← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 165

Sashe 144

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

an san kina bin wa ennan kawayen har ma ki bi su duk inda xa su?" Nihad ta girgiza kai tace "Stepmom dita ce kawai ta sani, ta ma san gaba dayansu" Buda baki Aunty Maryam tayi, sai kuma tace "Kuma bata hanaki alaqa da su ba?" Nihad tace "Aa, tace min in rikesu baxan samu kamarsu ba don suna sona sosai, kuma tana kare ni yanda yan sauran yan gidan baxa su gane ba, idan na dawo da daddare ita take bude min kofan parlon mu idan an kulle" Aunty Maryam was really shock jin abinda Nihad tace, taji zufa na keto mata, tace "Mamarki fa?" Nihad ta girgiza kai a hankali tace "Bata sani ba ai, dama a bangaren stepmom dina nake, so akwai distance tsakanin part din stepmom din tawa da na Mum dina...." Aunty Maryam tace "Wa ya ce ki koma part din stepmom din taki?" Nihad tace "Aa wai tun ina karama ta dawo da ni wajenta shi ne har na girma" Aunty Maryam tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, to ina jin ki, idan ta bude maki kofar da daddare sai tace maki me??" Nihad tace "Kawai cewa xata yi inyi sauri in wuce kar a gan ni" Aunty Maryam bata san sanda hawaye ya kawo idonta ba, nan ta kara tsorata da lamarin kishiya, bata san sanda ta dafe kanta da yayi mata nauyi ba, can ta dago da kyar tace "Bata da yara ne?" Nihad ta girgiza kai a hankali tace "Tana da yarinya mate dita, her name is Nihal, ita kuma tana side din Mumy na, sannan akwai Amina da Aunty Kamila that is married" Aunty Maryam tace "Kuma duk su ma yaran nata dake gidan suna fita su kai dare ta bude masu kofa?" Nihad ta girgiza kai da sauri tace "Aa babu inda suke zuwa su, ba ma su da friends" Aunty Maryam tace "Nihad" Nihad ta daga kai ta kalleta, Aunty Maryam tace "Ku nawa ne wajen mamanki?" Nihad tace "Mu uku ne, ni ce first born" Aunty Maryam was so heartbroken, tace "Ita kuma fa?" Nihad tace "Babban yayanmu ya Farooq sai ya Usman, sai Aunty Kamila, Nihal da Amina" Aunty Maryam na girgiza kai tace "Yanzu a tunaninki duk gidan wa yafi sonki? Yake maki duk abinda kike so?" Nihad ta sunkuyar da kai a hankali tace "Umma" Aunty Maryam tace "Wacece Umma?" Nihad tace "My Stepmom" cike da takaici Aunty Maryam na girgiza kai tace "Ta cuci rayuwarki, ta cuceki, ta cuci mahaifiyarki, ita kuma salon nata kishin kenan?? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, da wannan abun da ta maki da gwara ta fuskanci mahaifiyarki su xuba kishin yanda ya kamata, bata maki adalci ba, kuma ko tantama babu da sa hannun wannan matar a video din naki, Nihad wani masoyinka ne xai dinga supporting dinka kana bad things, kana abubuwan da basu dace ba? Wani masoyinka ne xai xuba maka ido ka fita ka kai har dare shi bai maka fada ba kuma ya kareka ta yanda wasu baxa su sani ba balle su maka fada? Wani masoyinka ne xai ce ka rike yan iska masu shaye shaye a matsayin kawaye har yana ikirarin baxa ka samu kamar su ba, sannan ya daure maka kugu ka dinga bin su duk inda xa su? Nihad me yasa ita nata yaran basu da kawaye sannan basa fitan dare?" Shiru Nihad tayi tana kallon Aunty Maryam ko kiftawa babu, Aunty Maryam tace "Ba shiru xa kiyi min ba bude baki ki bani amsa yanzun nan?" Tunda Nihad take bata ta6a zaunawa tayi wannan tunanin ba balle har ta gane komai tayi reasoning a kai, ita dai Aunty Jamila kawai rabata take da Umma ta karfi da yaji amma bata ta6a zaunawa ta zayyano mata abubuwan nan da Aunty Maryam ta zayyano mata ba yanzu, to ai bata ma san abinda take yi da sanin Umman ba balle har ta zayyano mata wannan abubuwan tunda komanta a boye take yi, Umma ce kawai ta sani... Aunty Maryam bata yi interrupting Nihad a duniyar tunanin da ta fada ba, kana kallon fuskarta zaka fahimci she is slowly trying to comprehend duk wani abinda Aunty Maryam ta fada ne, babu kuma abinda ya fado ran Nihad sai karyan da suka yi ma yan gida wai zata bi Aunty Kamila kebbi alhalin hostel xata koma da zama, Umma da Aunty Kamilar ne kadai suka san gaskiyar maganar, kuma har ta gama zamanta hostel din for more than 3 months Umma bata ta6a zuwa inda take ba, har ita Aunty Kamilan, alhalin idan mutum na hostel kuma iyayensa na garin ko bayan sati uku ne su kan kai masa ziyara.
Chapter 144 · 0% Book details