Sashe 132
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
taga Nihad a tsaye bakin kofa tana shesshekan kuka, tun bayan da taga khaleel ya mata wannan kallon sannan ga shiga kofar ya kulle tayi saurin komawa bakin kofar fita parlon ta tsaya zuciyarta na raya mata shikenan babu wani tantama ya kawota ne kawai a gille mata kai ayi kudi da ita, dama masu kudin nan wasun su kowa yasan ai suna yankan kai, to kila mai gidan ya ba khaleel contract din samo masa kan da za a gille shi yasa har ya shigo gidan tare da ita babu wanda ya hanasa, sai ma bude masa kofa da securities din suka yi har da masu gaishesa, irin dai ya saba shigowa gidan kenan, sannan gashi taga kansa tsaye ya taho bangaren nan da ita, wato in da za a gille mata kan kenan, uwa uba tun da suka shigo gidan bata ga ko wani mutumin ba sai securities, Da mamaki Mami ke kallon Nihad ganin yanda take hawaye tace "Subhanallah, Baby are you okay? why are you crying?" Kallon matar kawai Nihad take hawaye na sauka idonta kuma taki ce mata komai, wannan ba ita ce ta gani a hoto ranan a dakinsa ba? Mami tace "C'mon, come in dear...." Nihad taki karasowa sai kallonta take, Mami na ganin haka ta juya ta koma dakinta ta shiga tana kallon Khalil dake kwance saman gadonta da mamaki tace "Khaleel na ganta tsaye bakin kofa tana kuka, is she okay? Nace ta shigo kuma ta ki" Mikewa Khalil yayi ya fita parlon Mami ta bi bayansa, yana kallon Nihad, ya dake yace "Shigo ciki" Mami ta karasa inda take tsaye ta kamo hannunta ta shigo da ita parlon tana kallon Khalil murya can kasa tace "Doesn't she understands English?" Bai ce komai ba ya juya ya koma dakin, Mami ta zauna gefen Nihad da ta zaunar edge din kujera kamar me shirin fillawa da gudu, tace "Ya kike yan mata?" Nihad ta goge idonta tana kallonta a hankali tace "Ina yini" Mami na Murmushi tace "Alhamdulillah, ya su mamanki?" Nihad ta sauke idonta kasa cikin sanyi tace "Lafiya lau" Haka kawai Nihad taji hankalinta ya ɗan kwanta ganin Mami, Mami ta kwantar da murya tace "Ki saki jikinki kinji, nan ma duk gida ne" Nihad ta kasa ce mata komai, Mami tace "Kin yi sallan magariba?" Nihad ta girgiza mata kai, Mami tace "To ga banɗaki kije kiyi alwala, bari in kawo maki darduma a bedroom yanzu" Nihad ta mike ta tafi kofar da Mami ta nuna mata a parlon ta bude a hankali tana kallon ciki, bandakin ya kusa girman dakinta, ta karanto addu'ar shiga banɗaki a ranta sannan ta shiga, Mami ta mike ta tafi daki ta ga Khalil ya dauro alwala ya fito, area din da Mami tayi demarcating a dakin don yin sallah ya nufa, Mami ta dau ma Nihad darduma daya ta kai parlor ta shimfida mata, sannan ta koma dakin ta shiga bandaki ita ma ta dauro alwalan, Khalil na zaune saman darduma yana azkar bayan ya idar da sallah, Mami ta mike bayan ita ma ta idar tana kallon side din da yake tace "Yanzu abincin xan dauka in kai can parlon, ko ta shigo nan kawai ku ci?" Yace "Ki deba kawai ki kai mata can parlon Mami" Mami tace "Ai ban san abinda tafi son ci ba, kawai bari ta shigo ta yi serving kanta ko?" Mami na fadan haka ta fita zuwa parlor tana kallon Nihad dake saman darduma tayi kuri da ido tace "Baby shigo ki ci abinci" Nihad ta mike a hankali ta tafi kofar dakin ganin taki shigowa Mami tace "Shigo mana" Cikin sanyin murya tayi sallama ta shiga dakin, ta dinga bin abincin dake jibge a kasa da kallo kamar za ayi party, Mami tace "Ki duba duk abinda kike so ki diba" Mami na fadan haka ta fita daga dakin, Nihad ta durkusa tana kallon Khalil, murya can kasa tace "Don Allah ina ne nan ka kawo ni?" Sai a sannan Khalil ya kalleta tun da ta shigo dakin yace "Inda za a mana alfarma ba tare da an walakanta mu ko an ci zarafinmu ba, ba kuma tare da an damu da mu talaka ne ko masu arziki ba" Shiru tayi tana kallonsa, ya mike ya zauna gefen gadon yace "Debi abinda zaki deba ki fita" Ita dai ta kasa cewa komai kuma ta kasa bude ko warmer daya balle ta zuba abincin, Mami ta dawo dakin rike da teapot da cups dinsa biyu a tray, da mamaki ta ke kallon Nihad bayan ta ajiye tray din hannunta tace "Baki debi abincin ba" Sai kuma ta kalli khalil kafin tace komai ya kirkiri murmushi yace "Haka take Mami" Nihad ta daga kai ta kallesa, Mami tace "But why? pls tell her to feel free" Khalil ya maida idonsa kan tv dake aiki silently bai ce komai ba, Mami ta dau plate ta debar ma Nihad shinkafa da miya ta ajiye mata, ta debar mata duk wani abu da xata dibar mata sannan ta mike, Nihad dai bata ta6a jin she is confuse kamar yanda take ji yanzu ba, gaba daga kanta ya kulle ta kasa fahimtar komai, lkci lkci sai ta kalli khalil sannan ta kalli Mami, Mami na kallon Khalil a hankali bayan ta gama zuba ma Nihad abinci tace "When did you say he called you?" Khalil ya kalleta duk da ya gane wanda take nufi yace "Ke baxa ki ci abincin ba Mami? Ki zuba mana tare mu ci" Mami tace "Talk to me son, he is back now" Sai da gaban khalil ya fadi ya mike yace "Really? But hope you didn't...." Sai kuma yayi shiru, ta gefen ido ya kalli Nihad da ta kafesa da ido babu ko kiftawa, sai kuma ya fice daga dakin, Mami na kallon Nihad da murmushi fuskarta tace "Ki ci abinci kin ji Baby" Daga haka ta juya ta bi bayansa, Nihad ta bi su da kallo bata kwakkwaran numfashi, bayan kusan minti sha biyar Khalil ya dawo dakin shi kadai, har sannan Nihad na zaune position din da take kamar warce ruwa ya cinye, gaba daya jikinta yayi sanyi qlau kana mata kallo daya zaka gane hakan, Ta bi sa da kallo har ya dau teapot da cup zai fita, cikin sanyin murya tace "Ka gaya min, wanene kai?" Bai yarda ya kalleta ba yace "Driver!!" Daga haka ya fice daga dakin, ta bi sa da ido babu ko kiftawa, abinda ya fada dazu da turanci ne ke kai komo a ƙwaƙwalwarta, lokaci daya ta runtse ido ko zata samu saukin sara mata da kanta ke yi. Khalil na zaune parlor sai ga Mami ta shigo tana kallonsa, shi ma kallonta yake, a hankali tace "Kaje wajen Abbanka, yana kiranka parlonsa" Khalil ya kalleta looking so worried yace "Mami da baki ce masa na dawo yau ba" Mami ta girgiza kai tace "I never told him, tun daga gate ya tambaya securities, su suka sanar masa kana gidan nan....." Yayi kasa da murya yace "But bana son kowa ya san am around Mami" Mami tace "Zaka iya zagawa ta baya ai, har yanzu babu wanda yasan kana gidan nan" Mikewa yayi ya nufi kofa yana tafiya a hankali ta bi sa da kallo har ya fita.