Sashe 75
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read
tace "Shi ne ai nake kallon ikon Allah" Naf ta kalli Amina tace "Ke tafi ki karbo mana makulli wajensa tunda ba shi da hankali, uban wa zai bari tsaye cikin rana" Amina ta tafi a gun motar yana ganinta ya sauke glass din can side din don duk sun gwala ido su ga ya sauke glass din side dinsa ko xa su samu a little glimpse of him, Amina na ganin haka ta zaga tana kallonsa ta cikin motar tace "Ka bamu makullin gidan" Yace "Su waye bakin gate din?" Amina tace "Kawayen Aunty Nihad" Yace "Ohk, ke kika kawo su kenan?" Tace "Ehh Umma ta bani sako in kawo mata ne shine muka taho tare da su don basu san gidan ba" Ya mika hannu yace "Toh kawo a ajiye mata sakon, yanxu kasuwa xanje in yanko wani makullin wancan ya fadi" Amina tayi kasake tana kallonsa, mika hannu yayi ya amshe ledan hannunta yace "Ko xaki shigo in ajiye ki gida daga nan in wuce kasuwar?" Amina ta daure fuska tace "Ni ai a motarsu muka zo" Yace "Toh koma motar tasu" Daga haka ya ja glass ya tada motar yayi reverse ya bar layin.....