← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 165

Sashe 40

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

yayi dialing number din sa sannan ya mika mata, amsa tayi ta kira number, karamar wayar dake aljihunsa ya fara ring, tace "Nagode" daga haka ta bude motar ta sauka, Nihad dake ta kallon ikon Allah ta ja tsaki me tsayi sannan ta sauka, ko barin wajen motar basu yi ba tace "Me ye na wani exchanging digit da driver idan ba kaskantar da kai ba Nihal? Me yasa ke kin fiye over sabi a rayuwarki? Ni ban san me yasa ke da Mumy ku ke yin haka ba wllh" Nihal taki tanka mata, Nihad tace "Though wannan ba damuwata bace, my problem is ban ji kin masa maganar jakata da wayana ba?" Nihal tace "Xan yi" Suna shiga mall din, Nihal ta fara daukan abubuwan da ta xo siya tana xubawa a cart Nihad na tura mata cart din, duk inda suka gifta sae an kallesu don babu wanda bazai ce su ba yan biyu bane, they look so cute, beautiful and adorable, kawai dai Nihad ta fi Nihal haske da tsayin hanci with more cute lips, ita kuma Nihal ta fi Nihad cika, though she isn't chubby but ta fi Nihad warce iska me karfi idan aka yi xae iya tafiya da ita... Lol, tsayinsu daya haka ma shape din large eyes dinsu, sae dai kana kallonsu kasan Nihad tafi Nihal wayewa nesa ba kusa ba, ganin Nihad isn't taking anything Nihal tace "But kince kema xa kiyi shopping kin fasa ne?" Nihad ta yatsina fuska tace "I won't shop here" Nihal bata kuma ce mata komai ba, har ta gama daukan duk abinda xata bukata a makaranta, sannan ta dau ma Umma turarurrukan da tace, wani tsadadden turare da ta san Nihad na so ta daukar mata, Nihad ta amsa tace "Thank you" Daga haka ta saka shi cikin cart din, Nihal ta dau wayarta tayi dialing number da Khalil ya sa mata with the intention of asking him a question, can kuma dae kawai ta katse ta fasa kiran nasa sbda Nihad dake ta kallonta, wasu turarurrukan biyu ta deba ta sa a cart sannan tace "Shikenan na gama" Nihad ta tura cart din suka nufi counter. Suna tsaye counter din Nihad tace "Na manta xan dau Sanitary Napkin" Daga haka ta juya zuwa in da zata dauka, khalil ya shigo cikin mall din with facemask, yana hango Nihal a counter ya nufi wajen yana kallonta yace "Naga kiran ki..." Nihal tace "Oh bansan ya shiga ba" Yace "Ohk, sun gama in dau kayan?" Xata yi magana kawai wata yarinya kamar balarabiya ta nufosu tana kallon Khalil closely tace "KJay?" Juyawa yayi da sauri, Ta wara ido kafin ta ce komai yace "Ohh Nadiya, daga ina haka?" Ta kyalkyale da dariya tace "How wonderful i recognized u upon the nose mask KJay..." Ya kalli Nihal da sauri yace "erm, yi hakuri don Allah minti daya..." kawai yace "Mu yi magana a waje Nadiya" yana fadin haka ya bar wajen da sauri, Sai a sannan Nadiyar ta kalli Nihal dake ta kallonta daga sama har kasa, Nadiya ta daga mata hannu tace "Hi" Nihal tayi murmushi ta daga mata hannu ita ma, juyawa tayi ta bi bayan khalil da har ya fita mall din, Nihal ta bi ta da kallo, har gadon baya ta saki dogon baƙin gashin kanta, daga ganinta kasan half cast ce, sae ga Nihad ta ajiye Sanitary Napkin din a kan counter, tana kallon Nihal sai kuma ta kalli inda take ta kallo amma tuni Nadiya ta fita daga mall din, Nihad tace "What are u staring at?" Nihal ta dauke kanta da sauri tace "Nothing" ma'aikatan wajen ne suka kwasar masu kayan xuwa mota bayan an biya kudin kayan, Khalil na jingine jikin mota ya rungume hannunsa, ganin sun fito ya xaga ya bude booth din motar, wanda ya tayasu fito da kayan ya shigar cikin booth, Nihal ta bude handbag dinta ta dau dari biyar ta basa, yayi mata godiya sannan ya wuce, tuni Nihad ta shige bayan mota, Nihal ta xauna gaban motar, ya tada motar suka bar shopping mall din. Tunani iri iri ke yawo a xuciyar Nihal, she can't even think straight, Nihad kuma ta kasa kunne taji Nihal tayi ma Khalil maganar wayarta amma shiru, har ta shirya rashin mutuncin da xa tayi mata suna shiga gida don dab suke da isa gidan kawai ta ga Nihal ta kallesa tace "Ina son xan maka magana don Allah" Bai kalleta ba idonsa na kan titi yace "Toh ina jin ki Hajiya" Ina a polite state tace "Jakar Nihad yana wajenka ko?" Yayi ɗan yi shiru kamar baxai ce komai ba, Nihal dai kallonsa kawai take, sai kuma yace "Eh yana wajena" Tace "Toh xaka bani don Allah idan mun isa gida" Yace "Toh ba damuwa, in sha Allah" Nihad ta galla masa wani tsinannen harara ta kauda kai, da yace baxai bada ba ya gani mana, suna isa gida yayi parking Nihad ta bude motar ta sauka ta tsaya nan parking space babu yabo babu fallasa tana jiran jakarta. Nihal ta sauka ya bude mata booth ya saukar da kayan kasa, xagawa tayi xuwa gun Nihad tace "Ki tafi ciki, ai xan amsar maki" Nihad tace "Nooo, Baxan tafi ba, ina nan ina jira" Khalil dake jin abinda tace, ya dai kwashi kayan Nihal gaba daya ya kai mata can bakin kofar shiga main building din gidan ya ajiye, Nihal na tsaye har ya dawo yana kallonta yace "Anjima da daddare xan baki jakar idan na shiga can bangaren kenan" Nihad tace "Ban gane anjima da daddare ba, kai ko kunyan sata baka ji ba a ranka, to tun wuri ka shiga yanxun nan ka fito min da jakata kar in tara maka mutanen gidan nan, wallahi rashin mutunci xan maka don ma kaji in gaya maka" Khalil ya kalleta yace "Toh" Daga haka ya tafi wajen mai gadi yayi xamansa, a fusace Nihad ta kalli Nihal tace "Kina dai gani ko, wllh sai na nuna masa wacece ni yau kar ya fito min da jakata" Nihal tace "Ba sai da nace ki shiga ciki xan taho maki da shi ba, toh ai gashi nan kin ji" Nihad tace "Na ji me? Ai jakata baxata kara minti biyar a hannunsa ba, bari ya gani" Tana fadin haka ta juya fuuu ta wuce cikin gida, ita damuwarta kar ya ba Nihal jakar ta bude taga kayan Husnah dake ciki, Nihal ta nufe Khalil dake kusa da mai gadi ta mika masa ledan hannunta tace "Gashi nan na daukar maka kai ma, amma don Allah kayi hakuri ka bamu jakar yanxu" Yana kallon ledan yace "Nagode sosai Hajiya, Allah ya saka da alkhairi.... Bari in dauko maki jakar" Daga haka ya mike ya nufi chalet, ta bi sa da kallo sannan ta bi bayansa, da ya lura tana biye da shi, sai yayi slowing pace dinsa, tana isa kusa da shi tace "Ina son xan maka tambaya" suna ci gaba da tafiya ba tare da ya kalleta ba yace "Ohk ina sauraronki?" Tace "Tell me... who are you?" Ya ɗan yi jim sai kuma yayi saurin cewa "Ban gane abinda kike nufi ba" Tace "Nasan ka gane" Yace "Da gaske ban gane ba" suna isa Chalet din kafin tace komai, yayi maza yace "Ina xuwa in dauko jajad yanxu" daga haka ya shiga ciki ta bi sa da kallo, ba a dau lkci ba ya dawo rike da jakar Nihad, a bude zip din jakar yake, ya mika ma Nihal ta amsa, babu abinda idonta ya fara cin karo da sai kwalban Codeine da prophylactics da ke saman jakar, lkci daya ta rude apart from being shock, bata san sanda ta rungume jakar ta juya da sauri xata bar wajen ba, yace "Ga wayarta" Nihal ta juyo da kyar amma ta kasa barin su hada ido, ta dai amshi wayar da yake mika mata ta juya ta bar wajen tana tafiya da sauri, tana shiga gida direct dakin Nihad ta wuce, Nihad xata fito daga dakin kenan suka kusa cin karo, Nihad ta koma baya, Nihal ta shiga dakin ta jefa mata jakar a kasa tana girgiza kai sadly tace "Nihad meye wannan a cikin jakar ki??" Nihad ta kalli jakar lkci daya gabanta ya fadi, Nihal ta karasa cikin dakin ta xauna gefen gado ta dafe kanta, Nihad dai sai kallon jakarta take tana tunanin abinda xata ma khalil taji sanyi a ranta, ko daxu da ta bude jakar bata ga abubuwan nan a saman jakar ba, wato shi ya daura su saman jakar ya bar zip a bude don Nihal ta gani, Bayan kusan minti daya Nihad ta kalli Nihal, hawaye ta gani idonta, Nihad tace "Look Nihal wllh wllh ba kayana bane na Husnah ne, haba don't u trust me?? kema kinsan i can neva posses such stuffs, i swear to God na Husnah ne, shi kuma munafuki algungumin da ya daura a saman jakar ya jira ya ga abinda xai faru da shi a gidan nan" Tana fadin haka ta durkusa ta hau tattara abubuwan dake cikin jakar ta kulle, Nihal dai bata ce komai ba ta mike a sanyaye ta ajiye mata wayarta a gefen gado sannan ta fice daga dakin.
Chapter 40 · 0% Book details