Sashe 7
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
sbda kiran yan uwa da abokan arziki da suka san Nihad, Abba yayi gyaran murya yace "Ban ga laifinki ba Maryam don ni nasan kinyi iya bakin kokarin ki na ganin kin ba ma Nihad tarbiya yanda ya kamata, u tried ur best, matsalar kawai u didn't make Nihad ur frnd aside mothering her, amma dai babu komai, kawai dai kafin Nihad ta dauko mana abinda xuciyarmu xai kasa dauka nan gaba tun wuri ni da yayana da yan uwana mun mikata, kusan xance na bada sadakarta" Abba na fadin haka ya ciro sadakinta dake aljihunsa ya mika ma Umma yace "Sai ki damka mata ku da xa ku kai ta" Umma ta amsa cikin sanyin murya tace "Yanxu Yallabai mun yi deserving a bada er mu ba tare da mun san wanda aka ba ma ba? Ai hankalinmu baxai taba kwanciya ba, tun jiya nake bin ka kaki gaya min, ai yana da kyau a sanar mana mu sani don muna da hakkin sani, idan ma ni bani da hakkin in sani mahaifiyarta fa?" Abba ya ɗan yi shiru, sai kuma ya dau wayarsa yayi dialing number snn ya kai kunne, ana dagawa yace "Ka shigo nan parlor ka sameni yanzu" daga haka ya katse wayar, duk kowa yayi shiru ya xuba ido ya ga wanda xai shigo parlon barin Farooq da Umma. Da sallama ya bude kofar parlon, ganin su Umma ya dakata daga bakin kofar bai shigo ba, Abba na kallonsa yace "Karaso" ya karasa shiga cikin parlon kansa a kasa, duk occupant din parlon kallonsa suke with full shock, Abba ya nunasa yace "Shi na ba auren Nihad, shine mijinta" Mikewa Farooq yayi yana kallon Abba baki bude, Mumy ta hadiyi wani kullutu da taji ya tokareta a makogwaro, Umma kuwa sae kallonsa take daga sama har kasa babu ko kiftawa, ta ma rasa yanayin da take ciki ita, Kowa na parlon ya kasa cewa komai, tsabar silence din parlon da allura xai fadi xa a ji karar faduwarsa, shi kam dai yana ta tsaye ya sunkui da kai har sannan, Abba yayi breaking silent din yace "Je ka" Juyawa yayi ya fita daga parlon, Usman ya kalli Abba yace "Haba Dad? Yanxu shi ka aura ma Nihad?" Farooq yace "No Abba, u should have given her a choice, bata yi deserving ayi mata dole ba sbda wannan kaddarar tata, but Abba...." Kasa cewa komai yayi ya koma ya xauna, shi ma ya rasa yanayin da yake ciki, but he don't think it's still bad after all, just dat.... Girgiza kai kawai yayi, Umma tace "Haba Alhaji...." Abba ya mike yana bin kowa da kallo yace "No one have the right to query my authority" Yana fadin haka ya bar masu parlon ya shiga bedroom dinsa, suka dinga kallon kallo a tsakaninsu a parlon, Usman ne ya fara mikewa ya fice daga parlon, Mumy ta mike ta bi bayansa ita ma tana share idonta, Umma ta sauke ajiyar xuciya tana kallon Farooq, ita gaba daya ma kanta fa ya kulle, Abba really took them unaware, jinginar da kanta tayi da kujera Farooq ya mike ya fice daga parlon shi ma. Ana idar da magrib yan kai amarya suka fara shirye shiryen kai ta, Nihad bata ta6a shiga irin tashin hankalin da take ciki ba a wannan moment din, ko video dinta bai tada hankalinta kamar yanxu ba, gashi nobody is there to console her, Nihal na schl, Husnah kuma taki xuwa gidan sbda Farooq, gashi bata da numberta a kai balle ta amshi wayar wani ta kirata, su kamila da Amina tamkar ma farin ciki da abinda ya sameta suke don uban kwalliya suka ci har da kashe dauri Hajiya Zuwaira ce ta kai ta gun Mumy tayi mata fada ta sa mata albarka, sbda takaici da bakin ciki Mumy ta ki cewa komai daga karshe da aka tilastata sae cewa tayi Allah ya tsare, Alhaji Abubakar ne kawai yayi mata fada, Abba kuwa tun da aka idar da magrib ya ki shigowa gidan dama, a haka dai aka tattara ta da akwatunan kayanta uku wanda Umma da Kamila suka hada mata wasu kayayyakinta a ciki, kuka take kamar xata shide, har addu'a ta dinga yi Allah ya dau ranta kafin a karasa da ita gidan, tana ganin an shiga gidan ta kara sautin kukan da take a haka har aka shigar da ita daki, gida ne bungalow madaidaici me dakuna uku, ko wani daki da bandaki, sae bandakin dake parlor sai kitchen, anyi furnishing gidan babu laifi sai dai furnitures din ba masu tsada bane, Nihad ta dinga kuka tana cewa ta shiga uku, masu bata bakin ma har sun gaji sun daina, karfe tara saura suka fara shirin tafiya, Nihad ta rike hannun Kamila cikin kuka tace "Aunty ynxu tafiya xa ku yi ku bar ni, don Allah kar kuyi min haka..." Kamila tayi dariya tace "Ae ko dole xa mu yi maki haka tunda mun kawo ki gidan mijinki kinga ni ynxu sae na koma xan dau jakata inyi driving xuwa gida, kawai kiyi hakuri ki bi mijinki ku xauna lafiya ko hakan xai goge wannan ta6on da kika ma kanki" Daga haka ta fice daga dakin don dama ita ce karshen fita, Nihad ta silalo kasa ta xauna tana kukan takaici, tana jin duk suka fice daga gidan ta daina jin hayaniyar kowa, nan kuma tunanin ta ya tafi gun wanda xata gani a matsayin mijinta, tsoho ne, yaro ne, baki ne, fari ne, kato ne, siriri ne, mummuna ne, kyakkyawa ne, infact duk wannan tunanin ne suka baibaye ranta gabanta ya dinga faduwa hankalinta ya kara tashi, daga karshe ma daina kukan tayi banda bugawa babu abinda xuciyarta yake, ta fi minti ashirin a haka taji an bude gate, da sauri ta mike ta tafi gun window ta bude labule amma sai taga ba ta nan gate din ma yake ba balle taga me shigowa, komawa tayi ta xauna can karshen gado tana jin yanda kirjinta ke heaving, to waye wannan da ko mota ba shi da, bayan wasu mintuna taji an shigo parlor, daga karshe ta ji kamar an bude wani daki an shiga, mikewa tayi ta jingina da window with so much fear, har ta gaji da tsayuwa bata ga alamar xa a shigo dakin ba, komawa tayi ta xauna gefen gado, a kan idonta karfe sha daya tayi, bacci take ji amma taki kwanciya sbda fargaba, kafin sha biyu bacci barawo ya saceta. Ba ita ta bude ido ba sae da hasken rana ya sauka saman fuskarta washegari da safe, a firgice ta mike xaune, sae kuma ta sauka daga saman gadon ta shige bandaki da sauri, bayan ta idar da sallah ta mike a hankali ta nufi kofar dakin ta bude ta fita xuwa parlor, ta dinga bin ko ina da kallo xuciyarta na bugawa, kofar da take tunanin kitchen ne ta nufa ta bude kofar a hankali, wani kara ta saki ba tare da ta shirya ba ganin mutum a tsaye yayi backing kofar kitchen din ga ruwa ya daura saman gas, juyowa yayi suka yi ido hudu da ita, wani irin shock ne ya bayyana a fuskarta ta dinga komawa baya tana kallonsa bakinta ya kasa furta komai, can ta nunasa da yatsa nan ma words suka yi failing dinta, juyawa yayi ya kashe gas din don ruwan ya fara tafasa ya juye cikin mug sannan ya bi gefenta ya fice daga kitchen din ba tare da ya sake kallonta ba, makalkalewa tayi jikin kofa jikinta na 6ari tana ganin abun kamar a mafarki, sae a sannan bakinta ya bude ta fasa wani raxanannen ihu, sai kuma ta fara ganin kitchen din na juya mata lkci daya ta sulale kasa....