Sashe 33
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mu samu matsala da ita, kawai dai kamata yayi mu ma a kama mana dakin dama dare yayi ba lallai a bari mu shiga schl ba yanxu, idan ya so duk sai mu kwana a nan" Ba don ransa ya so ba haka nan ya kama masu dakin, suka ciccibi Nihad sai dakin suka kwantar da ita saman gado, Husnah dai na ta kaffa kaffa da Iphone din Nihad a wajen tunda ta san halin wasu daga yan matan dake wajen. Sai kusan biyu suka kwanta a dakin bayan duk sun yi wanka. Karfe hudu da rabi Nihad ta farka da wani axababben ciwon kai, da kyar ta mike xaune tana bin dakin da kallo, sai kuma ta sauka tana layi ta nufi kofar dake dakin wanda bandaki ne, ta kuma sani tunda sun saba lodging a wajen ita da su Husnah, tana shiga bayin bayan tayi fitsari taji wani amai ya taho mata, nan ta dinga kwarara aman tana rike da cikinta dake juya mata, da kyar ta wanke bakinta bayan ya lafa mata ta fito, bata sake komawa baccin ba sbda ciwon kai me tsanani da ya takurata, ganin biyar ya kusa ta ta6a Husnah da kyar, ta fi minti goma tana tada Husnah dake xuba minshari kamar wani kato, kafin ta bude ido cikin magagin bacci tace "Wai ya aka yi Nihad?" Da kyar Nihad tace "Don Allah wa xai yi dropping dina gida kafin yan gidanmu suyi noticing bana nan, asuba ya riga yayi" Husnah ta ja tsaki tace "Tsakar daren nan wa xai wani kai ki gida kowa na bacci, ki bari gobe kawai" Nihad tace "Ke asuba fa yayi ki duba agogo ki ga, wllh na manta yayanmu na gida zai iya xuwa bedroom dina yace xai tasheni inyi sallah, idan yana gari duk yana tashin mu...." Husnah tace "Ohh God Nihad ki barni inyi bacci mana, haba" Daga haka ta juya ta ci gaba da baccinta, tashi Nihad tayi da kyar ta bude jakarta ta dau Hijab dinta ta saka sannan ta bude kofar dakin ta fita, babu kowa reception din hotel din sai tv dake aiki, ta fita haraban wajen, wani mutumi ta gani xaune yana ta xukar ta6a a waje, ganinta ya kashe ta6ar, ta nufesa tana kallonsa ganin bahaushe ne tace "Bawan Allah idan babu damuwa ina son taimako wajenka don Allah" Daga sama har kasa yake kallonta yace "Taimakon me?" Tace "Nasarawa GRA nake son ka ajiyeni pls, kawayena da muke tare da su bacci suke ni kuma ban xo da motata ba" Yace "Ohk babu damuwa, bari in dauko makullin motata" Tace "Toh Nagode, nima xan dauko jakata" Daga haka duk suka koma ciki, ta shiga dakinsu, shi ma ya shiga nasa, ta tattara komai nata a jakarta, wayarta ne kawai bata gani ba, zaro ido tayi lkci daya hankalinta ya tashi ta fara tashin Husnah a rikice tace "Husnah ina wayata??" Da kyar Husnah dake ta snore kamar doki ta bude ido, a fusace tace "Ohh my God Nihad ki kyaleni mana inyi bacci, me yasa kin fiye takura ne wai" hankali tashe Nihad tace "Dalla can ina wayata??" Husnah ta ja wani dogon tsaki ta daga pillow dinta ta zaro wayar ta ajiye mata a gefe sannan ta ci gaba da baccinta, Nihad ta sauke ajiyar xuciya sannan ta dau jakarta da wayar da sauri ta fita, Tsaye ta gansa a haraban hotel din yana jiranta jikin motarsa, bayan ta shiga motar shi ma ya shiga, suna fita daga suite din yace "Ku ne ku ka yi birthday jiya?" Gyada masa kai tayi kawai, yace "Gaskiya ne, birthday din na manya ne" Duk surutun da yake Nihad ba tankasa take ba, banda tashi babu abinda xuciyarta yake, she was so uncomfortable, a haka ta dinga daurewa tana masa kwatance har suka isa dai dai inda su Husnah suka dauketa daren jiya, yace "Ina gidan naku?" Ta nuna masa wani layi dake a rufe tace "xan karasa da kafa, kaga gate din a kulle yake" yace "Ohk amma ya sunanki?" Cike da karfin hali tace "Aysha" yace "Maa sha Allah, Aysha ki bani digit dinki mana" ta gyada masa kai kawai, ya mika mata wayarsa ta amsa tayi dialing wani old line dinta dake a kashe tace "Wayar a kashe yake sai na shiga gida na kunna" yace "Toh shkkn nagode Aysha ni sunana Mustapha" tace "Nagode, sae anjima" daga haka ta bude motar ta sauka, cike da karfin hali take tafiya don jiri ke dibanta, ta shiga layin da ta nuna masa, sae da ya ga tayi nisa sosai a layin sannan yayi reverse ya bar wajen, tana waigowa taga ya wuce, ta juya da sauri ta dawo ta fita daga layin sannan ta dau hanyar nasu layin, gani tayi kamar an idar da sallah bayan ta iso kusa da gate din gidansu, da sauri ta bude karfen inda aka xagaye da flowers a kofar gidan nasu ta shige bayan flowers din ta buya tana maida numfashi, don har an fara fitowa daga masallaci, tana jin aka shiga cikin gida aka kulle gate, Sai kuma ta sake jin an bude gate din, Muryar Abbanta taji yana amsa gaisuwa nan bakin kofar gate din, sai da zuciyarta ya kusa shigewa cikinta, ta kara yin lamo a cikin flowers din duk da ant da taji suna cizonta bata damu ba, ta fi minti bakwai a haka bata sake jin motsin kowa ba bakin gate din, hautsinewa cikinta ke yi taji amai na taho mata, kokarin fitowa take yi daga flower din don ta samu ta shige cikin gida, kawai taga mutum xaune a dakalin dake kusa da inda take labe, sai da zuciyarta ya kusa shigewa cikinta don duk xatonta ya Farooq ne don shi ma ya kan xauna a waje idan aka idar da sallah, ya daga kai jin motsi, sai kuma ya mike tsaye da sauri, komawa baya yayi yana kallonta with surprise, ita kuwa tsabar tsorata aman da take rikewa ya taho mata, ta durkusa ta dinga kwarara aman a wajen, kauda kansa yayi bayan yayi perceiving din aman da take yi, ya sake kallonta this time around da wani expression a fuskarsa, duk sae da ta amaye sauran liquor din cikinta sannan ta mike da kyar, ko kallonsa bata yarda tayi ba ta shige gate din gidan, ya bi ta da kallo babu ko kiftawa, ko second ashirin ba ayi da shigarta ba sae ga mai gadi da gudu ya fito waje yana kallon Khalil yana zare ido yace "Ina me tabbatar maka bata kwana gida ba, dawowarta kenan daga duk inda ma taje wllh" Khalil dai bai ce komai ba, mai gadi ya yamutse fuska yace "Ni warin giya ma nake ji, ko kai baka ji ba don Allah?" Khalil ya juya ya shiga gate din gidan ya xauna nan saman bench dake gefen dakin mai gadi with numerous thought running his mind, mai gadin ma ya shigo ya zauna yace "Ni fa sai nake ganin ma kamar warin giya take ko kai baka ji ba?" Khalil ya kallesa yace "Amma baka wanke bakin ka ba ko?" Mai gadi ya ɗan zaro ido, sai kuma yayi yake yace "Ai shi xan wanke ma na fito yanxu..." Tashi yayi da sauri ya shige dakinsa, Khalil ya kalli hanyar gate din, sai kuma ya mike ya fita, jakanta da ya hango cikin flowers da ta bari ya dauko ya shige cikin gidan sannan ya nufi chalet dinsu, A parlor ya tadda Su Saminu sun yi dai dai duk suna bacci, ya ciro makullin daki a aljihu, ya bude dakin sannan ya shiga ya kulle kofar, xaunawa yayi gefen gado ya bude jakar, takalma heels ya fara cirowa da kayan kwalliya da turarruka, sai iphone dinta da ya gani, ya dinga jujjuya wayar don a lock yake, sai kuma ya ajiye ya ci gaba da ciro sauran kayan jakan, bai san sanda ya bude baki ba ganin kwalban Codeine, can ya ajiye a gefe, ya bude wani zip dake cikin jakar, still yayi ya dinga kallon abinda ke wajen babu ko kiftawa, ya kai hannu a hankali ya cirosu gaba daya yana jujjuyawa, prophylactics ne na maza da na mata, ya ajiye su a gefen gado ya mike ya nufi window din dakin yana kallon waje babu ko kiftawa. Nihad na fitowa daga wanka aka bude kofar dakin, sae da zuciyarta ya kusa shigewa cikinta don tsoro, Umma ce ta shigo dakin ta rufe kofar murya can kasa tace "Daga ina kike Nihad?" Nihad ta daburce tace "Ni Umma?" Umma tace "Aa ban son karya ba yanxun nan naga giftawarki ba na fito daga parlon Abbanku?" Nihad tayi narai narai da ido tayi shiru, Umma tace "Gaya min gaskiyan inda kika je" A hankali tace "Wata kawarmu ce ke birthday Umma" Umma tace "Ki dai nutsu, in ma xaki birthday ae sai ji gaya min ni baxan hanaki ba, amma baxa je makarantar yau ba bacci xa kiyi ko?" Tace "Aa xan je" Umma tace "Toh sai kiyi ki shirya karki makara" Daga haka Umma ta juya ta fita, Nihad ta sauke ajiyar xuciya, sai yanxu da ta sake wani aman da xata yi wanka taji ta ɗan fara dawowa dai dai, kanta ya daina juya mata, tana gaban madubi tana shafa mai ta tuna da jakarta, xaro ido tayi ta mike da sauri ta dau hijab dinta gogagge ta saka sannan ta fito daga dakinta, downstairs ta sauka ganin Farooq a xaune dining area tace "Yaya ina kwana?" Yace "Kina jin ina Knocking ki ka ki bude kofa daxu?" Tace "Aa yaya ina bandaki ne, ai na tashi sannan ma" Bai ce komai ba, ta sauke wani boyayyen ajiyar xuciya ta bude kofa, yace "Ina xa ki?" Ta marairaice tace "Xan je in duba ko Allah xai sa tsuntsayen sun dawo" Murmushi kawai yayi ta juya ta fita, da sauri ta nufi gate, taji dadin ganin mai gadi baya bakin gate din, sannan khalil ma baya wajen, tana bude gate ta samesu su biyu xaune kofar gidan, suna hada ido da khalil ta daburce, sai ta hau kame kame, bata amsa gaisuwar da mai gadi ke mata ba tace "Aminu a layin nan babu inda