← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 165

Sashe 101

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

+2347057607751✍🏻A hankali Nihad ta bude idonta ta dalilin sanyin da take ji, at first sai da tayi imagining cewar ai fa kauyen nan take, a firgice ta tashi xaune tana tattaba daya side din gadon don wutan dakin a kashe yake, amma taji ba kowa wajen, jin laushin duvet yasa ta tuna ashe a hotel suke, wani boyayyen ajiyar xuciya ta sauke, ta sauka daga kan gadon tunda hotel din ba bakonta bane ta san inda switch yake, tana tafiya a hankali ta xagoya xata kunna wutan taci tuntube da mutum ta fada kansa duk da a zaune yake, da farko tayi mugun tsorata amma tana jin kamshin turarensa ta gane shi ne, tashi tayi ta dafa bango ta kunna wutan, zaune ta gansa saman darduma alamar sallah yake, ta zaga daya side din ta kalli agogon dakin ta ga karfe biyu da minti goma, komawa tayi gefen gado ta zauna tayi tagumi, sai kuma ta tuna bata yi isha'i ba ta tashi da sauri ta shiga bandaki. Har ta idar da isha'i sallah yake shima, ta ɗan yi jim kamar xata tashi ta koma ta kwanta can dai kuma kawai ta mike ta hau sallan nafila, har ta mance rabon da tayi qiyamul lail, sai dai in mistakenly ta kwana dakin Nihal shine Mumy ke tashinsu su yi sallan dare, don dare daddaye ne Mumy bata sallan dare, a wannan daren kuma tayi addu'a sosai a kan Allah ya toni asirin duk wanda yayi ruining happiness dinta cikin gaggawa, abinda bata ta6a yi ba tun da abun ya faru, daga karshe tayi addu'ar Allah ya sa khalil ya rabu da ita na har abada don ita ba class dinsa bace, sannan baxata ta6a zama da shi a matsayin mijinta ba, ta kuma yi addu'an bayan Khalil ya rabu da ita Allah ya mallaka mata Aliyu, wajajen karfe Uku da rabi ta fara jin bacci, ta ɗan saci kallon side dinsa, yana zaune saman darduma shi ma da alamar ya idar, amma kana kallonsa xaka san yayi nisa tunanin da yake, and he look so distressing, dauke idonta tayi daga kansa tayi kwanciyarta saman inda tayi sallan, har dai bacci ya dauke wajen karfe hudu bata ga alamar Khalil xai kwanta ba. Da asuba loudspeaker din masallacin dake hotel ne ya tasheta, bata gansa a dakin ba alamar ya tafi masallaci, bayan ta idar tana zaune saman darduma tana azkar ya shigo dakin, ba tare da ya kalleta ba ya shiga bandaki, tana ta zaune kan darduma taji ring din wayarsa kallon gaban madubin tayi da sauri don bata san wayar na nan ba, kuma bata ta6a jin wayarsa na ring ba sai da vibrate, ta mike tana tafiya a hankali ta tafi gaban madubin, Mami ta gani gaban screen din karamar wayar, ta dauka kenan kawai ya bude bandakin ya fito da sauri ya nufota yace "Keee" Ba karamin rikicewa tayi ba ta juyo wayar na hannunta, zaro ido tayi ta saki wata er kara ganinsa daure da towel ta durkushe kasa ta rufe fuskarta da gwiwanta a tsorace, yana isa inda ta durkusa ya warce wayarsa a hannunta ya koma bandakin, duk da taji rufewar kofar bandakin taki dago kanta, bayan kusan minti daya ta dago a hankali tana kallon kumfan da ya sa mata a hannu wajen warce wayarsa, turo baki tayi ta mike jiki a sanyaye ta koma can daya side din gadon ta kwanta tare da juya ma kofar bandakin baya. Tana ji ya fito daga bandaki bayan kusan minti sha biyar sai kuma ta ji ya fita daga dakin gaba daya. Wajen karfe takwas ta gaji da kwanciya ta tashi ta zaga ta shiga bandakin, wanka tayi ta fito bayan ta goge jikinta ta maida kayan da ta cire, tana zaune gefen gado ta jinginar da kanta da gadon tana kallon Tv duk da hankalinta baya kan kallon ya bude kofa ya shigo dakin, tunda ta kallesa sau daya bata yarda ta sake kallonsa ba, ta dai ga ya canxa kaya, shi kam bai kalli inda take ba ya dau towel din da ta yasar saman gado ya shigar da shi bandaki ya fito, ya dauko magungunan da ya siyo mata jiya dake yashe kasan dakin ya jefa mata gefenta ya hade rai yace "Wato dama lafiyarki qlau kika sa naje chemist nayi asaran kudina ko?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Kudin babana dai" kallonta kawai yake ba ko kiftawa, can yace "Gaskiya ne, kudin babanki ne, sai ki taso mu koma can garin kiyi kumallo a can gidanmu, kinga can ai kudin babana ne ba na baban wani ba" Kallonsa tayi da sauri, ganin hada abubuwansa dake dakin kawai yake, tayi karfin halin cewa "Wani garin xan je in yi kumallo?" Ba tare da ya kalleta ba ya nufi kofa yace "Ina jiranki a waje" Ta fashe da matsanancin kuka tace "Ni wallahi baxa ka maida ni wannan garin ba, wai kai baka tsoron Allah ne?" Juyowa yayi ya rungume hannu ya jingina da kofa yace "Sai ke" Cikin kuka tace "Allah baxan je ba, kaji har na rantse, dama ba kwana biyu kawai xa mu yi ba? To wllh baka isa ka maida ni ba" Yace "Ohk, xan nuna maki kuwa na isa, sannan in mun koma sai mun yi wata daya kafin mu bar garin, kinga baxa ki kara min gorin kudin babanki nake ci ba" Cikin tashin hankali tace "Kaga don girman Allah kayi hakuri ka daina ce min haka, wallahi in ka sake maida ni kauyen nan xan iya mutuwa kawai" Khalil yace "Toh mu je a ga adadin kwanakin da xaki iya a can din kafin ki mutu" Cikin kuka tace "Don girman Allah kayi hakuri ka rufa min asiri" Shiru yayi na few seconds, sai kuma yace "Ohk, baxan maida ki garin ba amma da sharadi" Tana goge idonta tace "Ina ji" Ya fi second talatin yana kallonta kafin yace "Nasan komin daren dadewa xa mu rabu... Don haka idan Allah ya kai mu lokacin ina son ko me xai faru baxa ki fasa nuna ma iyayenki cewar ke kika bukaci mu rabu ba ni ba....." Nihad dake ta kallonsa da mamaki tace "Toh me yasa yanxun baxa mu rabu ba kawai, kuma wallahi babu wanda xan gaya ma, kaga babu wanda xai sani sae mu biyu" Yana kallonta yace "Ohk ta yaya kike tunanin xa mu rabun yanxu?" Ta gyara xama tace "Kawai kace ka sakeni, babu me sani sai ni da kai" Yace "Toh idan aka yi hakan sai me xai faru?" Ta daga kafada tace "Ba komai, kawai kayi rayuwarka inyi ta wa, ni xan ma iya bar maka gidan gaba daya kawai sai dai in dinga xuwa diban kayana, idan kana so ma sai ka saka yan haya ka dinga karban kudin kana xubawa a aljihu" Khalil ya ɗan yi murmushi ya gyara tsayuwarsa yace "Ohk, sai ki ci gaba da iskancinki daga inda kika tsaya kenan ko?" Tayi masa wani kallo tace "Me kake nufi? Ni nake yin iskanci? Kana nufin ni yar iska ce?" Yayi wani murmushin takaici yace "Toh baxan yi abinda kike so yanxu ba, kawai dai ki sa a ranki lokacin hakan na zuwa, nan ba da dadewa ba" Ta kyabe baki tace "Ni fa lokacin da kake nufi da yanxu duk daya ne ni a wajena" Ya daga kafada yace "Gwara dai a jira lokacin" Ita dai bata kuma cewa komai ba amma a ranta tunani take ashe ma ba wani babban sharadi bane, dama ita ai babban burinta su rabu na har abada, Ta kallesa tace "Ka dai yi alkawarin rabuwa da ni??" Yace "In sha Allah" Wani farin ciki taji ya rufeta tace "Toh nima in sha Allah ko ma me xai faru xan ce nice nace mu rabu babu ruwanka" Yace "Toh" Tace "Toh nima ina da deal dina in har kana son inyi abinda kace nima sae kayi abinda nake so" Yace "Ina sauraronki" tana gyara zama tace "Na farko ina son ka bar ni in ci gaba da xuwa makaranta na, na biyu baxa ka hana duk wanda xai zo wajena xuwa ba, like kawayena infact everybody, na uku xaka bani spare key na gida nima, sannan na karshe ina son ka bar ni da wayata..." Kallonta kawai khalil yake, ta langwabar da kai ta wara ido tace "Ehh, ni gwara nawa minor request ne, babu abinda xai ragu a jikinka idan kayi accepting, naka request din kuwa kilan har tsine min xa a iya yi a gida amma kuma ban damu da hakan ba na amince xanyi yanda kace" Khalil yace "Abu biyu kadai xan iya maki a abubuwan da kika ce, idan kuma kinga hakan bai maki ba kawai a bari, mu ci gaba da zaman mu yanda muke, kuma dole a titi ace maki matar drivern gidanku" Ta marairaice sai kuma tace "Toh ina ji, ka gaya min abu biyun" Yace "Babu xancen xuwa makaranta sannan baxa ki rike waya ba!!!" Shiru Nihad tayi tana nazari, wato kawayenta xa su iya xuwa gidan sannan xai bata makullin gida, daga kai tayi ta kallesa taga kallonta yake yana jiran jin me xata ce, tace "Toh ai shikenan, na amince" Yace "Sannan abu na karshe wanda muhimmancinsa kusan daya da sharadin farko...." Tace "Ina jin sa" Yace "Babu ke babu kallon inda wayata take balle ki ta6a, a takaice babu ruwanki da wayana har xuwa lokacin da xa mu rabu" Nihad ta kyabe baki tace "Toh dama ni meye ruwana da torchlight phone dinka bawan Allah??" Ya gyada kai yace "Toh" Juyawa yayi ya fita daga dakin, ta mike ta dau ledan magungunanta ta saka Hijab sannan ta bi bayansa. A reception ta tarar da shi ya bada makullin dakin ya fita compound din hotel din ta bi bayansa, wani ma'aikacin hotel din ne irin masu share share ya ganta yace "Ahh Hajiya kwana biyu kin buya, ya kawayenki" Nihad ta juya ta kallesa, murmushi tayi tace "Lafiya lau ya aiki?" Yace "Alhamdulillah, yau baku zo da kawayen naki ba kenan? Naga kullum tare ku ke" Sai kuma ya kalli Khalil dake tafiya yace "Au ashe da oga ku ke...." Katse sa Nihad tayi da sauri tace "Aa, drivern
Chapter 101 · 0% Book details