Sashe 103
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
yace "Kuma Ummanku bata ce komai ba?" Nihal ta girgiza kai tace "Kawai ce min tayi inyi hakuri in tafi ABU din" Khalil ya gyada kai yace "Amma secondary daya ku ka yi ko?" Nihal ta girgiza kai tace "Shi ma ba daya muka yi ba, ita Nigerian Turkish tayi, ni kuma Yan dutse nayi" Khalil ya gyada kai yace "Ohk, yan dutsen kamar su Amina da Sudais nan suke xuwa ko?" Nihal tace "Har Aunty Kamila da Ya Usman da ya farooq ma can suka yi, Nihad kadai ce tayi Nigerian turkish" Khalil yace "Amma kamar er uwartaki tafi sabawa da Ummanki akan mamanta ko" Nihal tace "To ai a bangaren Umma take, ni kuma ina side din Mum dinta, though I don't know for her" Shiru Khalil yayi yana kallonta, can yace "Maa sha Allah, hakan yayi.... amma wani saurayinta da ya zo can gida ranan, sun dade tare ne?" Nihal tace "Wai Aliyu? Yea definitely shi, don ita bata kula wani saurayi idan ba shi ba, shekaran da ta shiga Maryam Abatcha suka hadu, shekara uku kenan" Yace "Ohk, kinsan saurayin sosai kenan?" Nihal ta bude ido tace "Nasan shi mana, he is the son of General Jikamshi..." Muryan Nihad dake labe jikin pillar din corridor tum daxu ya katse Nihal, cike da bacin rai Nihad tace "A gidan uwar wa kika san shi? Shi Aliyun kike tunani kinsani? Har da wani gaya masa sunan babansa salon yayi masa mugun abu irin nasu na kauye? To wallahi baki san shi ba kuma baxa ki ta6a saninsa ba, dama don ki zo ki hadu da wannan mutumin ku kafa munafurcina ya sa kika zo gidan nan ashe ban sani ba? To wallahi ni dai ki tashi ki tafi baxa ki kwanan min a gida ba, ai dai mun ga juna, har da wani ce masa ni kadai nayi Nigerian turkish, to wani yace kar kema kice ma Abba can kike so? Naga dai choice dina ne kuma Abba yayi accepting, sannan Maryam Abatcha ma wani yace kar ki sakar ma Abba kuka kice ke baxa ki je ABU ba sai dai Maryam Abatcha? Wallahi kin ban mamaki har xaki zauna da bare kuna cakalkalar namana ko tausayina baki ji ba, to Allah ya isa wannan gulman nawa da kika yi" Nihal dai bata ce mata komai ba, Banda kallon Nihad babu abinda khalil ke yi, tana huci tace "Shi kuma saboda gulma har da wani cewa nafi son Umma, dama ashe maza na gulma ban sani ba? Kuma ai Umma da Mumy duk daya suke a wajena babu wani bambanci, to tunda dai mun ga juna zo ki dau handbag dinki kiyi tafiyarki" Mikewa Nihal tayi ta nufi daki, Nihad ta bi ta da harara, sai ga ta ta fito sanye da hijab tana rike da handbag dinta ganin xata nufi kofa Nihad ta rikota tace "Ina xa ki tafi da daddaren nan" Nihal ta fizge Hijab dinta hawaye cike idonta ta nufi kofa, Nihad ta bi bayanta da sauri tace "Ke ni fa wasa nake maki ina zaki da daddaren nan" Tuni Nihal ta fice daga parlon, Nihad ta marairaice tana kallon Khalil tace "Don Allah kayi mata magana, ni wallahi ba haka nake nufi ba" Ko kallonta Khalil bai yi ba, hakan yasa ta fita da sauri, can ta tarar da Nihal zaune bakin gate dake kulle tana rera kuka, kukan ta ita ma ta fara ta durkusa gabanta tace "Don Allah kiyi hakuri wallahi i didn't mean it, ni ba da ke nake ba, da shi nake"