Sashe 113
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Husnah tace "Tohh idan mutum na cikin azaba ai baya ma tunanin komai, kawai burinsa a fitar da shi daga axaban da yake ciki, to situation din da na tsinci kaina kenan, amma ni kaina ina ni ina wani driver can" Nihad bata sake cewa komai ba, Husnah tace "Shikenan, tunda har kika koreni bari in yi tafiyata ko hotel ne in kwana don a hostel na riga nace masu baxan dawo yau ba" Nihad tace "Ni fa bance kar ki kwana ba, kawai haushin yaron can ne yasa nace mu kai ki hostel" Tana kai wa nan ta mike ta cire Hijab din jikinta tace "Bari in mana boiling din spaghetti din yanzu, daga can xan gyara kitchen din" Tana fadin haka ta fita parlor ta wuce kitchen tsaye taga Khalil yana kokarin mopping din kitchen din, ta wani hade rai, yana ganinta ya ajiye mop din ya fice daga kitchen din ya shiga dakinsa, bayan few minutes da fitar Nihad Husnah ta leko daga dakin tana lekan parlor amma bata ga Khalil a ciki ba, komawa dakin tayi ta cire yagaggen wandon jikinta da riga ya rage daga ita sai bra da skin tide ta dau after dress dinta ta saka tayi buttoning dinsa sannan ta fito, ta fi second goma tana kallon kofar da take tunanin dakinsa ne sai kuma ta murda, dago kai yayi suna hada ido ta sunkuyar da kai ta shiga dakin ta tura kofar tana tsaye bakin kofar tace "Dama nace bari in maka godiyan dawainiyar da kayi da ni, Allah ya saka da Alkhairi.... kuma don Allah abinda ya faru kwanaki ina sake neman yafiyarka don wancan ranan baka ce min komai ba da na baka hakuri" Kallonta kawai Khalil yake, can ya ajiye lemon kwalin dake hannunsa yace "Ohk, kawarki ki ce ta aikoki ki bani hakuri kenan?" Husnah ta zaro ido tace "Waaa?? Ai inda muka bambanta da ita kenan, da ita ce baxa ta ta6a baka hakuri ba, kasanta da taurin kai da kafiya, yanzun ma bata san na shigo nan ba da baxata bari ba, amma ka sani wllh tunda muka maka wannan rashin kirkin bana samun nutsuwa saboda ba halina bane" Yace "Ohk ai na zata duk ku ke sa ta a hanyar walakanta mu talakawa" Husnah ta dafe kirji ta karasa cikin dakin tace "Waa?? Halin kishiyar mamarta ne ta dauko, kasan duk abinda ta sata tayi shi take yi, amma basu san da talaka da mai kudi duk Allah ne yayi su ba, ka gan ni nan babana yalo yake siyarwa a kawo kaduna, ni ba er kowa bace shi yasa nasan mutuncin ɗan adam" Khalil yace "Ohk, ai ina ce er kano ce" Husnah tayi wani dariya tana jujjuya ido tace "Wallah er kaduna ce ni gaba da baya, Zully da Naf ne yan kano" Yace "Toh naga makarantar taki ta masu kudi ce" Husnah tace "Ehh wallahi wani saurayina ne ya biyamin tun daga level one har karshe, wata kawar mu zully ma saurayinta ke biya mata, Naf ce dai iyayenta ke biya mata don su ma masu kudi ne" Khalil ya gyada kai yace "Allah sarki" Husnah ta zauna gefen gadon tace "Amma ina jiye maka zama gida daya da Nihad, yanda bata kaunarka ta tsaneka kullum a makaranta cikin tsine maka take wai kana matsayin driver kana nuna mata isa, bayan anyi auren nan har ikirari tayi wai zata kasheka, nan kuwa kai jahadi kayi, halan baka hawa social media? Ina nufin baka da babban waya?" Ya girgiza kai yace "Bani da" Husnah ta gyada kai tace "Allah sarki, kawai dai ka saka ido sosai kada kiyayya yaje ya kaita ga aikata abinda ba shi kenan ba, in sha Allah in xan sake dawowa nayi maka alkawarin babban waya" Khalil yace "Toh Nagode, amma kawar taki bata da saurayi ne?" Husnah ta rike ha6a tace "Ita kuwa take da saurayi wanda ita ta makale masa ba shi ba, kana jin janaral jikamshi?" Khalil yace "Eh nasan shi, ko ba wani babban soja ba?" Husnah ta dafa kafarsa cike da kissa tace "Yauwaaa, Toh shi fa.... ɗan sa kwaya daya take so kamar ta kashe kanta, tun yana basar da ita har dai ban san sanda suka dinke ba, mu dai mun fi zargin bashi kanta tayi, don kawai lkci daya muka ga ya fara kiranta ba kakkautawa a maimakon ita da ke yawan kiransa" Khalil ya sauke idonsa kasa daga kallon da yake ma Husnah, Husnah tace "Kuma fa duk wannan abun sau daya ya zo wajenta a nan kano suka hadu a wani waje, kamar dai kar su hadu shkkn ya makale mata, kasan mu mata idan muna son abu babu abinda baxa mu yi kan abun ba, to tun dai daga sannan ya fara kulata sosai, kuma kar kace fa yana zuwa gidansu, aa sam... duk xuwan da yake yi wajenta nan kano sai dai su hadu a wani waje su yini sannan yayi tafiyarsa, toh kwanaki can ban san ya aka yi ba yaje gidansu wai xai tura iyayensa, mu dai ko gaya mana bata yi ba gaskiya sai daga baya, ai ko muna ta murna xa mu hade da 'ya yan manya mu ma a dama damu tunda abokanansa duk 'ya yan manyan kasar nan ne kawai wai sai ga videon tsaraicinta ya bazu a duniya, ni takaicina daya da ba a bari sai da muka hadu da abokansa ba, har yau mun rasa ta ina video din nan ya fita, muna dai tunanin garin yawace yawacenta ne aka mata video din nan" Khalil bai kuma cewa komai ba, lkci daya kuma duk mood dinsa ya canza, Husnah ta shafa kafarsa a hankali tana kallon kwayar idonsa tace "Sai kaji babu dadi ace videon tsaraicin warce aka aura maka na ta yawo a duniya ko? A ranka kana tunanin an cuceka ko?" Kallonta Khalil yayi, tana Murmushi ta janye hannunta a hankali tace "Toh Nagode bari in je inyi wanka" Daga haka ta mike tana juya manyan mazaunanta ta nufi kofa, tunda ya kalleta sau daya ya dauke kai har ta fita dakin, karo ta kusa ci da Nihad, Nihad ta tsaya tana kallonta daga sama har kasaasa, Husnah tace "Ke yace min maganin na wajenki kuma ni ban gansa a dakinki ba" can kasa kasa Nihad tace "Ba ya wajena" Daga haka ta shige dakinta, Husnah ta tafi parlor ta dau magungunan nata ta dawo dakin Nihad. Nihad dai na ta zaune gefen gado, Husnah tace "Wai taliyar bata yi bane Nihad?" Sai a sannan Nihad ta kalleta tace "Mu je mu duba" Husnah tace "Ohk" Daga haka ta mike ta fita Nihad ta tashi ta bi bayanta, tana tsaye parlor har Husnah ta shiga kitchen, a hankali ta bude kofar dakinsa ta leka taga baya ciki, ta kalli kofar bandaki sai kuma ta kulle kofar dakin, entrance din fita ta kalla bata ga takalminsa ba, ta karasa jikin window ta tsaya ta bude labulen a hankali tana lekan waje, yana tsaye balcony ya rungume hannunsa, can ta ga ya nufi dakalin da yake son zama ya zauna kana ganinsa kasan he is moody, Husnah ta fito daga kitchen tace "Me kike nema a waje" Nihad tace "Ba komai, kin zubo taliyar?" Husnah tace "Ehh na zuba, ashe har kin sauke" Nihad tace "Toh dauko mu je daki" Husnah ta koma ta dauko suka wuce dakin, bayan sun gama cin abincin Nihad ta fitar da kwanukan ta sake leka waje taga har sannan khalil na zaune inda yake staring into space, kafin Nihad ta dawo Husnah ta jawo jakarta ta fito da kayan mayenta ta sha sannan ta mayar da jakar ta ajiye ta kwanta, Nihad na dawowa dakin ta zauna gefen gado, tana son shiga bandaki tayi wanka amma ta kasa tashi, Wajen karfe sha daya da rabi Husnah ta mike Nihad na kallonta tace "Ina za ki?" Husnah tace "Ruwa zan dauko kitchen" Nihad ta dauko wani bottle water dake daya side din gadon ta mika mata, Husnah ta amsa ta koma ta zauna tana sauke numfashi a hankali, ita fa dama kwana biyu duk samarin nata basa Kano gaba daya a takure take dama, daga karshe dai Husnah ta kwanta ta kulle ido duk da ba bacci tayi ba, Wajen karfe sha biyu da rabi Nihad ta mike daga kwancen da take ta nufi kofa ta sa makulli sannan ta ciro, Da mamaki Husnah ta mike zaune tana kallonta tace "Me yasa zaki kulle mu har da cire makulli Nihad?" Nihad tace "Saboda duk dare haka nake yi dama" Husnah bata kuma cewa komai ba ta kyabe baki ta koma ta kwanta, Nihad ta saka makullin cikin pillow ta kwanta kai. Washegari da sassafe bayan sun yi sallan asuba sun koma bacci kiran Umma ya tashe su, Bayan Husnah ta daga jin muryar Umma tace "Auu Umma ce, ina kwana?" Umma tace "Lafiya lau Husnah baki yi saving number na har yanzu ba ko?" Husnah tace "Yanzu xan yi Umma, ya gida?" Umma tace "Alhamdulillah, ina Nihad din?" Husnah ta mika ma Nihad waya ta koma ta kwanta, Bayan Nihad ta gaidata, Umma tace "Ya, kin gano sunan iyayen nasa kuwa Nihad?" Nihad tace "Aa Umma, dama sai yau" Umma tace "Kin ji irin shiriritar taki ko? Ke da tun jiya nace kisan yanda kika yi ya gaya maki amma sbda shashanci baki yi ba? Ko dai kin fi son kiyi ta zama da dreban nan ne Nihad?" Da sauri Nihad tace "A'a Umma, in sha Allahu yau xan gaya maki" Umma tace "Toh kar ki bari Husnah ta bar gidan nan sai kin gano kin sanar min ta wayarta tukunna" Nihad tace "Toh Umma" Umma tace "A handsfree wayar yake ne naji maganata na dawo min?" Nihad tace "Aa" Umma tayi kasa da murya tace "To dai ki xama me rike sirrinki a ciki, ciki da kike gani ba don tuwo kadai aka yi sa ba, ko da mun gana waya kawarki ta tambayeki me muka ce kice mata ba komai kawai daddawa da kuka nace xan bada a kawo maki, don ba komai ake sanar ma k'awa ba, wa ya sani ko da hadin bakinsu aka saki video dinki a duniya"