Sashe 66
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
And u show ur evidence via👇🏻 07087865788 Thank you as u patronize and i am assuring u that Nihad will be counted among my best In sha Allah💖[7/6, 12:20 PM] Ummy Sfna: At first tsayawa yayi kamar bazai bi ta ba amma ganin ta kulle kofar kitchen din yayi saurin bin bayanta, Tsaye ya ganta ta dau table knife tana kuka sosai facing the knife towards her stomach, ya kalleta daga sama har kasa, sae kuma ya shiga cikin kitchen din ya dau asalin wuka ya karasa har gabanta ya mika mata yace "In da gaske kike" runtse ido tayi tana kuka iya karfinta, ya kamo hannunta ya saka wukar a ciki sannan ya koma bakin kofa ya jingina da wall din wajen ya rungume hannunsa yana kallonta da wani scorned expression, ta bude ido a hankali ta jefar da wukar ta sulale kasa tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wayyo na shiga uku na lalace" sai kuma ta daura hannu a ka ta kurma uban ihu tana kallonsa, juyawa yayi ya bata waje, Ko sanda aka yi leaking Video dinta bata tunanin tashin hankalinta ya kai wanda take ciki yanxu, she is still yet to believe who she is seeing, wani ihun tashin hankali ta kuma kurmawa lkci daya kuma tayi shiru, to ko dai aiko sa aka yi gidan, tunanin hakan ya sa ta hau share idonta gabanta na bugawa da sauri, lkci daya tayi assuring kanta kawai aikosa aka yi gidan shine ya shigo masu har ciki, da kyar ta mike tsaye kamar me tsoron taka kasa ta karasa kofar kitchen din ta leko parlon a hankali with throbbing heart, zaune ta gansa saman kujera, suna hada ido ta wani hade rai har sannan gabanta na faduwa tayi karfin halin cewa "Malam idan aikoka aka yi sai ka shigo ma mutane har cikin nan? Wannan wani irin samun waje ne? Duk tsakar gida bai isheka ba sai ka shigo har nan" Kallonta kawai yake da wani stern look a fuskarsa, ta wani kara shan kunu tace "ko shi mai gidan ne ya baka damar shigo mana har cikin nan?" Ba abinda yace mata still, kuma babu alamar xai ce mata komai sai ma dauke idonsa da yayi, ta dake ta fito daga kitchen din gaba daya, tace "Wai baka jin ina maka magana ne ko nan din ma rashin kunyan xaka min?" Yace "Ok" Yana fadin haka ya mike ya juya yayi hanyar kofar fita daga parlon, wani irin kwanciya hankalinta yayi, taji ta samu relieve da nutsuwa, sulalewa kan kujera tayi ta jinginar da kanta da kujerar tare da sauke wani dogon ajiyar xuciya, haba ita dama ta san aikosa gidan aka yi shine xai shigo ma mutane har parlor saboda samun waje, shi kam yana fita ya kulle kofar parlon, Nihad ta share hawayen idonta a hankali tana tunanin to ina wanda aka aura mata din, har yanxu fa bata gansa ba, mikewa tayi ta nufi hanyar dakuna ta bude wani daki a hankali ta leka ciki taga babu komai dakin banda katifa, ta kulle ta sake bude wani taga shi ma katifar ce kawai, toh where is the so called husband, a hankali ta juya ta koma dakin da ta kwana ta xauna gefen gado, she is just imagining ace abinda tayi tunani daxu a kitchen gaskiya ne ai da kawai da gaske kashe kan nata xata yi kowa ma ya huta, but why will she even think that way at the first place, it is something that is neva and neva going to happen, agogon dake dakin ta kalla taga karfe goma sha daya saura, har lokacin bata ji tana jin yunwa ba, ita ta ma mance rabonta da cin abinci a cikinta, tana ta xaune dakin with different thought and imagination a ranta, can kuma ta mike duk jiki ba kwari tana tafiya a hankali ta koma parlor, windown dake kusa da kofar parlon ta tafi tana leka compound din, karamin compound ne da xai iya cin mota uku, ga mamakinta sai ta gansa xaune kan wani dakali a tsakar gidan ya rike kansa, wani faduwar gaba taji ya dirar mata, but seriously what is this man doing in this house for God sake, me yake har yanxu bai tafi ba, to ko dai mai gidan ne yace ya jirasa, this time around ta ma rasa wani takamaiman tunanin xata yi, duk sai ta birkice taji jikinta na rawa.... amma taki barin ƙwaƙwalwarta ya fassara mata abinda xuciyarta ke raya mata a lokacin, noooo it can't and will never be, tasan aikosa gidan kawai aka yi wallahi...... _Har a lokacin da ya gama hada takalman idon Abba na kansa, ganin xai fita parlon Abba yace "Ibrahim" Juyowa yayi yana kallon Abba, Abba ya nuna masa waje alamar ya xauna, komawa yayi ya xauna a hankali yana kallon Abban, Abba ya nisa yace "Kana da mata ne Ibrahim?" Khalil ya ɗan yi jim, amma ganin yanda Abba ya kafe sa da ido yayi saurin girgiza kai yace "Aa" Abba yayi kasa da murya yace "Ohk! Kana da wani dalilin da yasa baka yi auren ba har ynxu ko kawai ra'ayinka ne?" Khalil ya sunkuyar da kai yace "Dama da kaka aka ce xan yi auren idan Allah ya yarda" Abba yace "Kana da yarinyar da xaka aura ne Ibrahim?" Khalil ya dago ya kalli Abba dake ta kallonsa, sai kuma ya sake sunkuyar da kai a hankali yace "Aa ban samu ba dai tukun" Abba yayi shiru yana kallonsa as if thinking of where to start from, kallonsa kawai Abba yake daga sama har kasa duk da a xaune yake, kamar jikinsa ya basa Abban na kallonsa, sai duk ya tsargu, upside down ya juya palm dinsa a hankali not wanting to disclose the ring he is putting on, muryar Abba yaji yace "Ina son xan maka aure, xan kuma yi maka komai na auren sannan in baka gida ku xauna don na ya6a da nutsuwa da hankalin ka, bana jin ina da fargaba a kanka Ibrahim.... amma baxan yi hakan ba tare da yardar ka ba, da kuma yardar iyayenka, ina rokan wannan alfarman a wajenka Ibrahim" Khalil ya ji komai ya tsaya masa na kusan 10 seconds, lkci daya ya ji he is feeling heat all over, ya dai yi karfin halin dago kai ya kalli Abba, ganin yanda Abba ke kallonsa wanda in dai ka san Abba to xaka fahimci yana cikin damuwa wanda baya iya boyuwa ko min pretence din mutum, Khalil ya kirkiri fara'a a fuskarsa yace "Amma nagode sosai Alhaji, Allah ya kara girma, Allah ya saka da alkhairi, Nagode Alhaji" Abba yaji dadin reaction dinsa sosai cause he neva expect that, ya xata xai ce Aa ko kuma ya kawo wani excuse din, Abba ya sauke boyayyen ajiyar xuciya yace "Ameen Ibrahim, sai mu je can gun iyayenka yau mu yi magana da su ko? Su ma kuma ina fatan Allah xai sa su amince" Khalil ya hadiye abu da kyar yace "To ba damuwa Alhaji" Abba yace "Ka shirya nan da awa biyu mu tafi" Yace "Toh Alhaji" Abba yace "Nagode, amma sai dai baka tambayeni da warce xan hada ka ba" Khalil kallon Abba kawai yake, Abba yace "Yar cikina ce ba wata ba, saboda na yaba da komai naka ya sa nake son hada zuri'a da kai, ni kadai na yanke shawarar nan, kuma idan Allah ya yarda ban yi abun da xai cutar da kai a gaba ba Ibrahim, xaka yi farin ciki da hadin nan wataran, kawai tun yanxu ina neman alfarman ka koyi hakuri da ita don yarinya ce, kuma ita ma nasan watarana xata yi alfahari da xabin da nayi mata, fatana kawai Allah ya dora ni kan iyayenka" Khalil kam yayi nisa tunanin da yake don bai ma assimilating maganganun Abba, thousands of thought ne suka yi crossing mind dinsa a moment din nan, why him of all people, this means disappointing every of his relative, ko Abba bai fada masa wacece cikin yaran nasa ba ya san wacece, no!!! they are not and will neva be compatible, how will that even be? Muryar Abba ya tsinta a tsakiyar kansa ya a ce masa "Xaka iya tafiya, Allah yayi maka albarka" Ko Ameen din khalil bai iya ya amsa ba ya mike ya kwashi takalman Abba ya fita daga parlon, lkci daya yanayinsa ya sauya, wasu xufa suka hau keto masa, Yana fita compound ya nufi mai gadi ya dire masa takalman, Aminu ya mike da sauri yace "Lafiya na ganka a birkice haka? Me ya faru?" Khalil bai basa amsa ba ya nufi chalet, har idanuwansa sun kada .... Muryar Nihad ne ya dawo da Khalil duniyar tunanin da ya fada a tsakar gidan, ya daga kai fuskarsa daure yana kallonta, a fusace tace "Wai baka ji abinda nake ce maka bane? Ka gaya min uban me ya kawo ka gidan nan?" Mikewa yayi yace "Ki kira babanki ki tambayesa, don shi ya kamata ya baki wannan amsan" Kasake tayi tana kallonsa gabanta na faduwa, har ya juya ya fara tafiya sai kuma ya juyo, severely yace "Sannan ina me baki shawaran kada ki sake daga min murya, ko kuma ki sake min wasu tambayoyi a gidan nan" Daga haka ya bar ta wajen tsaye ya koma cikin gidan walking fast, shikenan abinda take ta hana ƙwaƙwalwarta fassara mata ya tabbata, shikenan tsoronta da fargabanta ya tabbata, ta fashe da wani matsanancin kuka me ban tausayi ta sulale kasa ta daura hannu a ka ta kurma wani uban ihu tace "Na shiga uku na lalace, na banu na lalace, Me nayi ma Abbana xai min haka, me yasa Abbana xai min haka, me nayi ma yan gidanmu suka min haka, innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Kuka take sosai kamar ranta xai fita, ta fi minti ashirin xaune kasan interlock ta kasa tashi, she is more than shock, why her?? Ganin abun ma take kamar a mafarki, Nihad ta ci kuka ta gode Allah a zaune wajen, daga karshe ta kalli gate din gidan sai kuma ta mike da sauri ta nufi gate din amma tana kokarin budewa taji key aka sa, sulalewa wajen tayi tana ci gaba