← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 165

Sashe 120

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To view our catalogue🥰Nihad tayi shiru tana kallonsa jin bai ce komai ba, bayan few seconds cike da karfin hali yace "Baxa ki dauko min ba?" Ta marairaice tace "To wai ba nace maka tsoro nake ji ba, ni baxan iya fita ni kadai ba wallahi, bayan Husnah tace min aljanun dare na gidan nan" Da kyar ya mike zaune ya nuna mata jakarsa murya can kasa yace "Bani shi" Mikewa tayi ta tafi ta dauko jakar ta ajiye masa tana kallonsa, ya jingina da gado, kana ganinsa kasan ba shi da strength, bayan few seconds a hankali ya bude side din jakar ya ciro jotter da biro ya ciri jotter daya ya daura kan main jotter din ya fara rubutu da biron, iya layi hudu yayi rubutun sai kuma ya rubuta digit hudu sannan ya ajiye biron ya kwanta breathing slowly, ta dau takardan tana ta kallon rubutun sai kuma ta kallesa tace "Wa ya koya ma rubutu haka?" Ya nuna mata makullin mota yace "Ki je pharmacy ki basu, akwai Atm card dina a nan, ga pin na rubuta, current account" Sake baki tayi ta kallesa ta sake kallon takardan hannunta, can tace "lallai, kai ne xaka wani rubuta ma kanka magani, a ina ka san magani da har zaka rubuta ma kanka? Ko mutuwa kake so kayi?" fizge takardan hannunta yayi a fusace yace "Bar shi ma" Ta wani hararesa ta kwace takardan tace "Toh a ina aka ce ka siya maganin nan ka sha tunda kai dai ba likita bane" Kamar baxai bata amsa ba don shi kadai yasan me yake ji a jikinsa, sai kuma yayi karfin halin cewa "Likita ya turo min jiya da daddare" Tace "Wannan da ya zo ya dubani ranan?" Mika mata hannu yayi yace "Idan baxa ki je ba bani takardan" Tabe baki tayi ta mike ta tafi inda makullin motar yake ta dauka tare da makullin gida da Atm card dinsa, sai kuma ta kallesa tace "Savings account?" Ba tare da ya buda idonsa da ya kulle ba yace "Current" Tsayawa tayi tana kallonsa, sai kuma tace "Kasan meye current account kuwa?" ya bude ido a hankali yace "Bani, ba sai kinje ba kuma" Ta turo baki tace "To ai ni dai ba ruwana idan naje aka sa current aka rufe maka account dinka" Daga haka ta nufi kofar har ta bude sai kuma ta dawo ta marairaice tace "Ni fa tsoro nake ji" Lumshe ido kawai yayi, tayi shiru tana kallonsa, can ta bude kofar a hankali ta fita kafin kiftawar ido sai ga ta a compound tana maida numfashi, gun motar ta nufa ta bude ta shiga ta kunna tana warming, sauka tayi ta tafi gate amma ta kasa turawa har xata koma ta gaya masa sai kuma a hankali tace "Toh ai shi ma ba iyawa xai yi ba tunda ba shi da lafiya" bude gate din tayi ta fita kofar gida, ganin wani mutumi tace "Don Allah ka tayani bude gate din nan xan fita da mota" yana shigowa zai bude mata ta tafi ta shiga motar, bayan ya bude ta fita da motar waje, tana ganin ya kulle gate din ya fito tayi masa godiya sannan ta sauka ta kulle gidan da makulli ta hau motar xuwa pharmacy, bayan magunguna har da allurai taga an hada mata, ta basu Atm card dinsa da har xata ce masu Savings don bata yarda da current da yace mata ba, sai dai kuma tace "Current" Suka cire kudinsu suka mayar mata da atm card din ta amsa ta dinga jujjuyawa tana kallonsa, daga karshe ta amshi ledan maganin ta fito ta tafi zuwa inda tayi parking. Nihad na isa gida sai da ta kara neman wanda ya bude mata gate ta shiga da mota sannan ya kulle, godiya tayi masa ta nufi kofar shiga ciki ta bude ta tsaya tana bin ko ina na parlon da kallo, to ta ina Aljanun dare xa su shigo gidan bayan ko ina a kulle? sai kuma tayi karfin halin shiga tana tafiya a hankali ta karasa dakinsa ta bude ta shiga, kwance ta samesa yanda ta barsa ta ajiye ledan maganin hannunta ta durkusa tana kallonsa tace "Ga maganin na siyo" Ya bude ido a hankali yana kallonta, ajiye makulli da Atm card din hannunta tayi ta fita daga dakin zuwa kitchen, ba a dau lkci ba ta dawo dakin rike da cup din shayi ta ajiye masa tace "Gashi" Tashi yayi ya zauna ya bude ledan maganin da ta kawo ya fiddo su gaba daya, ta dau cup din shayin ta mika masa tace "Gashi" Ya kalli cup din ya kalleta sai kuma ya amsa, komawa gefe tayi ta zauna, lkci lkci take satan kallonsa kamar yanda shima yake satan kallonta, da sun hada ido kuma sai kowa ya dauke kai, har ya kusa shanye shayin sannan ya ajiye cup din taga ya fara hada allura, tana ta kallon ikon Allah, taga ya sauke trousers dinsa, zaro ido tayi ta kauda kai da sauri ta rufe fuskarta da tafin hannunta, bayan few seconds ta juyo a hankali, empy syringe ta gani, ta mike da sauri tace "Me yasa zaka ma kanka allura?" Bai ko kalleta ba ya bude maganin ya sha da sauran shayin da ya rage sannan ya koma ya kwanta ya lumshe ido ta dinga kallonsa da mamaki, har bayan kusan minti goma bata ga ya bude idon ba sai ma taga kamar bacci yake, juyawa tayi ta fita daga dakin ta koma parlor ta zauna, ko minti sha biyar bata yi a parlon ba taji ana kwankwasa gate, ta tashi da sauri ta koma daki, bacci taga yana yi heavily, ta dau makullin gidan ta fita zuwa gate ta bude, Amina ta gani a tsaye sanye da uniform din islamiyya don ranan lahadi ce, Amina na mika mata waya tace "Ina kwana, wai gashi Umma xata maki magana" Nihad ta amshi wayar sai ga kiran Umma dagawa tayi ta kai kunne daga daya bangaren Umma tace "Kin isa gidan Amina?" A hankali Nihad tace "Umma ina kwana?" Umma tace "Ya haka Nihad, tun jiya ina ta jiranki shiru, Nayi ta kiran Husnah kuma bata daga wayar, ko ta bar gidan ne?" Nihad tace "Ehh ta tafi Umma" Umma tace "Amma ba sai da nace maki kar ki bari ta bar gidan ba sai mun gama magana da ke?" Nihad tace "Nima tashi nayi naga bata gidan" Umma tace "Toh Allah ya kyauta, kin tambayesan kuwa?" Nihad tace "Ehh Umma, yace min sunan Mamarsa Nihad" Umma tace "Amma dai ke shashasha ce wawuya, sai kika yi shiru kika kyalesa da yace maki haka?" Nihad tace "Wallahi haka yace min" Tsaki Umma tayi tace "Baki da wayo ko kadan wallahi, kuma banga alamar za kiyi wayon nan ba, ai shkkn sai kiyi ta zama da dreban, ni sai anjima, haba sai kace ba mace ba ki rasa yanda xa ki bi da shi har ya gaya maki sunan iyayensa, ni gata nake maki, gatan da uwarki ko mutuwa xaki yi baxata ta6a maki ba" Cikin sanyin murya Nihad tace "Toh xan kara tambayarsa Umma kiyi hakuri" Umma tace "Ni sai anjima da Allah" daga haka ta katse wayar cike da bacin rai, Amina ta karba tace "Kin gama?" Nihad bata ce mata komai ba, Amina tace "Sai anjima" Daga haka ta shiga adaidaita da xai kai ta islamiyya don kudin drop Umma ta bata, a hankali Nihad ta juya ta koma cikin gidan. Umma ce zaune gaban wani Rantamemen mutumi ita da Hajiya Turai, Umma na girgiza kai tace "Wallahi Malam ba a samo sunan iyayen nasa ba, kasan yarinyar shashasha ce ga ta kuma er fari, ba wayo" Mutumin dake kallonsu da jajayen tulla tullan idonsa yace "To ai tun farko nace maki xa a iya aiki da sunan nasa kadai kuma aiki zai ci kamar yankan wuka, kawai ku dai in ji dumuss" Umma ta gyara zama tace "Toh madallah malam, kuma ai kai ma kasan kudi ba matsala bace" Yana muxurai yace "Ya kika ce sunan nasa?" Umma tace "Ibrahim" Girgiza kafa ya dinga yi, bayan kusan minti daya ya kalleta da gefen ido yana murmushi yace "Yana nan wani me kyau, dogo sangameme sannan shi ba baki ba, yana kuma da faffadan kirji" Umma tace "Haka yake wallahi malam, duk yanda ka fada wllh haka ne" ya kyalkyale da wani dariya Yace "Toh ai jefaffe ne tun asali, Jifa kuwa ba na wasa ba aka yi masa, ga shi nan naga jifa iri iri a kansa, a jefe yake..." Su Umma dai suka yi shiru suna kallonsa, ya langwabar da kai kamar me nazari sae kuma ya gyada kai yace "Gashi nan an nuna min, ashe ma ruwa biyu ne, ko ta ɓangaren uwa ko na uba" Umma tace "Ba shakka, hakan take malam, ai buzu ne, uwarsa wai er Nijar ce" Yayi wani dariya yana jijjiga kai, Umma tace "Toh amma daga ina aka masa asirin Malam?" Mutumin yayi wani shu'umin murmushi yace "Ɗan wani kauye ne kika ce?" Umma ta girgiza kai tace "Aa, shi dai maigidana ne yasan sunan kauyen nasu tunda har can yaje aka daura auren amma ni ban sani ba gaskiya" Yace "Toh daga kauyen nasu aka jefesa, wato ana masa bakin ciki da ɗan abun da yake samu" Yana gyada kai yace "Shi din me kwazon nema ne tun da ya taso, yana kuma da farin jini, dalilin da yasa ake jifansa kenan.... Sihiri me karfi aka yi masa gashi nan na gani" Umma tace "Ikon Allah, kuma gashi an ga ya fito birni nema dole kuma ya dinga samu sosai" Mutumin yace "Kwarai kuwa, sannan kamar yanda nace maki Allah yayi sa da farin jini da cikar kamala, duk wanda ya ra6a sai ya so shi so na gaske, zai kuma iya damka masa amanar dukiyarsa sbda yarda" Umma ta wani hade rai tace "Toh ni sai6 yanzu so nake ayi masa yanda sisin me gidana baxai sake shiga hannunsa ba don Ubansa, kasa masa mugun tsanarsa wanda xai ji baya son ganinsa baya son mu'amala da shi har abada" Hajiya Turai dake kallonta tace "Idan aka yi haka ke kuma ai sai ya iya cewa
Chapter 120 · 0% Book details