta hade rai bata ce komai ba, yace "Ke ce ai kika dau girman kai kika daura ma kanki but there is nothing wrong to have people that are under you phone number" All through the journey Nihad bata sake cewa komai ba amma fuskarta a daure yake. Satan kallon Nihal take taga tana bacci, a hankali ta dauke wayarta dake kafarta ta bude don ita bata sa password, ta shiga call logs tayi blocking number Khalil sannan tayi deleting ta mayar mata da wayar ta ajiye. Har Nihad suka kai Nihal Zaria bata ce ma kowa komai a motar ba, Farooq ya kalleta yace "Sauka ki kama mata kaya ku shiga hostel" Ta ɗan daure fuska ta bude motar ta sauka, nan ta taya Nihal suka kwashe kayanta xuwa hostel din, bayan Nihad ta ajiye jakar karshe ta juya xata wuce Nihal tace "Are u still angry? Toh kiyi hakuri" Nihad ta kalleta tace "Baxan yi ba, ba dai driver ya fi ni ba" Nihal tayi Murmushi tace "Ya xa ayi driver ya fi ki, kema kinsan babu wanda ya fi ki a wajena, kiyi hakuri i didn't mean to make u angry" Nihad ta harareta tace "Kamar da gaske" Rungumeta Nihal tayi tace "Wllh kema kinsan da gaske nake blood" Nihad tace "Toh shkkn na hkura" Nihal tace "Toh nagode" a tare suka koma gun mota inda Farooq ke jiran Nihad, Nihad ta bude jakarta jin wayarta na vibrate, ganin Aliyu ke kiranta ta daga, bayan sun gaisa yace "Xan shigo kano in the evening, ki turo min address din gidanku" Nihad ta wara ido tace "Are u coming to our house" Yace "Ki turo ina jira" daga haka ya katse wayar, Farin ciki ne ya lullubeta, bai ta6a cewa xai je gidansu ba sai yau, a baya babu yanda bata yi da shi a kan ya xo gidan nasu ba amma sai ya ki, har ta kagu ta gansu a gida ta tambayi Umma abubuwan da xata dafa masa, nazari ta shiga yi... or is he coming because of that useless driver?? Ohh God that will be very great.