← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 165

Sashe 109

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya gaishesa kansa a kasa, kallonsa kawai Abba yake yana son jin me ke tafe da shi, hoping ba wani abun Nihad tayi masa ba, Khalil yayi kasa da murya yace "Alhaji dama na zo neman alfarma ne gun ka" Abba na kallonsa yace "Ina jin ka Ibrahim, fadi koma meye kanka tsaye" Khalil yace "Ina son xan koma garin mahaifiyata can Zaria tare da ita... Saboda xan ɗan yi noma a can tunda damuna ya fadi" Abba yace "Yanzu ai karkashin ikon ka take Ibrahim, ba sai ka tambayeni izini ba don xaka canza wajen zama da ita, iyaka ka sanar min don in maku fatan alkhairi sannan idan da tallafawan da xan maku sai a maku" Khalil dai ya sunkuyar da kansa, Abba yace "Maa sha Allah naji dadin noma da kace zaka yi, don noma ai shine tushen arziki dama, Allah Ubangiji ya baka nasara Ibrahim" Khalil yace "Ameen Alhaji, nagode" Abba yace "Yanzu dai ka sa a bincika maka nawa ake bada hayan gida a garin" Khalil yace "Ina da wani aboki a can na tambayesa jiya" Abba yace "Nawa yace maka?" Khalil yace "Dubu dari yace min" Kallonsa Abba yake ba ko kiftawa, can yace "Aa da dai a samo na sama da hakan Ibrahim, ni ko nawa ne ba matsala bane xan bada" Khalil na kallon Abba yace "Gidan a kusa da kauyen da xan yi noman yake, shi sa nace xan amsa" Abba yace "Dubu dari nawa kace?" Khalil yace "Dubu dari daya" Abba ya kasa cewa komai yana kallonsa, Gaba daya tunaninsa na kan Nihad duk da haushinta da yake kwana yake tashi da shi a ransa yasan baxai ta6a son ta zama uncomfortable a rayuwarta ba, deep down him yasan he still love his daughter" Abba ya sauke boyayyen ajiyar xuciya yace "Shikenan zan sa maka kudin" Khalil yayi noticing change a muryar Abba hakan ya sa bai dago kansa ba, Abba yayi breaking few second silence da ya biyo baya yace "Yaushe xa ku tafi?" Khalil yace "Ko zuwa satin da xa mu shiga in sha Allah" Abba yace "Ohk to amma ka sa abokin naka ya ɗan bincika min ko za a samu filaye a nan arean" Khalil ya daga kai ya kalli Abba yace "Toh Alhaji" Abba yace "Ina sauraronka zuwa gobe da safe" Khalil yace "Toh in sha Allah" Daga haka yayi ma Abba sallama ya mike ya fita, ɗan murmushi yayi kawai ya fice daga main parlor. Yana fita parlon Umma ta shigo da sallama, bayan ta zauna tace "Bako kayi ne halan" Abba ya girgiza kai yace "Ibrahim ne" Umma tace "Allah sarki, haka dai kawai ka hanani zuwa gun 'ya ta in dinga duba halin da take ciki, yau kusan sati biyu kenan rabona da ita, wallahi kullum da ita nake kwana nake tashi a raina, in ji dai suna lafiya?" Abba yace "Lafiya lau, zuwa yayi min da wani batu" Umma ta gyara zama tace "Wani batu kuma, to Allah ya sa dai lafiya" Abba yace "Lafiya lau, wai zai je noma garinsu xai tafi da ita" Umma ta zaro ido tace "Ya tafi da ita ina?? Yaushe Nihad xata wani iya zama a garinsu? To sai kace masa me Alhaji?" Abba yace "Toh ai a yanzu dai ya fi mu iko da ita, babu ta yanda xan iya hanasa tafiya da matarsa Sumayya" Umma na girgiza kai tace "Aa Yallabai wannan ba magana bace, to ko dai ka sallama ma duniya er nan ne bamu da masaniya? Duk wannan punishment din da kayi mata na aura mata dreba bai isheka ba sai ka ba dreba goyon bayan tafiya da ita kauyensu da sunan noma? Haba Alhaji ko ba kai ka haifi er nan ba kaddarar nan ya fada mata ai ka ji tausayinta ka raga mata balle er cikinka ce kuma masoyiyarka, ina laifin kace ya kawota nan gida ta zauna har sanda xai gama nomar tasa ya dawo daga kauyen nasu?" Abba yace "Aa, ai mu ba kananun mutane bane da zance ya bar ta gida Sumayya, tunda har ya girmama ni ya zo neman izinin tafiya da ita ni kuma baxan yi karanta ba a matsayina na mutum me kamala a gunsa, yanxu dai nace ya sa a bincika min fili a inda xa su zauna din, ko nawa ne xan siya, idan ya so ko 3 bedroom flat ne in sa a gina babu bata lkci, don yana min maganan sun samu gidan dubu dari, dama akwai gidan dubu dari a zamanin nan?" Shiru Umma tayi tana kallonsa babu ko kiftawa, Abba ya daga kai ya kalleta jin tayi shiru, tayi murmushi tace "Maa sha Allah, gida xaka gina ma Nihad din a can kenan?" Abba yace "Hakan xai fi gaskiya, idan ma babu wuta garin a saka masu solar 24/7, sannan ayi borehole a gidan, ayi furnishing yanda ya kamata" Umma ta gyara zama tana Murmushi tace "Hakan yayi kyau kam gaskiya, Allah ya saka maka da alkhairi ya kara budi, kaga zata zauna comfortably baxata takura ba, har ma ta sake a gidan ta ji kamar a cikin gari take" Abba yace "Yeah!! So i think duka duka da filin da ginin ai baxai ci miliyan goma ko sha biyu ba ko?" Umma tace "Ehh to, xai iya zama hakan tunda ai ba cikin gari bane kila, balle ace filin xai yi tsada sosai" Abba yace "In sha Allah, ko zuwa gobe aka samu filin xa a daura gini kawai" Umma na Murmushi tace "Madallah, Allah ya kai mu goben, bari in je in gama abinda nake a sama" Abba yace "Alright" mikewa tayi ta fita daga parlon. Yau ma kamar jiya ana kwankwasa gate Nihad da Khalil suka fito a tare, bai ko kalleta ba har ya fita, ta bi bayansa don wannan karan sai dai duk abinda xa ayi ayi a bakin gate din in dai Umma ce sai ta bude mata, Ya hade rai ya juya yana kallonta yace "Meye kike bi na?" Ita ma ta hade rai tace "Kayi tafiyarka inyi tawa mana" ya ci gaba da tafiya tana bin sa har suka iso gate din, yace "Wanene?" Husnah tace "Assalamu alaikum" Ya wani hade rai yace "Nace waye?" A hankali tace "Husnah ce" Nihad ta hade tafin hannunta kamar xata yi kuka tace "Don girman Allah kayi hakuri ka bude mata, ni kenan sai inyi ta zama babu wanda ke xuwa wajena kamar mayya,x kuma ai a sharadinmu nace baxa ka ki barin kawayena su zo wajena ba kuma ka yarda" Kallonta kawai yake, nan da nan hawaye ya cika idonta tace "Don Allah fa nace maka" Duk Husnah na jin su ita kanta addu'a take Allah ya ta6a zuciyar Khalil ya bude mata gate din, Juyawa khalil yayi ya bar wajen, Nihad ta wara ido cike da farin ciki ta bude gate din, tayi tsalle ta rungume Husnah tace "Wallahi nayi missing dinki kawata, ina su Naf da zully?" Husnah tace "Ba su ma san xan zo nan ba wallahi, tun shekaranjiya kike raina in gaya maki, shine kawai nayi tahowata ban gaya masu ba" Nihad ta kulle gate din tana Murmushin jin dadi ta kama hannun Husnah da ta bi khalil da kallo har ya shige parlor, suna isa balcony Husnah tayi kasa da murya tace "Amma dai kawai in gaida mutumin nan don gobe ma ya barni in shigo, kinsan abun sai da siyasa kawata, barin ma shi da yake ɗan kauye gaishesan da xanyi yanxu xa ki ga farin cikin da zai yi kansa yayi kato, kinsan bakauye akwai son girma" Nihad ta kyabe baki tace "Kar ki wani gaishesa, meye hadinki da shi ko ina ruwanki da shi bayan ba wajensa kika zo ba, ni kaina da nake gidan ban ta6a gaishesa ba saboda bai isa ba balle ke" Nihad na gama fadin haka ta ja hannun Husnah suka shiga parlon, Husnah na hada ido da shi ta janye hannunta daga na Nihad dake jan ta zuwa daki, ta dan yi murmushin yake tace "Ina wuninmu?" A fusace Nihad ta ja Husnah fuuu suka wuce daki ta kulle kofar tace "Amma ba nace kar ki gaishesa ba? Meye amfanin gaishesa yanzu?" Husnah ta yatsine fuska tace "Ni kaina wllh sai bayan da na gaishesa naga rashin dacewan hakan, baki ga ma wani shan kamshi da yake shi a dole ya aureki ba, yanzu fa ji yake shi wani shege ne ya auri er mai kudi" Nihad tace "Ke mu fa mun riga mun ajiye deal kan cewa xai sakeni, na amince shi ma kuma ya amince ya kuma yarda ni ba class dinsa bace" Husnah ta zaro ido tace "Haba??" Nihad tace "Wallahi in gaya maki, ai yaga tsanar da nake masa tayi yawa baxan kuma ta6a raga masa ba shi yasa yaga gwara mu rabu..." Husnah tace "Yanzu yaushe yace xai sake kin?" Nihad tace "Ku dai kawai ku zuba ido ku ga ikon Allah" Husnah tace "Kai amma na tayaki murna wallahi, ashe shegen ya san abinda yake yasan ke ba class dinsa bace cikin ruwan sanyi xai rabu da ke" Nihad ta tuntsire da dariya tace "Wallahi fa in gaya maki" Husnah ta cire Hijab din jikinta ta jefar kan gado, Nihad tace "Yaushe kika dinka hijab ke da baki da ko guda daya" Husnah tace "Wannan ma a hostel na aro shi, ke akwai abinci yunwa nake ji" Nihad tace "Ehh daxu nayi stew, kawai spaghetti xan yi boiling" Husnah tace "Toh bari in yi boiling dinsa, akwai a kitchen ai?" Nihad tace "Ehh akwai" Mikewa Husnah tayi ta bude handbag dinta ta fiddo after dress ta daura a kan riga da wandon jikinta ta fita, Nihad ta jawo jakarta bayan ta fita ta bude, as usual kayan maye iri iri ta ga a jakar da Prophylactics dinta, Nihad ta mayar mata da kayanta ta dau wayarta da ta gani ta bude password don tasan password din nata, har tayi dialing number Aliyu sai ta tuna ba shi da number Husnah don haka baxata samesa ba, lkci daya jikinta yayi sanyi, sai dai kawai tayi dialing number Umma, Umma na jin muryata tace "Daughter, ina ta tunanin ta yanda xanyi waya dake tun
Chapter 109 · 0% Book details