← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 165

Sashe 102

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gidanmu ne, ya kawo ni in amshi sako wajen wani" Murmushi kawai Khalil dake tafiya xuwa inda ya ajiye mota yayi ba tare da ya juyo ya kallesu ba, Ma'aikacin ya fasa gaida Khalil da yayi niyyar gaidawa, sai kuma yace "Allah sarki ni na zata oga ne ae nagansa kalarki, to na gaisheki Hajiya" Bude jakarta tayi taga dari biyar ta zaro ta mika masa, ya amsa da ladabi yana mata godiya, tuni Khalil har ya kai gun mota ya bude driver seat ya shiga, Nihad ta karasa ta bude back seat ta shiga ta kulle, har suka isa gida bai ce mata ba bata ce masa ba, bayan yayi parking ya sauka ya tafi ya kulle gate, sannan ya nufi entrance din gidan ya bude kofar main parlor, Nihad dake ta tsaye tana jiran ya xo ya bude ta kyabe baki ta bi bayansa suka shiga parlon, wani ajiyar xuciya ta sauke direct ta nufi dakinta. Bacci sosai Nihad tayi bayan ta shiga dakinta, wajen karfe sha daya da rabi ta farka ta dalilin yunwan da take ji, a hankali ta mike ta shiga banɗaki tayi wanka ta wanke baki sannan ta fito, bata gansa a parlor ba har ta nufi dakinsa sai kuma ta fasa bude kofar ta dawo parlor ta zauna tana jiran ganin fitowarsa bude kofar parlor aka yi ta juya da sauri, taga ya shigo parlon rike da leda kallo daya yayi mata ya dauke kai ya karaso cikin parlon, a takaice tace "Makulli xaka bani xan fita in siyo kayan miya, sannan anjima xan je kasuwa siyo atamfofi don na kyautar da duk kayana a can garinku" Ya girgiza kai yace "Baya daga cikin sharadinmu, duk me kike bukata xa a siyo a ajiye maki" Ta kyabe baki tace "Toh a fita a siyo min kayan miya" Cike da isa tayi maganan, yace "Sai sanda nayi niyya" Yana gama fadin haka ya ajiye ledan hannunsa ya nufi kitchen don dauko plate, bin sa tayi da kallo yana shiga tayi saurin dauke ledan abincin nasa ta shige daki da sauri ta sa makulli, shinkafa ne da miyya da yaji uban nama sannan ga coslow a wani karamin takeaway din, ga ruwan roba me sanyi da drink, tayi er dariya ta gyara zamanta ta dau cokali ta fara cin abincin. Wajajen karfe uku Nihal ta kira Khalil, bayan sun gaisa yace "Kin dawo lafiya?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Maa sha daya, yaushe xa ki zo ganin er uwar taki?" Nihal tace "Shine dama nake son in ce mata xan zo yau, ka kai mata wayar pls" Yace "Xan gaya mata, Allah ya kawo ki lafiya" Tace "Ameen" daga haka ya katse wayar, tun da Nihad ta shige masa da abinci daki bata sake fitowa ba, don bayan ta ci ta koshi ma ramuwan baccin da bata yi a kauye ba ta ci gaba da yi. Wajen karfe biyar Nihal ta iso gidan, Khalil ne ya bude mata gate bayan ta kirasa a waya ta sanar masa tana bakin gate, ta sunkuyar da kai ta gaishesa ya amsa da murmushi yace "How are you Nihal?" Ta daga kai ta kallesa tace "Alhamdulillah" Yace "Maa sha Allah" Tana biye da shi suka shiga parlon gidan, ganin ta zauna a parlon ya daga kafada yace "Tana can daki, ki shiga" Nihal tace "Ko zaka dan mata magana ta fito" Yace "Aa, just go in" Mikewa tayi ta nufi kofar dakin da ya nuna mata, a hankali ta kwankwasa kofar, Nihad ta juya tana kallon kofar, to me xai ce mata yake mata Knocking, can dai ta mike ta nufi kofar ta bude a hankali, ido hudu suka yi da Nihal, wara ido tayi ta rungumeta tace "Yaushe kika dawo Nihal?" Nihal na Murmushi tace "3 days ago" Sai kuma Nihad ta hade rai ta koma cikin dakin, Nihal ta bi ta da kallo sai kuma ta bi ta cikin dakin ta kulle kofar, Nihad tace "Wato ke har xa a iya hada baki dake a cuceni ko Nihal? Ni nasan babu yanda xa ayi kice baki san komai a kan abin nan da Abba yayi min ba" Innocently Nihal tace "Wallahi ban san komai ba Nihad, kiji har na rantse" Nihad tace "Toh sai aka ce maki yarda xan yi da ke? Bayan nasan har tadi ku ke yi da drivern nan a waya amma kice baki sani ba?" A hankali Nihal tace "Allah ne shaida na, amma meye ribata idan nayi maki karya?" Nihad ta tabe baki tace "We have already sort out things da shi daxu da safe, and we are okay with our plan" Nihal tace "What plan?" Nihad tace "Ba sai kin ji ba, ina umma?" Nihal ta mika mata wayarta tace "Tace in na xo ki kirata" Murmushi Nihad tayi ta amshi wayar ta tafi can karshen gado ta hau kiran Umma, Umma na dagawa tace "Auta har kin je gidan ne?" Nihad tace "Umma ni ce" Umma tace "Aa Nihad, wato dai wannan matsiyacin duk wayar da aka baki sai ya karbe ga shi tatattce ko?" Nihad ta tabe baki tace "Wallahi Umma" Umma tace "Toh xa mu xuba da shi kuwa, xan kawo maki waya sannan in mika masa a gabana ya damka maki wayar da hannunsa" Nihad tace "Kin ma san abinda yayi min Umma?" Umma ta zaro ido tace "Me yayi maki?" Nan Nihad ta labarta ma Umma garinsu da ya kai ta ta kusa mutuwa, Umma tace "Ikon Allah, amma shine matsiyacin nan ya samu waje yake nuna ma mutane isa daga an aura maki shi? Asha ɗan kauyen kayau ne" Nihad tace "Wllh Umma ban gama rainasa ba sai da naje garinsu, yanxu 100% na rainasa wallah, Umma ko wuta fa babu a garin, sannan rafi suke xuwa debo ruwa, kai ni baxan ma iya baki labarin garin nan da baki ba, sai da nayi rashin lafiya kamar xan mutu sannan ya dawo da ni cikin gari" Umma da ke ta sauraronta tace "Ikon Allah, dama ance talaka da matsiyaci basu iya samun waje ba, ki ga yanda ya dawo birni ya kile yake daddaga ma mutane kai alhalin ko mage me gata baxata iya rayuwa a kauyen ba" Nihad ta sauke ajiyar xuciya tace "Na sha mamaki Umma, ɗan kauyen kayau ne wllh, kuma yanda kika gansa fari haka family dinsa suke da haske a kauyen" Umma tace "Toh Allah ya kyauta, in sha Allah gobe ko jibi ina nan shigowa daughter" Nihad tace "Toh Umma kar ki manta wayar, idan ya so kamar yanda kika ce sai ki basa ya bani a gabanki sannan ki ja masa kunne sosai kar yace xai amshe" Umma tace "Kar ki damu sai dai na zo" Daga haka suka yi sallama, Nihal na kallon Nihad tace "kinsan Mumy bata da lafiya kuwa Nihad?" Nihad ta kalleta tace "Haba? To ai ni ba a gaya min ba" Nihal tace "Ai kam bata da lafiya, in kirata ku gaisa?" Nihad ta ɗan yi shiru sai kuma tace "Ki bari anjima da daddare xan kirata" Nihal tace "Toh shkkn" Nihad tace "Idan xa ki ci abinci ga indomie can kitchen ki dafa fa" Nihal ta mike ta fita daga dakin, tana shiga kitchen taga kayan miya kawai tayi deciding ta dafa jollof rice, tana cikin grating kayan miyan taji muryar khalil yace "Sannu da aiki" Ta kalli kofar da sauri sai kuma tayi murmushi tace "Nagode" Yace "Yaushe xa ku kare hutun?" Tace "Nan da sati biyu" Yace "Ohk nan xaki gama hutun ko?" Tace "Aa ni da gobe xan tafi, i don't want to over stay my welcome" Murmushi yayi yace "Aa kiyi hutunki kawai a nan" Ita dai bata ce komai ba tana ci gaba da aikinta, juyawa yayi daga karshe ya bar kitchen din. Bayan Magriba yana xaune a parlor Nihal ta fito daga daki xata je kitchen ta xuba ma ita da Nihad abinci, ganin khalil zaune parlon ta koma daki wajen Nihad tace "Ki fito ki zuba masa abinci, ban fa xuba masa ba tun daxu" Da mamaki Nihad ke kallonta, sai kuma tace "A saboda me xan xo in xuba masa abinci? Dama da shi kika dafa abincin ne?" Nihal dai bata ce mata komai ba ta juya ta fita, Nihad ta rike ha6a tace "Ji wani iyayi wai in xuba masa abinci kamar wani mijina, ashe xai tsufa bai ci abincin ba" Tsaki ta ja ta jawo wayar Nihal for the 10th time ta sake kiran layin Aliyu amma a kashe, kwantar da kanta tayi saman pillow kamar xata yi kuka don har ta gaji da trying layin nasa, tun xuwan Nihal take abu daya, Nihal na komawa kitchen ta fara xuba masa abincin a plate sannan ta dauka ta fito parlor ta nufesa ta durkusa tace "Ga abinci" Yana kallonta yace "Thank you Nihal" Ta mike ta koma kitchen din ta xuba ma ita da Nihad a tare, kadan Nihad ta ci abinci duk hankalinta a tashe yake bata samu Aliyu ba, Nihal ta ci abinda xata ci ta bar mata ta koma saman gado ta dau wayarta tana dannawa, Daga karshe wajen karfe goma da taga Nihad ba ci xata yi ba ta dau plate din ta fita, Bayan ta kai kitchen ta fito khalil na kallonta yace "Wani level kike a makaranta?" Ta tsaya tace "Level daya muke da Nihad" Yace "But in tambayeki" Ta ɗan tsaya sai kuma ta dawo parlon ta xauna tana kallonsa yace "Ke kika ce ma Abba Ahmadu Bello University kike so?" Nihal tayi murmushi tace "Aa, kawai cewa yayi can xan je ni" Yace "Ita kuma er uwarki fa?" Ta sunkuyar da kanta tace "He gave her option" Khalil dake ta kallonta yace "Ohk ke daga baya baki ce masa makaranta daya kike son xuwa da er uwar taki ba?" Nihal tace "Ya Usman da Mumy sun masa magana a lkcn, Mumy tace masa tunda har Nihad ta zaba Maryam Abatcha nima ya biya mun Maryam Abatcha din mu tafi tare ko kuma duk mu tafi ABU, amma sai yace Nihad kawai xata je ni in tafi ABU, he can't afford the fee of Maryam Abatcha for the two of us" Shiru Khalil yayi yana kallonta, can
Chapter 102 · 0% Book details