Sashe 78
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
na shiga uku" Ya daga kai ya ɗan kalleta, juyawa yayi yana kallon ruwansa dake saman gas, ta dago kai cikin kuka tace "Koma me kayi da wayar ban yafe ba...." Ko rufe baki bata yi ba taga ya cire hannunsa da sauri daga handle din tukunyar alamar ya kona sa, ya koma baya yana kallon tukunyar, wani shegen dariya ta saki har da kyakyatawa ta durkusa a wajen, yanda take dariyar kai kace bata da sauran damuwa a duniya, ya ɗan kalleta sai kuma ya shafa kansa ya juya yana murmushi ya kalli inda ya tukunyar ta kona sa, ruwan da bai juye ba kenan ya bi gefenta ya fice daga kitchen din ya bar ta a ciki, bayan ta ci dariyarta ya isheta sai kuma ta mike ta hade rai, a hankali ta dauke tukunyar shinkafar da Aunty Jamila ta girka, ta dau na miyan ma duk ta kai dakinta da plate da spoon sannan ta koma ta jawo kofar kitchen din ta saka makulli ta zare, sai ta ga ta yanda xai sha shayin yau, infact forever and ever, don ta kulle kitchen din kenan har abada, Dakinta ta wuce ta bude akwatunta ta binciko duk kayan ta ajiye makullin karkashin akwatin sannan ta mayar da kayan ta kulle akwatin ta koma gefen gado ta zauna. Tun kafin tayi sallan magrib tayi wanka, don haka ta zuba abinci ta ci, ta tashi ta shiga bandaki ta wanke bakinta ta dauro alwala, tana yin sallan isha'i ta sa ma dakinta makulli ta ta dawo ta kwanta. Washegari bayan Nihad tayi wanka ta wanke bandakinta, she can be lazy in all aspects but not when it comes to her bathroom and Bedroom, bayan ta fito sai da ta fara gyara dakinta sannan ta saka kaya, sbda mugunta haka ta zuba sauran shinkafar da sanyi ta ci, ta koma bandaki ta kuskure bakinta da mouth wash ta fito, Hijab har kasa ta daura saman kayanta, sannan ta dau jakar da take xuwa makaranta da shi ta bude kofa a hankali ta fito parlor, yana kwance saman doguwar kujera, ta galla masa wani harara ta karasa cikin parlon, ta tsaya bayan 2 seater, ta dake tace "Makaranta xaka ajiyeni malam" Khalil ya daga kai ya kalleta, sai kuma ya mike zaune yace "Ohk, wace makarantar?" Babu yabo babu fallasa tana juya ido tace "Wanda ka saba kai ni" ya gyada kai yace "Ohk" Sai kuma ya koma ya kwanta, a mugun fusace tace "Kana bata min lokaci lectures din safe gareni, ko kuma ka bani makullin motarmu inyi tafiyata" Khalil yace "Ki jira duk sanda Allah ya nufa kin koma can gidan naku da xama sai ki ci gaba da xuwa makarantar, amma a nan gidan kam ke da fita ko nan da gate sai wani ikon Allah, na soke xuwa wannan makarantar har abada" Da mamaki take kallonsa baki bude, sai kuma ta hadiye abu da kyar tace "Kai kuma a uban wa xaka gaya min haka? Kai a wa xaka soke min xuwa makarantata?" Ya kalleta yace "Kira Abbanki ki tambayesa" Bata san sanda ta fashe da kukan takaici ba tana kallonsa, yace "Allah ya amfana ɗan wanda kika samu" Yana kai wa nan ya mike ya shige daki ya bar ta wajen, sulalewa kasa tayi tana kuka sosai, wai yau common driver ne yake ce mata baxata je makaranta ba wai ya soke, whatttt??? Nihad ta ci kuka ta gode Allah a wajen kafin ta shiga daki, komai na duniyar ta ji ya isheta.... Throughout ranan haka ta yini a kwance tana hawaye, tana mugun son tayi magana da Umma amma babu dama, don babu wayar da xata yi kiran, she needs to tell Umma this, bayan Umma bata da wani wanda xata gaya ma, tana jin an kira la'asar ta mike zaune, sosai kanta yayi mata nauyi, ga magungunanta rabon da ta sha tun jiya, kuma bata jin xata sha, shiru shiru bata ji alamar ya fita gate ba gashi har an tada sallah, mikewa tayi a hankali ta fita parlor, ta dinga bin parlon da kallo ta kalli bakin kofa taga ba takalminsa, to har ya fita kenan bata ji ba, komawa corridor din dakunan tayi ta kai hannunta handle din kofar dakinsa ta murda a hankali kofar ya bude, ta leka cikin dakin ta ga ba kowa, kallon karamar wayarsa dake saman gado ta dinga yi, dai dai nan ya bude kofar bandaki ya fito, tayi masa wani tsinannen harara ta juya ta koma dakinta. Bayan ya dawo masallaci yana zaune compound bai shigo parlon ba yaji an kwankwasa gate, ya dinga kallon gate din kafin ya mike ya tafi bakin gate din, har sannan ba a fasa kwankwasawa ba, yace "Waye?" a fusace Umma tace "Malam xaka bude min kofa ko kuwa? Ji wani tambayar walakanci wai waye, shi dama talaka ai bai iya samun waje ba, ka tashi ka garkame gida kamar na ubanka, da an kwankwasa kuma kace waye, to masu shi ne sai ka bude ko?" Khalil na tsaye yana sauraronta, sai da ya dau kusan 40 seconds kafin ya bude gate din, Umma ce tsaye da su Husnah a bakin gate din, Yayi kasa da kansa yace "Ina yini" Umma tayi mitsi mitsi da ido tace "Ban yini ba, nace ban yini ba, ɗan marasu mutunci" Ya so juyawa ya bar wajen amma ya kasa sbda girma da mutuncin da Abba ke da shi a idonsa, Husnah, Naf da Zully suka dinga kallonsa babu kwakkwaran kiftawa, duk tambaya daya ce ke yawo a xuciyarsu, wannan shi ne dreban, is he the driver? Husnah tace "Umma wai shine driver din??" Umma tace "Gashi kuwa kin gansa" Duk suka kalli junansu, Husnah ta tafe hannu tana kallon khalil tace "Wato kai ne ɗan rainin wayon da ya barmu bakin gate jiya? Kai ga ka shafaffe da mai ko?" Naf na nuna sa da yatsa tace "Kai kana buzu har xaka zo kasar mutane kana bubbusa hanci kamar algaita? Waye kai? Kuma uban me kake takama da shi? Kasan mu su waye da kake tunanin zaka mana walakanci ka kwana lafiya?" Zully tace "Ai ni na ma rasa ta cewa, wato wannan dai shine driver me ba kawar mu though time, toh hasken naka kake takama da shi kake tijara ko me?" Nihad ce ta taho da gudu ganin Umma ta rungumeta cike da farin cikin ganinta, Sai kuma ta sake Umma ta rungume su Husnah gaba daya har da hawayenta sbda tsabar farin ciki, juyawa khalil yayi ya bar wajen kamar zai tashi sama, Husnah tace "Sai ga mu ga ɗan rainin wayon nan yau" Nihad ta sauke wani ajiyar xuciyar takaici, Umma tace "Wato bai baki wayar ba dai" Nihad tace "Wallahi kuwa, ya ki bani" Umma tace "Mu je ciki, sai na ci kaxa kazansa, wato yanxu baya ganin kowa da gashi sbda Alhaji ya gama bada mu gabansa yayi mugun raina mu, yo ya bada mu mana tunda har xai dau yar sa ya basa, idan ma hadin yake son yi ina 'ya yan abokanansa?" Duk suka dukufa xuwa cikin parlon Umma na ƙare ma Khalil zagi su Husnah na tayata, shi kam tuni ya shige daki ya sa makulli, sabuwar waya dal Husnah ta siya ma Nihad har da sim card a ciki, murna wajen Nihad ba a cewa komai, gaba daya ta mance damuwar da take ciki, Umma tace "Kinga shikenan sai ki kwantar da hankalinki yanxu, tunda sun ga gida kullum kya gansu, kafin dai su dawo nan din gaba daya" Nihad ta marairaice tace "Umma fa kulle gate din yake yi kuma makullin na jikinsa" Naf tace "Amma fa kamar a jikin gate din ya bar makullin yanxu da ya bude mana fa" Husnah tace "Idan ko haka ne kawai cirewa xa mu yi mu je a yanko mana spare" Zully tace "Bari in duba" Mikewa tayi ta fita, sai ga ta ta dawo rike da makullin tace "Ai ko dai gashi" Umma tace "Toh Alhamdulillah, tunda dare bai yi ba yanzu me xai hana ku je inda ake yankan spare din a yanka maku?" Naf ta mike tace "Yanzu kuwa, kawai kudi za mu cika masu yau yau din nan xa a yanka a bamu" Naf da Zully ne suka tafi da makullin wajen yankar makulli, Nihad ta dauko ma Husnah makullin kitchen xata dafa masu taliya wai, Nihad na kallon Umma ta marairaice tace "Umma yau na shirya xan je makaranta ya hanani wai ya soke" Buda baki Umma tayi tana kallon Nihad, sai kuma tace "Toh ba a haifi ubansa ba balle shi, shi har ya isa ya soke maki karatu? Bari dai su yanko makullin kawai, ki kwantar da hankalin ki, ai indai da raina babu me cutarki a duniya Nihad, sannan nace maki ki wani manta da batun dreba kiyi rayuwarki yanda kike so, ga makulli nan xa a kawo ai, rayuwarki kawai za ki dinga yi yanda kike so kanki tsaye" Nihad ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh Umma" Umma ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Yanxu shkkn har yau Aliyu ba neme ki ba ko?" Lkci daya hawaye ya kawo idon Nihad ta girgiza kai hawayen na sauka fuskarta tace "Ai blocking dina yayi Umma, kuma sim din ma na karya ai... Umma ban san waye yayi min haka ba kilan don a rabani da Aliyu ne." Kuka take yi sosai kamar ranta xai fita, cikin rawar murya tace "Wallahi ina sonsa Umma, gashi yanxu an rabani da shi" Umma tace "Aa ki daina cewa an raba ku, kina fara xuwa makaranta duk yanda xa ayi ki nemi numbersa ki nema, ba kince min a kawayenki akwai me numbersa ba?" Nihad ta gyada kai hawaye na gangarowa fuskarta tace "Naf tana da numbersa, dama can sun san juna a Uk" Umma tace "Toh ko wajenta ki amsa, kar ma ko da wasa ki wani ce ai Abbanki ya maki aure ko da xa ku fara magana da shi" Nihad dai tayi shiru bata ce komai ba, har kusan magrib Umma na parlor da Nihad, Husnah ta kawo taliyar duk suka ci, all this while kuma khalil na kwance daki ko masallaci bai fita ba, Karfe bakwai su Naf