← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 165

Sashe 12

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan minti talatin da biyar Nihad ta gaji da jiran Abbanta don har sannan bai fito daga gidan ba, ga kiran da Husnah ke ta yi mata taki dagawa don bata son tace mata bata gida tasan baxata jira ta ba, kallon agogon dake makale hannunta tayi ganin sha biyu har da minti goma ta tashi daga kan kujerar da take ta nufi khalil, Babu yabo babu fallasa tace "Hey xan koma gida kayi dropping dina yanxu" Sai da ya fara kallon mai gadi dake gefensa kamar dai da mai gadin take, ta daure fuska tace "Malam da kai fa nake?" Sai a sannan ya kalleta ya d'an kara kunnensa gaba yace "Na'am" Rasa ma me zata ce masa tayi saboda bakin ciki, har sannan fuskarta a daure tace "Ina ga dai kana da matsalar ji, dalla malam ka tashi ka maida ni gida" Yace "Naga ai Alhajin bai fito ba" Tana masa wani kallo tace "Eh na fi ka sanin bai fito ba" Yace "To kar ya fito ya tarar bana nan" Ta rike kugu cike da masifa tace "Sai ka maida ni, idan ka maida ni xaka iya dawowa idan ka ga dama" Ya dauke kai yayi shiru bai ce komai ba, shi dai mai gadi sai mazurai yake da ido babu damar ya kwaba ma khalil, shi tsoronsa ma kada wnn ɗan abin ya sa ya rasa aikinsa, yana ga kamar Khalil bai ta6a aiki gidan masu hannu da shuni bane shi yasa har ya tsaya suna ja in ja da Hajiya karama banda haka ina shi ina biyeta, ai duk abinda tace haka xa ayi, tsawar Nihad ne ya dawo da mai gadin reality don sai da ya tsorata, "Dalla Malam kana bata min lkci, are you even okay, how dare u query my order? Ko dai kana shaye shaye ne???" Khalil ya ɗan kalleta, sae kuma ya mike ya nufi motar, ta ja wani dogon tsaki ta bi bayansa kamar xata tashi sama tana harararsa, duk sai taji ranta yayi mugun baci, bayan mota ta bude ta shiga, tuni mai gadi har ya wangale gate yana daga mata hannu alamar Allah ya tsare, Khalil yayi reverse ya fita daga compound din, cikin mintuna kadan ya isa gida da ita, yana parking dai dai gate ta ja tsaki ta bude motar ta fice without closing the door, da ido ya bi ta har ta shiga gate din gidan, ya fi minti biyar tsaye da motar, daga bisanni ya sauka ya kulle door din motar, sannan ya shiga yyi reverse ya bar layin ya koma can gidan da Abba yake. Nihad na shiga gida bangaren Umma ta nufa, jefar da jakarta tayi saman kujeran parlon tana kallon Umma tace "Umma wani irin driver ne wannan Abba yayi employing, who even linked them? wllh yaron bai da kunya ko kadan Umma, kinga abinda yayi min kuwa??" Umma ta ajiye kayan hannunta tana kallonta tace "Me yayi maki?" Nihad tace "Wllh rashin kunya yayi min, ni babu wani wanda ya ta6a min haka ma tun da nake, wai yaron ya maida ni gida yaki fa" Umma tace "Aa abu me sauki sae ayi ma Abban naku magana ya sallamesa, halan d'an kauye ne?" Nihad tace "Toh ae dama su ne masu wannan tsagerancin da rashin ta idon, wllh Umma wannan idan yayi wata daya a gidan nan daina kai mu duk inda xa mu xae yi, Allah cewa xai dinga yi baxae je ba kansa tsaye idan ma bai hada mana da zagi ba, gwara kawai Abba ya dawo ya sallamesa a samo wani dama ni bai min ba from the start, irinsu ne idan an shigo da su inuwa su maida mutum rana, wai kinga me yayi min ne, jayayya fa muka tsaya muna yi da shi" Daga haka ta fice daga parlon ta tafi dakinta don ta shirya xuwa inda xa su hadu da Husnah, sae dae tana tsaka da shiryawa ta dinga kiran wayar Husnah ta ji a kashe, lkci daya ranta ya baci, kaddai har tayi tafiyarta, ta zauna gefen gado tana ta trying din layin amma ya ki connecting. Ana kiran sllhn Azahar Abba ya fito daga gidan tare da wata tsohuwa, Khalil ya mike tsaye ganinsu, suna karasowa inda yake Abba yace "Sabon drivern da na dauka kenan Hajiya, yau ya fara aiki..." Tsohuwar ta kallesa daga sama har kasa tace "To ba laifi, kuma da ganinsa xae fi Habibu kwazo duba da halittarsa, kawai dae sai mu yi fatan Allah ya sa ya fi Habibu nutsuwa, don Habibu ni kadai nasan ɗan iska" Khalil yayi kasa da kai tare da risinawa yace "Ina yini Hajiya" da fara'a tace "Lafiya lau, amma kai buzu ne koh?" Ya murmusa yana girgiza kai, Tsohuwar tace "Toh a dai kula da dukiyar mutane ka ji, kai ma sai kaga Allah ya kula da kai, baka ga motar da Habibu ya ajiye kafin ya tafi ba, duk ta fita hayyacinta daga karshe konden konden aka siyar ma, su ma din dai a walakance suka siya, ya sunanka?" Yace "Ibrahim" Buda baki tayi tace "Ikon Allah, Kai ae kawai ka zama d'an gida abun ka daga yau ka ji, babu me raina ka ko waye shi, kanka tsaye kar ka yarda da hakan, ae sunan Uban gidan naka kenan, kuma ni na haifesa, Allah yayi maku albarka gaba daya" yana murmushi yace "Ameen" Abba yace "Toh ki koma haka Hajiya, ni xan tafi" Tace "To Allah ya tsare, idan Habubakar din ya dawo xan tattauna da shi" Yace "Ba laifi, sae anjima" daga haka ya nufi motar, Khalil na biye da shi a baya. Yana ajiye Abba a gida, Abba yace "Ka tafi islamiyya ka dauko yara nasan sun tashi ynxu" Khalil yace "Toh in sha Allah" hanyar makarantar ya nufa, yana parking bakin gate sae ga Nihal, sannan Fadil da Sudais, Amina ce karshen fitowa duk suka shige bayan motar, ita kuma ta xauna gaba, ta madubi yake kallon Nihal, tace "Barka da rana" xai amsa Sudais da Fadil suka gaishesa su ma, amsa masu yayi gaba daya sannan ya maida hankalinsa kan driving din da yake. Nihad na tsaye bakin parlon Abba tana jiran ya amsa sallamar da tayi, yana amsawa ta shiga, ta karasa parlon ta xauna saman kujera tace "Abba ina yini" yace "Nihad me yasa kika ki shiga ku gaisa da inna da mutanen gidan?" Ta langwabar da kai bata ce komai ba, glasses dinsa ya saka yana maida dubansa kan laptop din gabansa, tace "Abba i came to report this new driver to you" Sake kallonta yayi yace "What about him?" Tace "Abba kawai don nace ya maida ni gida i am press shine mutumin nan ya ki, infact yi yayi kamar bai ji abinda nake cewa ba ya bar ni a tsaye" Abba yace "Is that so?" Tace "Wllh Abba, and it's not as if i was rude to him, kawai cewa nayi don Allah ka maida ni gida ina son xan koma, kawai sai yayi min banxa, wllh Sagir mai gadi ne shaidata" Abba dai yayi shiru yana kallonta, bude kofar parlon Abba aka yi sai ga su Sudais da Fadil sun shigo gaida Abban nasu ganin motarsa a gida, Nihal ce ta shigo bayansu, Abba yace "Welcome Nihal, tell the driver to wait me at the balcony...." Juyawa tayi ta fita, ba a wani dau lkci ba sai ga ta ta dawo tace "Abba na gaya masa" Abba ya ajiye laptop din kafarsa ya mike ya nufi kofa, Nihad taji wani dadi har cikin ranta dama babu abinda xata ce ma Abbanta tana so da baya yi, mikewa tayi da sauri ta bi bayansa Nihal ta bi ta da kallo, Abba na kallon Khalil bayan ya zauna saman daya daga kujerun dake wajen yace "Ibrahim me yasa tace ka maido ta gida ka ki?" Khalil ya durkusa kasa yace "Yallabai ban ki ba, ce mata nayi kar ka fito ka tarar bana nan kace inyi jiranka, amma daga karshe na daukota na dawo da ita gidan" Nihad dake jikin kofa ta hade rai jin abinda yace, Abba ya juya ya kalleta yace "Is that so?" Tace "To Abba sae fa da ya ja min rai, maimakon ina gaya masa kawai ya tashi ya kai ni gida" Abba ya kalli khalil yace "Je ka" Mikewa Khalil yayi yana kallonta yace "Kiyi hakuri, ban san haƙan xai bata maki rai ba" Wani shegen kallo tayi masa ta juya tayi wucewarta ciki. Bangaren Umma Nihad ta koma, Kamar xata fashe da kuka tace "Umma kin ga Abba bai dauki ko wani action ba dai ko?" Umma tace "Sai yace masa me?" Tace "Ba abinda yace masa, ni wllh sai dai duk abinda xai faru ya faru, da kaina xan dinga driving kaina, gashi gobe ina da lectures karfe goma a haka xai kai ni schl din? Nooo i will prefer to drive my sef" Umma tace "To idan kika tafi da motar da wanne xa a dauko kannenki daga makaranta?" Tace "Ba ga motar yaya Farooq ba ko yaya Usman" Bata jira me umma xata ce ba ta fita daga parlon xuwa kitchen, Aminu mai gadi ta gani a windown kitchen din ta baya, mai aikinsu Hafsah tana xuba wani abinci a plate, kallonta tayi tace "Abincin waye wannan?" Kafin tayi magana Aminu yace "Na sabon dreba ne" Buda baki tayi tace "Shi ma din sai an dinga basa abincin a nan? Waye yace haka?" Daga mai aiki har mai gadin suka yi shiru, tace "Ohh kawai ku kuka tsara hakan sbda ku ke siyan kayan abinci?? To Abba bai ce haka ba, ni ma kuma bance ba, saboda haka ajiye abincin nan dake hannunki baxa a kai ba, kai kuma Aminu ka kama gabanka, ba shi da portion din abinci a gidan nan" juyawa Aminu yayi ya bar wajen a sanyaye, Hafsah ta nemi plate ta rufe abincin ita ma a sanyaye, tsaki Nihad tayi ta dau plate ta debi abinda xata deba ta cika nama sannan ta fita, tana fita Nihal ta shigo kitchen din ita ma xata xuba abinci, ganin wanda Hafsah ta rufe tace "Hafsah wannan wa ya ci ya rage?" Hafsah dake wanke wanke tace "Aa ban
Chapter 12 · 0% Book details