← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 165

Sashe 53

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

cire kudi ba" Ta ta6e baki tace "Okay" Juyawa tayi ta koma ciki, tun jiya take avoiding ya farooq wannan ne ma yasa ta ki zama a parlor, ta koma dakinta tana jin dawowar Khalil ta sauko kasa da sauri, hade rai tayi ganin Ya Farooq a parlor ta gaishesa tayi ficewarta ba tare da ta jira ya amsa ba, Direct wajen khalil ta nufa babu yabo babu fallasa tace "Ehm ya ma ake kiranka? Abbana yace ka bada account number" Khalil ya kalli Aminu kamar dai yana jiran Aminu ya bata amsa, a fusace tace "Malam ai ba Aminu xaka kalla ba, da kai nake ni xaka kalla" Ya kalleta yace "Ohk, bani da account" Ta masa wani kallo tace "I thought as much" sai kuma ta ja tsaki ta juya ta koma ciki, Aminu yayi kasa da murya yace "Alhaji fa ya tambayi account din naka kasan ko ihisani xai maka" Khalil ya girgiza kai yace "To ai bani da account din ne" Aminu yace "Kashh" Nihad ta daidaici lkcn fitan Abbanta ta fito parlor da sauri yana ganinta yace "Yauwa kin amso account din" Tace "Abba bashi da shi, kawai ka sa a na kawata Husnah ita ta ma san wajen gyaran don nata ma ya ta6a lalacewa kamar nawa, don haka ita xata raka mu" Yace "Okay, forward the account to me via Sms" Tace "Toh Abba nagode, Allah ya kara budi" Yace "Ameen" Daga haka ya fita parlon Mumy tayi masa Allah ya tsare, Umma na tsaye bakin kofar kitchen tana kallonsu, Bayan fitan Abba Nihad ta juya da sauri xata bar wajen Mumy tace "Zo nan me xa a gyara?" Tace "Mumy laptop dina ne yake bani matsala shine xai tura min kudin gyara" Mumy tace "Toh amma lallai sai an sa kudi account din Husnah? Me yasa baxa ki je ki gyara account dinki ba, kuma nace maki bana son alakar ku da yarinyar nan kin ki ji, wai sai na fara nakada maki duka a gidan nan xaki nutsu Nihad?" Nihad ta marairaice tace "Mumy Coursemate dita ce fa, dole muna haduwa a class ko ban kulata ba ita tana kulani kuma ita kadai tasan inda ake gyara laptop din nan tunda nata ma ya ta6a lalacewa" Farooq yace "Dauko laptop din naki da ya lalace ki kawo min" Juyawa tayi ta kallesa, Umma ta karaso parlon tace "A saboda ka fara gyaran laptop??" Mumy tace "Ta dai je ta dauko masa laptop din da ya lalace" Umma tace "Toh naga ai ba shi ya bada kudin gyaran ba da xai hau tuhumarta" sum sum Nihad ta wuce sama, cikin lkci kankani ta shirya ta dau jakar laptop dinta ta fito, Umma kadae taje tayi ma sallama Umma tace "Toh Allah ya tsare daughter" Aminu ya kalli Khalil bayan ta fita yace "Kai fa yanxu huta roro, adaidaita take hawa xuwa duk inda xa ta." Nihad bata dawo gida ranan ba sai da sabon Iphone dinta dal a kwali, babu wanda ta sanar ma ta canza waya banda Nihal da Umma, Umma na jujjuya wayar tace "Gaskiya ne er daddy, yanxu duk kawayen naki su ma irin wannan ke hannunsu kenan?" Nihad ta washe fararen hakoranta tace "Ehh wllh Umma, shi yasa nima na dage sai da na canza, ai abun kunya ce ace ni kadai ce ban canxa waya ba a cikinsu" Umma tace "Ai ko kina da gaskiya abun ki" Nihad tace "Umma kinsan me?" Umma tace "Aa sai kin fada" Nihad tace "Umma xa mu fara exams nan da kamar sati uku kuma wllh ina son in koma hostel don in dinga karatu sosai, nasan Mumy da Ya farooq xa su xuga Abba kuma baxai bari in koma ba, pls ko xaki taya ni convincing Abbana?" Umma tace "Gaskiya ya kamata ki koma hostel din don ki maida hankali kiyi karatu sosai, amma kinsan me xai faru?" Nihad tace "Aa" Umma tace "Zan ce ma Abbanku Mijin Kamila xai yi tafiya kasar waje kuma xai yi kusan wata biyu a can, tace ki je ki dinga tayata kwana idan ya so daga can sai ki dinga xuwa makaranta, ita ma Kamilan xan sa ta kira Abban naku" Nihad ta wara ido cike da farin ciki tace "Yauwa Ummana, wannan shawarar taki tayi wllh" Umma tace "Kinga kawai daga nan sai kiyi komawarki hostel har sanda xa ku gama jarabawan, babu wanda xai san baki gidan Kamila" Nihad tace "Ai kuwa Umma, don Allah gobe da safe kiyi ma Abba maganar da wuri, on Thursday ma nake son in koma ni dai" Umma tace "Toh shikenan, Allah ya kai mu goben, ai gobe Wednesday" Nihad ta fita dakin cike da farin ciki, shi yasa take son Umma, haba she will be free for a while, babu me takurata. Da safe babu wani bata lkci Umma tayi convincing Abba, yace "Toh Allah ya kai mu alhamis din" Umma tayi murmushi tace "Ameen Yallabai, sai kayi ma Maryam magana da kanka ko?" Yace "Aa kema xa ki iya yi mata ai, menene a ciki" Umma tace "Aa gwara dai kai kayi mata, kace mata Kamila ce ta roki alfarman Nihad ta koma wajenta na kwana biyu mijinta xai yi tafiya" Abba yace "Ohk, amma suna da driver ne a can da xai dinga dropping dinta school?" Umma tace "Anya, da yake kasan shi yake ajiye kamilan duk inda xata je" Abba yace "Toh duk safiya sai Ibrahim ya dinga xuwa can yana daukarta ya ajiye ta makaranta, when ever her lectures is terminating sai ta gaya masa yaje ya dauketa ya maida ta gida" Umma tace "Hakan ma yayi kam" kafin Abba ya fita aiki ya shiga bangaren Mumy, nan ya sanar mata abinda Umma tace masa, Mumy tayi shiru alamar ta ma rasa abinda xata ce, Abba yace "Sai ki gaya ma Nihad din ta fara shiri" Mumy ta sauke boyayyen ajiyar xuciya tace "Alhaji idan Nihad taje gidan Kamila babu me kwaba mata, kasan ta da rawan kai fa, tana nan gida ma ya aka karke balle bata gida" Abba yace "So what are u insinuating?" Mumy ta girgiza masa kai kawai, Abba yace "Kar taje ta taya er uwartata xama kenan?" Mumy tace "Ko daya ba haka nake nufi ba" Abba yace "Toh Maa sha Allah, gobe alhamis ta shirya ta koma can gidan" Daga haka ya fice daga parlon, har ran Mumy bata son xuwan Nihad gidan Kamila amma to ya xata yi? Hakan ya sa ta tunani iri iri.
Chapter 53 · 0% Book details