← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 165

Sashe 90

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ko mu tace kar mu yi magana, baka ga inda taje tayi parking motar ba don kar ya gani" Khalil dai bai ce komai ba, amma Mumy da aka ce bata da lafiya ce ta tsaya masa a rai, Aminu ya tuntsire da dariya yace "Yanxu don Allah yaya zaman naku da yarinyar nan, ni fa na dauka xa ace ta kashe kanta da taga Alhaji ya aura maka ita, kiyayya ce fa ta gaske take maka" Khalil yace "Ni ban kashe kaina ba sai ita xata kashe kanta?" Dariya sosai Aminu yake yace "Gaskiya kam kai aka cuta, anyi mugun kwararka mutumina, yanxu fa har yara da jikoki sai sun ga wannan videon nata da yayi yawo a yanar gizo, tabo ne da baxai ta6a goguwa ba har karshen rayuwarta, kai don ma dai iyayenka ba yan boko bane basa hawa yanar gizo, ai da wallahi baxa su amince ka auri yarinyar nan ba, ko kai baka kare ma videon kallo bane? Saminu fa har jawo mana shi yayi kusa kusa yanda xa mu gani da kyau, ita wannan ba ma wani amfani ta sake yawo da kaya a jikinta bayan duk duniya sun san surarta" Lkci daya mood din khalil ya sauya, Aminu ya girgiza kai yace "Tirr, amma a gaskiya hada zuri'a da wannan yarinyar ma bala'i ne, banda kana jin nauyin ubanta me xai kai ka? Kai da kake da mutunci haka, Sauran titi ce fa, duk ta yasar da darajan nata ta rarrabar a titi, nan nan nan ranan ni da kai muka ganta da asuba ta dawo daga sheka ayarta tana ta rabe rabe bakin gate, kuma ta sha yin hakan tun ma baka xo gidan nan ba ya fi a kirga, labarinta ma ai sai a bakin Habibu, nasan bai san da wannan hadin ba da ya zuga ka yace kar ka yarda komin me ubanta xai ce maka, shi ma dai Alhajin ya so kansa da yawa, bai kuma yi maka adalci ba, ya rasa warce xai aura mata sai Nihad bayan ga salihar er uwarta Nihal, lalatacciya ce fa babu wanda bai sani ba, ni wallahi da kudi ma baxan amince in aureta ba balle kyauta...." Mikewa Khalil yyi ya nufi cikin gidan, Aminu yace "Auu har mun gama hirar? Ko xaka shiga ka fito?" Khalil na isa balcony ya kira Abba ya sanar masa yana gidan, Abba yace ya basa few minutes yana da baki, Khalil ya amsa masa da to sannan ya xauna saman kujeran dake wajen, har wani sarawa yaji kansa ke yi da maganganun Aminu, yana ta xaune balcony din sai ga Aunty Jamila ta fito xata kwaso kayan shanya da tayi a baya, mikewa yayi , ganinsa tace "Aa kai ne a nan..." Gaisheta yayi, ta amsa tace "Ya gida?" Yace "Alhamdulillah" Tace "Toh ka shiga ciki mana" kawai murmushi yayi bai ce komai ba, tace "Ka karasa Sudais ya kai ka ka duba Mumy kasan bata ji dadi ba" yace "Subhanallah, amma da sauki ko?" Tace "Alhmdlh" yace "Toh Allah ya bata lafiya" Tace "Ameen" tana barin wajen ya shiga parlon kansa a kasa, Sudais na ganinsa ya taho da gudu ya rungumesa yace "Uncle mun daina ganinka" Ya shafa kansa yace "Gani na zo ai, ina fadil?" Yace "Yana wajen Mumynmu bata da lafiya" Khalil yace "Toh kai ni in gaisheta" Har part din Mumy Sudais ya kai sa, yayi sallama bakin kofar parlon, Wata frnd din Mumy ta amsa, shiga parlon yayi kansa a kasa ya nemi saman carpet ya xauna ya gaishesu, duk suka amsa, Mumy dake xaune parlon an cire mata last drip dai kallonsa kawai take, Bayan few seconds ya daga kai ya kalleta yace "Ya jikin Mumy?" Cikin sanyin murya tace "Alhamdulillah Ibrahim, ya gida?" Ya sauke kansa yace "Lafiya lau, Allah Ubangiji ya kara Lafiya" Tace "Ameen Nagode" Bai kuma cewa komai ba, Hajiya Zara ta mike ta fita daga parlon, bayan few minutes Mumy tace "Kayi hakuri Ibrahim, an cuceka an hadaka aure da warce bata cacanceka ba, nasan baka da yanda xaka yi ne kuma baxa ka iya k'in amsan tayinta da mahaifinta yayi maka ba...." Da sauri yace "Aa Mumy, Allah ne ya tsara haka, kuma muna fatan Allahn yasa hakan shine mafi alkhairi" Hawaye na sauka idon Mumy tace "Ni kam bani da abinda xan ce maka sai dai in baka hakuri akan abinda Alhaji ya maka, sannan ni baxan ce kayi hakuri da Nihad ba, idan kaga baxa ka iya ba ko xaka cutu ina me goya maka bayan ka saketa kawai ta dawo gida...." Cike da karfin hali Khalil yace "In sha Allah baxa ayi haka ba Mumy" Mumy ta share idonta bata kuma cewa komai ba, Wani duniyar tunani khalil ya fada gaba daya jikinsa yayi sanyi, he couldn't even think straight, kiran sallahn magrib da ake ne yasa ya dago kai ya kalli Mumy ya ga kallonsa take, a hankali yace "Xan je masallaci Mumy, Allah ya kara lafiya" Tace "Ameen Ibrahim nagode" Tashi yayi a hankali ya fita daga parlon, Umma ya tarar a main parlor ta masa wani kallo sai kuma ta ja tsaki tayi hanyar kitchen, ya bi ta da ido kawai. Bayan an idar da sallan magrib tare suka shigo gidan da Abba har xuwa parlonsa, Khalil ya xauna ya gaida Abba da ladabi, Abba ya amsa yace "Ya gidan?" Yace "Alhamdulillah" Abba yace "Ya kamata xuwa gobe ku shirya ka tafi da ita can garinku ta gaida iyayenka, bayan kwana biyu sai ku dawo" Khalil ya ɗan yi jim, sai kuma ya dago ya kalli Abba yace "Toh in sha Allah Alhaji, Allah ya kai mu goben" Abba yace "Ameen, farooq ya zo min da wani batu jiya amma sai kun dawo dai" Khalil yace "Toh Alhaji, nagode" Abba ya ciro dubu dari ya mika masa yace "Ka yi full tank, sannan kayi ma iyayenka tsaraba da sauran" Khalil ya sa hannu biyu ya amsa yace "Toh Allah ya saka da alkhairi Alhaji" Abba yace "Ameen, Allah ya maka albarka" Khalil ya amsa da "Ameen" a tare suka fito main parlor da Abba, Umma ta fito daga kitchen kenan ganinsa da Abba tace "Aa Ibrahim har xa ka tafi, bari to ga abinci ka kai ma Nihad tunda an gama" Ya kalleta yace "Toh" Komawa kitchen tayi da sauri, Abba dai ya zauna parlon har sannan kana ganinsa xaka san yana cikin damuwa, dake xuciyarsa kawai yake yana ma Nihad wasu abubuwan as form of punishment amma shi yasan sonta a jininsa yake, but he can't help it, tayi disappointing dinsa sannan ta xubar masa da mutunci a idon duniya, Umma ta cika warmer da abinci, sannan ga wani warmer din daban na kaza ta fito parlor, sai da ta bubbude warmer din tana kallon khalil cike da damuwa tace "Don Allah idan ka je ka lallabata ta ci abincin nan, duk ta rame ta lalace wallahi, Shekaranjiya da naje ma da ya na samu ta ci abincin, yanxu kam ban san halin da take ciki ba baiwar Allah, wa yasani ma ko bata cin komai" Shi dai Abba bai ce komai ba, khalil kuwa banda kallonta babu abinda yake, Abba ya mike yace "Ka jirani Ibrahim" Khalil yace "Toh Abba" Ba a dau lkci ba sai ga shi ya dawo da dubu talatin ya mika ma Khalil yace "Ka siya mata carton din maltina da na madaran gwangwani" Ta gefen ido Umma ke ta kallon Abba, Khalil ya amsa yace "Toh In sha Allah Abba" Abba yace "Sai da safe, Allah ya tsare" Juyawa Umma tayi ta shige kitchen ta tsaya jikin cabinet kamar me nazari. Khalil na isa gida sai da yayi isha a masallacin dake layin sannan ya shiga gida da motar yayi parking, bayan ya kulle gate din ya dawo ya fiddo abincin daga cikin mota ya kai parlor ya sake fitowa ya kai maltina da madara parlon ya ajiye sannan ya kulle gidan, xaunawa yayi saman kujera ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido, da yasan haka abubuwa xa su kasance masa da bai yarda ya fara shigowa garin kano ba, where will he even start this amendment from?? Babu warce ta tsaya masa a rai sai Mahaifiyarsa, this seriously isn't going to be easy, Mikewa yayi daga karshe ya nufi dakinsa yana tafiya a hankali, har ya bude kofar sai kuma ya fasa shiga, ya dawo ya bude dakinta, zaune ya ganta a kasa idonta yayi bulu bulu alamar tayi kukan gaske yau, ya tabe baki ya kulle kofar ya koma parlor kawai yayi xamansa, tashi Nihad tayi ta bi bayansa, ta tsaya bayan kujera tana shesshekar kuka..., ya ɗan daga kai ya kalleta kamar bazai ce komai ba sai kuma yace "Da bashi ne?" Wani bakin ciki ya rufeta a fusace tace "Ban sani ba, ka zata kai ka isa ka dinga punishing dina? Waya biyu aka kawo min gidan nan ka salwantar min da su, toh wallahi zaka sha mamakin abinda xai faru idan baka bani wayata ba" Mikewa yayi ya bar mata parlon ya shige dakinsa ya kulle, kuka kawai take kamar ranta xai fita, babban tashin hankalinta shine Aliyu da xai yi ta kiranta ya ji a kashe, yanxu babu ta inda xata yi ta iya kiransa, da ma baya kulle gate ne ko makota ita sai ta shiga don ta kira Aliyu, amma ko daxu da xai fita kulleta yayi ta ciki, ko bin ta kan warmers din abincin dake parlon bata yi ba ta koma daki ta dinga kuka kamar ranta zai fita, har kusan karfe biyun dare Nihad bata yi bacci ba, abun duniya ya taru yayi mata yawa, last week fa warhaka tana baccinta peacefully a saman gadonta, tashi tayi a hankali ta goge idonta ta nufi kofa, a hankali ta bude kofar dakin nata ta fito, taga ya kashe duk wutan gidan, ko ina yayi duhu, tana lalubawa ta tafi hanyar dakinsa ta kai hannu handle din kofar ta murda a hankali ta bude ta shiga dakin, nan ma dai ya kashe fitilar, sai da ta fara tattaba socket din dakin cikin duhun ko xata ga karamar wayarsa a jiki taga babu, cikin sanda ta nufi gadon dakin
Chapter 90 · 0% Book details