← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 154 OF 165

Sashe 154

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

nasiha a kan ta bi mijinta, Nihad dai tayi shiru har Mumy ta gama, sannan tace "Toh nagode Mumy, Allah ya saka da Alkhairi" Mumy tace "Yauwa ki gaida yan gidan gaba daya" Nihad tace "Toh Mumy a gaida min da su Sudais" Daga haka ta katse wayar ta mika masa without looking at him, ya rungume hannunsa bai amshi wayar ba yana kallonta da kyau yace "Wato kin dawo da rashin kunya da fitsaran da kika saba yi ma mutane ko?? Kuma i am hoping kin dai tabbatar ni ba sa'anki bane yanzu in all aspect" Ta juya ido tace "To dama ai ba dainawa nayi ba" Sake baki yayi yana kallonta, Ta jefa masa wani kallo tace "Kuma da kake wani daddaga min shoulder 2 days back naga dai babanka ne mai kudi ba kai ba, kuma gidan babanka ne ba naka ba, duk motocin gidan nan na babanka ne not urs, all those securities are for ur father not you, don haka ka jira sai kayi naka kudin kafin ka dinga daga min shoulder kana forming, thinking u are not my mate in all aspect...." Kallonta ya dinga yi da mamaki, ya dake yace "Ke me yasa baki jira kinyi naki kudin ba kike daddaga naki shoulders din da kudin babanki a gidanku" Ta turo masa baki tace "Toh ai ni macece, kuma ni yarinya ce yar karama ban san abinda nake ba" ya kai hannu xai yi squeezing bakinta yace "Sha'awar gado ce ba yar yarinya ba" Ta koma baya da sauri tana kallonsa, ya hade rai yace "Na maki iya abinda xan iya maki albarkacin mahaifiyarki da mahaifinki amma ba don halinki ba domin baki cancanta ba, it's now left for u ki zauna gidan mutane kisan ba gidanku kike ba yanzu, ki kwantar da kanki, ki gane you are now a NOBODY, kina gida ne wanda level dinki bai kai nasu ba, baki wuce kiyi wanke wanke a gidan ba a biyaki, shi ma by luck xaki samu don mu masu degree muke dauka suyi mana aiki a gida.... Dai dai nan aka bude kofar dakin, Aunty Maryam na tsaye bakin kofa tace "Basu gama wayar bane?" Nihad ta mika masa wayarsa tana kallonsa, ya amsa shi ma yana kallonta, dauke kai tayi ta nufi kofa, Aunty Maryam tace "Pls ki yi feeding din Mus'ab, ko na basa ni ba ci xai yi ba" a hankali Nihad tace "Toh" Sannan ta fita, Aunty Maryam ta juya ta bi bayanta, sai a sannan shi ma ya fito parlor, Aunty Maryam tace "Ji Ayman da nake maka magana dazu ina buda WhatsApp yanzu naga message dinsa wallahi" Khalil dai kallonta kawai yayi ya zauna, sai kuma yace "Toh Allah ya baku nasara" Aunty Maryam tace "Ameen" Yace "Xan je gidansu Nadeeyah, sai da safe Aunty" ta gefen ido Nihad dake ba Mus'ab indomie ta kallesa, Aunty Maryam tace "To a gaisheta" Ya mike yace "Xata ji" Daga haka ya nufi kofa ya fita. Har Khalil ya koma Kasar Tanzania ranan lahadi bai koma gidan Aunty Maryam ba, ya dai mata forwarding admission letter da komai na Nihad ta e-mail dinta ranan lahadin kafin ya tafi, Aunty Maryam tayi murna sosai ganin Nile din ya samar mata kuma ta samu, Aunty Maryam ta fito parlor tana kallon Nihad looking so happy for her tace "Congratulations Dear, ga admission letter dinki...." Nihad ta amshi wayar da Aunty Maryam ke nuna mata, ta dinga kallon sunan makarantar as if she wants to be sure, wannan ai Nile take gani, can ta kalli Aunty Maryam tace "Aunty wani makaranta ne?" Aunty Maryam tace "Nile University my dear" Sai da Nihad tayi shock jin da gaske sunan da take gani jikin screen din wayar ne, Nihad tayi karfin halin cewa "Aunty na ina?" Aunty Maryam tace "Wanda dai kika sani" Nihad ta zaro ido tace "Aunty waye ya biya min makarantar?" Aunty Maryam na Murmushi tace "Khalil, he paid the tuition fees and everything, don haka it is good to be good, as a result of the goodness ur father did to him, he is also doing u good by sponsoring you to one of the costliest university...." Lokaci daya Nihad taji bata son zuwa makarantar kuma baxata je ba, amma bata ce ma Aunty Maryam komai ba, Aunty Maryam tace "Anjima xan kirasa in baki waya kiyi masa godiya" A hankali Nihad tace "Toh" Da daddare kuwa Aunty Maryam ta zo har daki ta kawo mata wayar, Nihad ta amsa Aunty maryam ta juya ta fita, ko sallama bata yi masa ba a takaice yace "Bana bukatar godiyarki ba don ki gode min na maki ba, sannan ba don kinyi deserving nayi maki ba...." Nihad tace "Toh ai ba godiyar xan yi ba dama, da ka kwantar da hankalinka kaji abinda xan ce maka kafin ka yanke hukunci.... If you are lucky xa su maka refunding ka sanar masu suyi maka, don baxan je ba" Abba ne xaune parlonsa da Umma dake yanka masa lemo, yace "Kamila ta zo gida ne?" Umma ta kallesa tace "Aa bata zo ba, rabonta da gidan nan ai xai yi sati daya" Abba yace "Ohk na fito masallaci yanzu mijinta ya kirani" Umma ta ajiye wukar hannunta tace "Lafiya dai ko?" Abba zai yi magana aka doka sallama bakin kofa, duk suka kalli kofar, Umma ta amsa ta mike, Inna ta shigo parlon Umma na mata sannu da zuwa da fara'a tace "Saukan yaushe Inna?" Inna ta saki baki tana kallonta, can tace "Da naje ina?" Sai kuma ta ja tsaki bata kara sauraronta ba tana kallon Abba tace "kai Ibrahim kira sabon drebanka maza ya taso ya kai ni wajen jikata ba kashe mutum tayi ba da xan yanke alaka da ita haka kawai, balle babu laifin tsaye balle na zaune sharri ne aka mata, abinda wasu haka zaka ga an masu bedion da mamansu saɓaɓar saɓaɓar a titi, sannan babu dan kamfai a jikinsu mazaunansu mala mala, matancinsu duk a titi, sai ita da idan ba ido mutum yasa sosai ba baxai san babu kaya a jikinta ba, wallahi wani ma tunani xai yi yar shekara shidda ce a bedion indai bedion da aka nuna min ne, bashi da wani aibu da har za a kullace yarinya a banzatar da lamarinta haka, bayan an aura mata gansameme da bamu san isilinsa ba ko ɗan yankan kai ne, ko ɗan kinnafin ne, ko ɗan fashi, oho duk dai bamu sani ba, duk da haka kuma mu fita harkarta? to na dawo hayyacina maza maza a kai ni gidan jikata in ga halin da take ciki yanzun nan"
Chapter 154 · 0% Book details