← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 165

Sashe 125

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

suka mike ganin irin firgitar da tayi, Nihad ta kasa karasawa cikin dakin ta makale jikin kofa ganin yanda kamannin Husnah ya canza, ita tsoronta ma take ji yanzu, shi kam ya karasa can cikin dakin har gun gadon ya kalli su Naf calmly yace "Sannunku" Siyama kawar Naf tana Murmushi ta tashi daga saman kujeran da take zaune ta ajiye masa tana kallonsa keenly, cikin taushin murya tace "Yauwa sannu da zuwa, have a seat pls" Ya dan kalleta yace "Nagode kiyi zamanki" Kallon siyamar kawai Nihad take babu yabo babu fallasa, ai tun da Husnah ta kalli khalil sau daya bata sake yarda ta kallesa ba sai mutsu mutsu take yi a inda take zaune kamar warce cinnaka ke cizo, Naf, Zully, da su siyama sai kallon khalil kawai suke, ya dafa gadon da Husnah ke kai yana kallonta da kyau yayi kasa da murya as if talking to him self yace "How are you feeling?" Naf ta kalli Zully da sauri, Husnah dai kai kawai ta gyada ba bakin magana, ko kadan Nihad bata ji abinda yace ba, Yana gyada kai yace "Quickest recovery dear!! And u are always welcome to our home you Slattern!!" Yana gama fadin haka ya juya ya bar wajen duk suka bi sa da kallo, Zully da Naf sai kallon juna suke da wani expression, Husnah dai bata dago kai ba, Yana isa bakin kofa ya amshi fruits din hannun Nihad ya ajiye masu nan bakin kofar a saman wani table, ya juya ya kullo masu ward din, har suka shiga mota Nihad bata iya ta ce komai ba kamar yanda shi ma babu abinda yace, she still can't believe Husnah ce ta koma haka.... Tana ganin ya dau hanyar gidansu ta daga kai ta kallesa, a kofar gida yayi parking ta sauka ta shiga gidan ba tare da ta jira sa ba, tana shiga parlor ta kalli Nihal dake zaune parlor tana welcoming dinta da fara'a, Nihad bata wani saurareta ba tace "Umma fa?" Nihal tace "Bata nan" Nihal ta taso tana kallonta tace "Kin ga yanda kika yi wani fresh kika kara haske sis, amma kin rame, mu je ki gaida Mumy" Daga haka ta ja ta zuwa bangaren Mumy, Nihad dai gabanta sai faduwa yake don yau kuma bata san me Mumy xata ce mata ba, ga mamakinta da ta gaida Mumy sai taga ta amsa mata normal normal, cikin sanyin murya tace "Mumy ina su Sudais" Mumy tace "Sun tafi islamiyya ya gida?" Tace "Lafiya lau" Mumy tace "Ina Ibrahim din?" A hankali Nihad tace "Yana kofar gida" Mumy tace "Ohk" Nihad ta daga kai ta kalli Mumy dake kallonta, tace "Mumy su sudais basu ta6a zuwa wurina ba" Mumy tace "Za su je in sha Allah" Nihal dake zaune parlon ta mike ta fita, Mumy na kallon Nihad tace "Kin shiga kin gaida Abbanki ne, yana parlonsa" Nihad ta girgiza kai tace "Aa" Mumy tace "Toh in za ku fita ki shiga ki gaishesa" Nihad dai ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, bayan few seconds a hankali Mumy tace "Ina sake tunatar maki ki rike mijin ki, ki bi sa, ki masa biyayya, ki zauna lafiya da shi, farin cikinsa ya zama naki, bakin cikinsa ma ya zama naki, a yanzu baki da wani gata a duniya sama da shi, shi ne gatanki Nihad, kar ki yarda ki bari baraka ya shiga tsakaninku har a ji kanku, Abbanki ba kallonki zai yi ba, tunda a haka kaddarar ki ta zo sai kiyi hakuri ki rungumi kaddararki sai Allah ya dubeki, in sha Allah ina da yakinin Ibrahim baxai cuceki ba, baxai bari kiyi kuka ba in har kika amshesa a matsayin mijin da Allah ya zaba maki a nan duniya" Nihad ta daga kanta hawaye na sauka idonta tana kallon mahaifiyarta, Mumy tace "Duk wani wanda zai zugaki kar ki zauna lafiya da shi ba sonki yake ba, makiyinki ne shi Nihad" Nihad ta gyada kai da kyar hawaye na bin kuncinta tace "Toh Mumy nagode" ita kanta Mumy daurewa kawai take, cike da karfin hali tace "Idan ma da wani abu zaki iya dinga amsar wayarsa ki kirani har zuwa lokacin da zai yarje maki rike waya, Allah ya maki albarka, Allah ya baku xaman lafiya me dorewa" Nan ma Nihad kai kawai ta gyada ma Mumy hawaye na sauka idonta, Sallama khalil yayi bakin kofar parlon, Mumy ta amsa ya shigo ciki, kallo daya yayi ma Nihad dake goge hawayen idonta ya zauna kasa ya gaida Mumy a hankali, ta amsa da fara'a tana tambayarsa gida, Mikewa Nihad tayi wasu hawayen na sauka idonta ta fita daga parlon ta koma main parlor, Nihal na ganinta ta mike tana kallonta har ta zauna kan kujera, Nihal ta karasa ta zauna kusa da ita a sanyaye ta jawota jikinta tace "Kiyi hakuri sis, nasan duk abinda Mumy ta gaya maki abu ne da zai taimakeki har karshen rayuwaki, i want to see u happy and lively once again as before plss sis" Nihad ta fashe da kuka sosai, Nihal ta rungumeta ita ma tana hawaye, Nihad tayi kukanta me isarta Nihal na rarrashinta, daga jajayen idonta tayi tana kallon Nihal da ita ma idonta yayi ja, cikin rawar murya tace "But kema ai kinsan abinda xanyi da wanda baxan yi ba ko Nihal? U know baxan taba yin wannan video din in bar shi a wayana, ba halina bane yin video haka" Tana fadin haka ta kara fashewa da sabon kuka, Nihal ta rungumeta a sanyaye tace "I know sis, ba halinki bane hakan, but we are hoping one day one time gaskiya zata bayyana, in sha Allah xaki yi dariya wataran, in sha Allah" Kai kawai Nihad ta gyada mata tana share hawayen da yaki tsaya mata, A hankali Nihal tace "Mu je parlon Abba ku gaisa, he is inside" Nihad dai tayi shiru, Nihal ta mike ta kamo hannunta suka nufi parlon Abba, Nihal ce tayi sallama bakin kofar parlon, ya amsa ta shiga ciki tana rike da hannun Nihad, tun da yaga Nihad ya hade rai sosai, Nihad dai ta kasa dago kanta, Nihal ta sa suka zauna kasa daga gefen Abba tana kallon Abban a sanyaye tace "Sister dita ce ta zo za ku gaisa Abba" Sai a sannan Nihad ta daga idanuwanta ta kalli Abba cikin rawan murya tace "Abba ina yini?" Abba ya mike yace "Wa ya kawo ki gidan nan" Cikin kuka tace "Tare muka zo da shi" Abba yace "Ba nace bana son in sake ganin kafarki a gidan nan ba, wato u want to dare me shi yasa kika zo right?" Nihad na kuka tace "Don Allah Abba kayi hakuri" A fusace Abba yace "Toh bari kiji, yau ya zama first and last day da zan sake ganin kafarki a gidana, bana bukatarki, bana bukatar ki kwata kwata, kije can kiyi rayuwarki amma wllh kar in sake ganin kafarki a gidan nan, idan kuwa ba haka ba duk abinda na maki You caused it for ur self, sannan ita ma uwarki xan dau mummunan mataki a kanta in har kika sake shigo min gida" Nihal ta fashe da kuka sosai tace "To nima Abba ka samar min wani wajen daban don in na koma makaranta babu abinda xai sake dawowa da ni gidan nan, why will u be so harsh on her kamar ita ta rubuta ma kanta ƙaddara, why are you doing all this to her Abba, so kake wani abun ya sameta, kar ka manta she neva bargained for all what is happening to her, me yasa baxa mu taya ta rungumar kaddararta ba ko zata samu sassauci a ranta? Me yasa zaka dinga korarta Abba??" da mamaki Abba yace "Ohk rashin kunya za ki min? Ni kike gaya ma wannan maganan??" Nihal ta mike tana kuka sosai ta dago Nihad suka fice daga parlon, Tsaye khalil da ya fito daga part din Mumy yayi yana kallonsu, nan saman kujera suka zauna suna kuka a tare, sai ga Abba ya fito parlon, Yana ganin khalil yace "A kan wani dalili ka kawota gidana? Ba nace maka ko da wasa bana son ganinta a gidana ba, don me zaka karya min umarnina?" Shi dai khalil bai iya yace komai ba sai kallon Abban yake, Strictly Abba yace "Toh yau ya xama rana ta karshe da zaka kawota gidan nan, kai ma ba sai ka zo ba kuyi zamanku a can kawai, wai ma ba cewa kayi zaku koma zaria ba? Me ya zaunar da ku har warhaka? To Gobe ka tattarata ku bar garin nan, bana kuma bukatar duk abinda zai sake dawowa da ita kano, gidan da kace ka samar maku da farko nasan akwai sauran kudin da na tura maka last week a account dinka kayi amfani da shi ka biya hayan gidan, sannan ka ajiye min makullin motata...." Shiru khalil yayi yana kallon Abba babu ko kiftawa, duk wannan abun Umma da dawowarta daga anguwa kenan tayi still bakin kofa ta kasa karasowa, Mumy ma da ta jiyo muryar Abba ta fito tana tsaye kofar parlornta, Abba ya kalli Nihad yana nuna mata kofa cikin tsawa yace "Tashi ki fita" Tashi Nihad tayi da sauri Nihal ta rikota cikin kuka sosai tace "But she have all right to stay Abba, u can't just send her away because of a mistake she never bargained for her self, ba ita ta rubuto ma kanta kaddarar nan ba ai naga" muryar Umma suka ji tana cewa "Kul Nihal, kul.... Karen hauka ya cije ki ne kike ja'in ja da mahaifinki? Ashe ke mahaukaciya ce dabba ban sani ba? Are you stupid? Kaji min mahaukaciya shashashar yarinya, ko duniyar ce baki son gamawa da lafiya?" Nihal ta sake Nihad tana kuka sosai ta mike da gudu ta wuce dakinta ta dau waya ta kira Yaya farooq, Umma ta nufi Abba tace "Alhaji ka yayyafa ma zuciyarka ruwan sanyi kada wani abu yaje ya sameka don Allah" Cikin tsawa Abba yace "Su fitar min a parlor kawai" Umma ta kalli Nihad da damuwa tace "Tashi ki fita Nihad...." Sai kuma ta kalli khalil tace "Ka ajiye masa makullin motar ibrahim, ku je kawai kun ji" Mikewa Nihad
Chapter 125 · 0% Book details