← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 165

Sashe 67

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da kuka tana girgiza kanta, nan ma tafi min sha biyar, bata ta66atar da gaske an tsaneta a gidansu ba sai yanxu, sosai kanta ya fara mata ciwo, jin strength dinta ya fara karewa saboda kukan da take tayi karfin halin tashi tana layi ta koma cikin gidan, kitchen ta shiga tana kallon wukar da ya bata ta wurgar daxu, karasawa tayi ta dau wukar hawaye me xafi na sauka idonta, jingina tayi da cabinet tana kuka a hankali, to ai in tayi hakan wuta kawai xata, jefar da wukar tayi daga karshe ta fito parlon tana bin ko ina da kallo hawaye na bin idonta, karamar wayarsa ta gani saman kujera ta karasa da sauri saman kujeran ta dau wayar ta shige dakin da ta kwana, xaunawa tayi gefen gado hawaye wasu na bin wani a idonta tayi dialing number Nihal, tana sa wa sunan Nihal ya fito baro baro, ta kai kunne, yana fara ring ba a wani dau lkci ba Nihal ta daga, kasa cewa komai Nihad tayi tana kuka a hankali ta runtse idonta, jin shiru ba ace komai ba cikin sanyin murya Nihal tace "Hello" Nihad ta fashe da matsanancin kuka tace "Na shiga uku Nihal, kinga abinda su Abba suka min ko, dama ashe har Abba baya so na, dama haka aka tsaneni a gidan nan ban sani ba? wayyo Nihal wllh da Allah baxai jefani wuta ba yau da na kashe kaina kowa ma ya huta, zuciyata kamar xata fashe nake ji yanxu, i can't take this any longer, me yasa su Abba xa su min haka, sun san ma meye aure kuwa?" Kuka take kamar ranta xai fita, Nihal dai tayi shiru bata ce komai ba, Nihad na shessheka tace "Pls ki turo min number Husnah yanxu ta nan, nasan kina da shi send it now plss i need it...." Tana gama fadin haka ta katse wayar ta fada kan gado tana rera sabon kuka, ko minti daya ba ayi ba Nihad taji shigowar message a wayar, ta mike xaune da sauri taga number Husnah ne Nihal ta turo mata, da sauri ta hau kiran number, yana fara ring Husnah ta daga tace "Hello" Nihad ta rushe mata da kuka tace "Husnah tawa ta kare, Abba na ya tsaneni baya so na, Husnah kila ma ba su suka haifeni ba wallahi" Da sauri Husnah ta rage volume din Mp da suka cika a daki tace "Calm down Nihad, kar ki je ki sa ma kanki wani ciwon mu shiga uku, wllh tsoron xuwa gidan nan naku nake saboda yayanki, babu ta inda kuma xan san halin da kike ciki tunda bani da number kowa a gidan, Nihal da nake da number ta tana school da na kirata tace min haka" Nihad tayi karfin halin cewa "Husnah kin san wa Abbana ya aura min?" Husnah ta gyara xama tana gwale ido tace "Aa waye?" Nihad ta kwanta gefen gado hawaye me xafi na sauka idonta tace "Husnah of all people wai drivern gidanmu Abba ya aura min" Husnah dake xaune sai da ta mike tsaye tace "Whattt???" Bude kofar dakin aka yi Nihad ta mike xaune da sauri lkci daya ta hade rai, yana mata wani kallo ya karasa cikin dakin fuska daure yace "Kar ki sake ta6a min waya a gidan nan" Wani matsiyacin kallo tayi masa ta wurgar da wayar tana ta6e baki tace "Wannan gwangwanin kake kira waya?" Kallonta kawai khalil yake babu ko kiftawa trying his possible best to calm himself, Nihad ta ja tsaki ta tashi ta koma can karshen gado ta xauna fuska daure tace "Wai waya, kai baka ma ji kunyan kiran wannan waya ba" Gyada kai yayi ya juya ya durkusa ya dau wayar da batur dinsa da yayi gefe daya ya mayar sannan ya mike ya nufi kofa ya fice daga dakin, wani sabon kukan ta saki tace "Wayyo Allah na." Wajen karfe sha biyu da rabi Nihad da har ta gaji da kukan da take ta ji ana kwankwasa gate din gidan, kamar tana expecting hakan ta mike da sauri tana share idonta ta fice daga dakin, dai dai fitowarsa shi ma daga dakin da yake, ta wani hade rai, ko kallonta bai yi ba ya nufi kofa ya fita, wani mugun tsanarsa da tafi ta ko yaushe take ji a ranta, even with joke baxata ta6a kiran wannan mutumin wai mijinta ba, mijinta ta ina? Shi har ya isa ya xama mijinta? This is even weird to imagine, bakin kofar parlon ta tafi ta tsaya fuska daure, yana bude gate din Umma ta shigo, har kasa ya durkusa yace "Barka da xuwa Hajiya, ina yini" Wani kallo Umma tayi masa sae kuma ta kyabe baki ta wuce ta bar sa durkushe a wajen, Nihad na ganin Umma ta taho da gudu ta Rungumeta ta sakar mata kuka da karfi tace "Umma na shiga uku, me yasa Abba xae min haka, me yasa Abba xae lalata min rayuwa, Umma ashe duk ba sona ake a gidanmu ba ban sani ba" Umma ta rungumeta cike da damuwa tace "Yi shiru mu shiga ciki Nihad, yi shiru" A haka Umma ta ja xuwa parlor, khalil da ya bi su da ido ya tafi kan dakalin da ya xauna daxu ya xauna, Umma na rungume da Nihad bayan ta zauna kan kujera tace "Wai ba nace kiyi shiru ba ko in tashe in tafi ne?" Nihad ta girgiza kai tana shessheka a hankali tana goge idonta, Umma tace "Ke yanxu kin yarda an aurar da ke kenan?" Nihad ta daga kai tana kallon Umma da kumburarran idonta, ba idonta ba har fuskarta ya koma ja, Umma tace "Ohh kin yarda kenan an daura maki aure da Driver?" Nihad ta girgiza kai disgustingly tace "Allah ya kiyaye wllh" Umma tace "Toh Alhamdulillah, yanda ko wace budurwa take rayuwarta haka xaki ci gaba babu batun auren kowa a kanki, kar ki kuskura ki amince wai kina da wani wai shi miji, a nan din ma bai wuce ɗan aiken ki ba kuma drivern ki, ki sa a ranki kema budurwa ce da xata iya shiga duk inda take so ta fito, ki ci gaba da rayuwarki yanda kika saba, sannan kar ki kuskura ki raga masa balle ya ga fuskar kawo maki raini, ba kowa bane shi facce drivern gidanku kuma har a yanxu dreban ne, kuma ɗan aike" Nihad tace "Toh Umma yanxu a gida daya xa mu xauna da shi kenan? Wallahi i just can't imagine that, ta yaya xa ace muna gida daya da shi?" Umma tace "Ka ji ki, Toh ina ruwanki da shi? Meye hadin ki da shi? Rayuwarki kawai xaki dinga yi kamar kina gidan ubanki, kar ki yarda ko kallon kirki ya hada ku da shi, har yau shi din ma'aikacin gidanku ne don haka a karkashin ki yake" A hankali Nihad tace "Toh, amma Umma shikenan baxan ci gaba da karatuna ba kenan" Umma tace "A saboda me? Ai kwantar da hankalin ki, yanxu daga nan gidan Alhaji Abubakar xan nufa tunda dai sun aurar da ke sai su bari kuma ki ci gaba da karatun ki" Nihad ta sauke ajiyar xuciya tace "Nagode Umma" Umma tace "Kar ki yarda ki kara xubar da hawayenki a banza a hofi, ke da ma kika samu freedom din kanki yanxu, da kin tashi fita kawai fitar ki xa ki yi kanki tsaye babu neman izinin ko wani shege, sanda kika ga dama kuma xa ki dawo babu me tuhumarki" Nihad da ta ji hankalinta ya kwanta sosai tace "Haka ne Ummana" Umma tace "Toh ko ke fa, sannan duk kawayenki xa su iya xuwa nan su dinga kwana kuna yini tare, kuyi duk wani sabgarku a nan babu me cewa don me" Nihad tace "Gaskiya ne Umma, amma ni damuwata kawai ganinsa da xan dinga yi a gidan, baxai yiwu ya koma can gidan ba kawai gaba daya ni kadai in zauna a nan, wllh i hate the sight of him, na tsani ganinsa, na tsanesa" Umma tace "Aa ke kuma, ai xai ci gaba da aikinsa na tuki, kinga duk safiya xai dinga xuwa can gidan kilan kuma sai ya dawo da Abbanku daga office sannan ace xai dawo nan gidan" Nihad ta yatsina fuska, Umma tace "Ke ma abinda idan kika fita kilan sai daren xa ki dinga dawowa gida" Nihad tace "Dama mana, yanxu kawai xance su Husnah da Naf su kwaso kayansu su dawo nan mu zauna" Umma tace "Shikenan kuwa" Nihad ta sauke ajiyar xuciyar relieve, Umma tace "Kin ci abinci kuwa?" Girgiza kai Nihad tayi, Umma tace "Me yasa? To tashi ki tafi kitchen ko indomie ne ki dafa" Nihad tace "Toh" Mikewa tayi cike da energy ta wuce kitchen, sosai ta samu nutsuwa bayan abubuwan da Umma ta gaya mata, ta dafa indomie sannan ta fito, Umma tace "Bari in xo in tafi don in samu Alhaji Abubakar a gida" Nihad tace "Umma bani da waya wllh" Umma tace "Akwai nokia din yayanku bari ko Amina xan ba ta kawo maki anjima" Nihad tayi Murmushi tace "To Umma Nagode" sai da ta gama cin indomie sannan Umma tace ta taso ta rakata, Nihad ta mike suka fito compound da Umma, har sannan khalil na xaune inda yake, Ya mike yana kallon Umma yace "Sai anjima Hajiya" Umma ta wani kallesa, sai kuma ta kyabe baki ta ci gaba da tafiyarta Nihad ta hade rai tana biye da ita a gefenta, Komawa yayi ya zauna ya bi su da kallo, suna isa gate Umma tace "Toh sai kin ji ni, idan Amina ta kawo maki wayar sai ki kirani don xan sa a siyo maki sim ayi register sai ta taho maki da shi" Nihad tace "Toh Umma" Umma tace "Maza tafi kiyi sallah ga azahar yayi, sai ki kwanta ki huta" daga haka tayi mata sallama ta wuce, Nihad ta kulle gate din, fuska daure ta nufi cikin gidan. Har bayan magrib Nihad na ta jiran Amina ta kawo mata waya amma shiru, gashi babu yanda xata yi ta kira Umma duk da tana da numberta a kai, wannan ne yasa ta kara shiga wani damuwa, karfe takwas da rabi ta mike a hankali ta
Chapter 67 · 0% Book details