Sashe 68
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
fito daga dakinta, dai dai nan Khalil ma ya fito... sosai gabanta ya fadi ta ɗan koma baya, sai kuma ta daure fuska, ko kallonta bai yi ba ya shiga parlor, ta bi sa da kallo taga kamar fita zai yi, tuni turarensa ya gauraye duk parlon, ko burgeta kamshin nan nasa baya yi, ta kasa kunne taji ko fita gate xai yi, ai ko taji ya bude gate, da sauri ta shige dakinsa ta kulle kofar, banda kamshi babu abinda dakin ma yake, ta tafi gefen gado ta dau karamar wayarsa da ta gani ta hau dialing din number Umma sharp sharp, yana fara ringing Umma ta daga hade da sallama, Nihad ta marairaice tace "Umma ni ce" Umma tace "Aa Nihad, Number waye haka duk zero zalla" Nihad tace "Wayar yaron nan ne Umma, ya fita yanxu shine na dauka da sauri na kiraki kafin ya dawo" Umma tace "Kin ji shiru ko, wllh ba a samu anyi rijistan layin yau ba sai gobe wai, don haka gobe da kaina xanje ayi, ita kuma Amina tana dawowa islamiyya xan bata ta kawo maki kin ji" Nihad tace "Toh shkkn Umma, Allah ya kai mu goben" Umma tace "Toh Ameen, sai da safe daughter" Daga haka ta katse wayar, Nihad na duba call logs don ta kira Husnah tunda daxu ta saka numberta a wayar amma bata gani ba alamar ya goge number, instead sai number Nihal ta gani wanda ko awa daya ba ayi ba da suka yi wayan da ita, ta dinga kallon number babu kiftawa, bude kofar dakin aka yi, Nihad ta zaro ido hade da kurma ihu a tsorace ta saki wayar hannunta jikinta na rawa, tsaye yayi bakin kofa yana kallonta da wani Strict expression, lkci daya ta wani sha kunu ita ma, can dai ta tafi can jikin bango har sannan gabanta na faduwa amma bata nuna hakan a fuskarta ba, ya karaso cikin dakin ta hadiye wani abu da ya tokareta a makogwaro da kyar xuciyarta sai bugawa yake tana kara shigewa jikin bango, yana dukawa zai dau wayar ta yi hanyar kofa a mugun guje, da hannu daya yayi hanzarin fixgota ta fasa ihu tana kokarin kwace kanta tace "Wallahi xan cijeka idan baka sakeni ba, ni me xanyi da gwangwanin wayarka"