← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 165

Sashe 98

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

saman gadon karan tana juye juye, daga karshe ta mike ta sauko kasa jikinta na rawa ta bude farau faron dake kulle ta dauka, runtse ido tayi cike da karfin hali ta kai bakinta kan kwanon ta rike breathing dinta sannan ta hau kwankwada, ajiye kwanon tayi da sauri bayan ta kwankwadi kusan rabi, saboda wani amai da taji ya taho mata, ta mike da gudu ta fita daga dakin, gwaggo da matan tsakar gidan dake surfe suka taso da sauri suna tambayarta lafiya, nan ta dinga kwararar masu aman abinda ta sha kamar xata shide, Gwaggo da duk ta rude tace "Subhanallahi, me ya sameki, gashi baya nan" Wata mata ta kawo ruwa da sauri suka ba Nihad dake maida numfashi, amsan ruwan tayi da kyar ta wanke bakinta duk jikinta na rawa, Gwaggo da hankalinta yayi mugun tashi ta kawo mata kujerar tsugunno tace "Hannu, zauna nan, zauna" Nihad ta xauna a hankali kan kujeran tana maida numfashi, Gwaggwo tace "Me ya sameki kike hararwa haka?" Da kyar tace "Bani da lafiya ne dama" Matan gidan suka dinga yi mata sannu, ganin yanda jikinta ke rawa Gwaggo ta maida ta cikin Bukkar tana mata sannu ba adadi, wata yarinya da ta aika ta dubo mata Khalil a waje ta dawo ta shigo Bukkar tace "Gwaggo bamu gansa ba" Gwaggo tace "Toh bari a mata jike jike tasha ko xaxxabin xai sauka" Daga haka Gwaggo ta fita, kuka Nihad take a hankali tana juye juye tana jin kamar kanta xai fashe don ciwo, bayan wani lokaci sai ga gwaggwo da kwano ta ajiye kasa ta dago Nihad tace "Ga nan jike jiken sassaken itatuwa na maki, tashi ki sha, ba daci ba bauri, ba hamami" Nihad ta mike tana rawan sanyi Gwaggwo ta dauko kwanon ta kai mata baki tace "Ungo sha" Cike da karfin hali Nihad dake ta kallon cikin kwanon ta kurbi ruwan ciki, Gwaggo tace "Kara sha" Nihad ta runtse ido ta kara kurba ta hadiye tsikar jikinta na tashi, dacin ruwan kuwa ba a cewa komai, Gwaggo tace "Yauwa, to koma ki kwanta yanxun nan xaki fara xufa, su ararrabi ne da sabara da tazargade, ga su nan dai" Nihad ta koma ta kwanta Gwaggwo na kokarin lullubeta Khalil ya shigo Bukkar ya nufo Nihad yana kallonta, Gwaggwo tace "Wallahi mugun zazzaɓi ne ya rufeta yanxun nan sai hararwa take" Khalil ya duka yana kallonta ya kai hannu jikinta wanda yayi zafi kamar wuta, cike da damuwa Gwaggwo tace "Akwai wani karamin asibiti a gidan Darho, kauyen da xaka wuto kafin ka zo wannan, ko xaka kai ta a dubata a bata magani ɗan nan?" Khalil yace "Toh xa mu je can" juyawa tayi ta fita daga Bukkar, Hannu ya kai goshinta duk da idonta a kulle yake yace "Ina ke maki ciwo" Ta fashe da kuka ta tura hannunsa daga goshinta tace "Ni ka maida ni gidanmu, idan ba haka ba sai Allah ya kama ka" kallonta ya tsaya yi, can ya gyada kai ya koma gefe yace "Ohkk" tayi karfin halin mikewa cikin kuka ta kamo hannunsa tace "Don Allah kayi hakuri ba don halina ba ka maida ni gida" Yace "Toh ina ke maki ciwo?" Tana shessheka tace "Kai na, kuma ina jin yunwa" Ya mike yace "Sakko" Da sauri ta mike xaune amma ta kasa tashi daga saman gadon duk yana kallonta, ya mika mata hannunsa ta rike sannan ta mike tsaye a hankali, dukawa tayi yana rike da hannunta ta dau Hijab jikinta na rawa ta saka, sannan ta dau handbag dinta, ko bin ta kan atamfarta na karshe da kayan shafe shafenta bata yi ba, a haka suka fita daga Bukkar, Gwaggwo da matan gidan suka taso, ana mata sannu in chorus, Gwaggwo tace "Can asibitin ku ka nufa ko?" Yace "Ehh" Nan dai aka dinga mata Allah ya sauwake, Fure dake tsaye kusa da wani ɗan mariki da aka daure tace "Gwaggwo in rakasu asibitin" Da sauri Nihad ta kalleta, murya can kasa Nihad ke girgiza ma Khalil kai tana cewa "Aa baxa mu je da ita ba" Ya ɗan kalleta ta gefen ido, Gwaggwo tace "Toh ko kama maka ita ai sai fure ta dinga yi a asibitin ko" Da sauri Nihad na Murmushi tace "Aa mama xan iya ai" Gwaggwo tace "Toh shkkn, Allah ya baki lafiya sai kun dawo" Nihad dai bata ce komai ba a ranta kuwa tunani take ina din xa su dawo da take ce masu sai sun dawo? Dalilin ma da yasa bata son Fure ta bi su kenan don in sun tafi da ita ai dole su dawo da ita kauyen, ita kuwa bata fatan abinda xai sake dawowa da ita kauyen nan, suna isa inda Khalil ya ajiye mota ya saketa ya zaga daya side din, a hankali ta bude front seat din ta shiga, bayan yayi warming motar ya ja motar, matan gidan da suka taru bakin kofar shiga gidan har da masu daurin kirji, ga yaransu duk ba wando a tsattsaye su ma, sai daga masu hannu suke kana ganinsu dai kaga yan kauyen kayau, haka ma sauran makota da suka fiffito jin karar mota, Nihad ta sauke wani ajiyar xuciya, at long last!!! har taji xaxxabin ya tafi sai kuma bakar yunwan da take ji, tafiyar minti talatin suka yi ta ga alamar sun fara shigowa gari, farin ciki gunta ba a cewa komai, bata ta6a tunanin xata fito daga kauyen can da ranta ba, ta zata sai buzunta, so truly akwai mutane irin haka a rayuwar nan, akwai mutane dake rayuwarsu cikin kauye haka? lkci daya jikinta yayi sanyi, and they are leaving happily abunsu babu wani damuwa, ko pole din wuta ita bata gani a garin ba balle a je ga an ja masu wuta, parking ta ga khalil yayi dai dai wani pharmacy, duk da bata san inda suke ba amma tasan sun shigo cikin gari gaba daya, ya kashe motar ya sauka yana kallonta yace "Sauko malama" A hankali ta bude motar ta sauko ta bi bayansa tana jan kafa saboda jiri da take gani, suka shiga pharmacy din, bayan sun gaisa da me Pharmacy din ya koma gefe ya tsaya yana kallon Nihad da ta jingina da kofar pharmacy din bata shigo ba, har ta rame tayi wani uban duhu kamar ba Nihad ba, Ya kalli me Pharmacy din yace "Ita ce bata da lafiya" Me Pharmacy din yace "Sannu Hajiya karaso" Tana jan kafa ta tafi gaban table dinsa ta xauna, Tunda aka haifeta ba a taba kawo su pharmacy idan basu da lafiya ba, sai dai asibiti, amma wai yau ita ce a pharmacy xa a mata treatment bata da lafiya instead of hospital, muryar Pharmacist din ne ya dawo da ita duniyar tunanin da ta tafi, ta sauke idonta kasa a hankali tace "Zazzaɓi nake ji da ciwon kai" Yace "Kina amai ne?" Ta gyada masa kai tace "Ehh nayi daxu" Yace "Ohk" Kallon khalil yayi yace "Xa a maganunguna da allurai...." Khalil ya rungume hannunsa yace "Sai dai magungunan kadai, don kauyen da muke akwai nisa, baxai yiwu mu dinga xuwa muna komawa ba kullum" Da mugun shock Nihad ta kallesa, bata san sanda ta fashe da matsanancin kuka tace "Don girman Allah ka rufa min asiri kar ka maida ni garin nan" Khalil ya danne dariyarsa ya hade rai, Me Pharmacy ya tuntsire da dariya yana kallon Nihad da duk ta gama rikicewa, Khalil yace "Shi garin namu kike ce ma garin nan" Ta hade hannunta cikin kuka tace "Ka rufa min asiri mu wuce gida don Allah" Khalil ya kalli me pharmacy yace "Malam ba mu maganin kawai, hanyar kauyen ba shi da dadin tafiya da daddare, kaga magariba ya kusa" Kuka kawai Nihad take hankali tashe tana kallon khalil, me pharmacy dai ya basu magunguna ya sa a leda ya mika ma khalil yace "Duk prescriptions din na jiki" Khalil ya amsa yace "Nawa ne?" Me pharmacy din ya gaya masa ya zaro kudin a aljihu ya mika masa, Yana kallon Nihad ya daure fuska yace "Tashi mu je" Ta mike tana kuka tace "Kayi min rai kar ka sake maida ni garin nan wallahi baxan iya xama ba kilan ma in mutu" Khalil yace "Fita mu je" Fita tayi daga pharmacy din ya bi bayanta, tayi mugun ba me pharmacy din dariya don sai kallonta yake, ta tafi gun mota tana kuka kamar an aikota ba tare da ta damu da mutanen dake kallonta a wajen ba, bude mata back seat yayi yace "Shiga inda kika fi jin dadin zama ki xage mutane kiyi masu rashin kunya...." Ta shiga bayan motar tana kuka kamar ranta xai fita, ya ajiye mata ledan maganinta ya koma driver seat ya ja motar suka bar wajen..... Wani eatry Khalil yayi parking ya kashe motar bayan ya ɗan sauke glass ya sauka sannan yayi locking motar, ita dai kuka kawai take don har ta saka a ranta cewar in har taga sun nufi hanyar kauyen nan to suma kawai xata yi a cikin motar kuma duk abinda xa ayi mata baxata farfado ba, ba a dau lkci sosai ba ya dawo rike da ledan take away, ya ajiye a back seat sannan ya shiga mazaunin driver yana kallonta ta madubi yace "Bari a kai ki inda xa ki yi wanka kafin mu koma, don naga babu wajen wanka a garin" daga haka yayi reverse suka bar haraban eatry din, Rokonsa Nihad ta dinga yi hankali tashe tana cewa ya rufa mata asiri su koma gida amma bai tanka ta ba, a wani hotel taga ya shiga yayi parking, tsaf ta gane hotel din don sun ta6a xuwa da su Husnah, yanxu da gaske wankan xata yi su koma wannan kauyen?? yana parking ya sauka ya kulle motar ya bude side dinta fuska daure yace "Sauko malama" A hankali ta sauko daga motar, ya dau ledan maganinta da abinci, yana gaba tana biye da shi suka shiga reception din hotel din, ya gaisa da masu aiki a nan, makulli kawai ya amsa alamar dai ya kama dakin tuntuni, ganin yayi hanyar stairs ta bi bayansa tana ji kamar iska xai kadata ta fadi, ya bude dakin ya shiga ita
Chapter 98 · 0% Book details