← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 165

Sashe 13

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dade da xubawa ba, Aminu ne ya xo amsar ma sabon dreba abinci Aunty Nihad ta hana" Nihal tayi shiru da mamaki, can tace "To saboda me?" Hafsah tace "Nima ban sani ba wllh" Nihal ta buɗe abincin tana kallo, can ta rufe ta kalli Hafsah tace "Ki kai masa" Hafsah ta xaro ido tace "Ta fa hana Aunty Nihal" Nihal bata kuma cewa komai ba ta dau spoon ta daura saman abincin ta fita daga kitchen, xaune ta tadda Khalil bakin gate da mai gadin, mai gadin ya dauko masa wani guntun bread dake ta ajiye dakinsa da pure water ya basa, kallonta suke gaba daya, shi dai Khalil yana kokarin gane wacece, don kamarsu ta ɓaci da Nihad, sai da ta karaso ya gane ba Nihad bace don Nihad ta fi ta haske har ma da tsayin hanci, amma both suna da dimple, ta mika masa abincin tace "Ga abincin" Amsa yayi ya d'an yi murmushi wanda iyakarsa Lips yace "Nagode" Juyawa tayi ta koma ciki, Mai gadi yace "Kaga er albarka, muna ganin abubuwan al'ajabi fa a gidan nan, halaye iri iri in gaya maka, kaga Nihal din nan da kake gani, ko kadan bata yi halin uwarta Hajiya ba, yarinya ce nutsatssiya ga sanin ya kamata, uwa uba ga girmama d'an adam ko da kuwa almajiri ne, ba dai ka ganta da kawaye ba kuma, uwarta kuwa ban ta6a ganin mace mara kirki mara mutunci irinta ba duk nan hakuri muke da ita, gashi bata da aiki sai shige ma matan manya manyan kasar nan, sannan ita kadai ce bata yarda Habibu ya ja ta a mota ba, duk sanda xata fita sai ta bari Alhaji ya fita sannan ta ja mota ita ma, bata dawowa kuma sai dab da magariba motar nan kaga duk yayi butu butu da laka malam, tana dawowa kuma xata sa Habibu ya wanke motar, ita kuma wancan Ja'irar da ta hanaka abinci ban ta6a ganin me kirki irin uwarta ba, wato matar Alhaji ta biyu kenan, ga dai ita ce ta fari gun uwarta, tsakaninsu da Nihal kwana daya tak, shi sa xaka gansu kamar yan biyu, sai kuma Allah ya basu kama daya, komai nasu iri daya ne, to wllh Hajiya Mumy uwar Nihad mace ce me mutunta mutum babu ruwan baiwar Allahn nan da duniya, sai gashi Allah ya hadata da shaidaniyar yarinya, bata da aiki sai na bitar kawaye da rashin daraja ɗan adam, to haka Allah yayi ikonsa a gidan nan, kyansa ace Nihad uwarta Umma, ita kuma Nihal uwarta Mumy kaga dai dai kenan, amma Allah bai tsara hakan ba, ni fa da rana daya aka haifesu sai muce canja su aka yi a asibiti, amma Nihal aka fara haifa er baka da ita washegari aka haifi Nihad ita kuma fara tass, kaga ko ai ba ayi canje ba" Khalil dake kallonsa yana sauraronsa attentively yace "Ita Umman yaranta nawa?" Mai gadi ya gyara xama irin abun nema ya samu din nan, yana kirga su da yatsa yace "Kaga Farouq shine ɗan ta na fari, a Habuja yake aiki, ya kan yi wata biyu ma bai leko gidan nan ba, ba laifi yana da kirki da faram faram da jama'a, shi ma kuma bai yo halin uwarsa ba gaskiya, sai Usman shi kuma kadaran kadahan, shi ba a ma gane alkibilarsa, yana da kirki oho, bashi da kirki oho, atoh a haka na san sa gaskiya, sai Kamila warce tayi aure shekara biyu kenan, wani shegen mai kudi Umman tasan yanda tayi ta hadata da ta aura, sai Nihal sannan autarsu Amina, amma fa ta fi ji da Nihal din don ita ma auta take kiranta, ita wannan Aminar ma mara kunya ce gaskiya amma fa akwai son karatun addini, tana ajin karshe na sakandari, Nihal kuma ABU Zaria take, ita Nihad makarantarta ance yayi Miliyan biyu xuwa uku, haka naji su Saminu ke cewa, Maryam Abatcha naji suka ce sunan makarantar" Khalil yace "Toh ita me xuwa Maryam Abatcha din su nawa ne gun Mamarta" Mai gadi yace "Ai ita ce ta fari, sai kanninta biyu duk maza, Sudess da Fadil" Khalil bai ce komai ba ya bude abincin hannunsa ya dau spoon ya fara ci. Nihad na gama cin abinci ta tafi bangaren Mum dinta, shiryawa ta sameta tana yi hankalinta a d'an tashe, Nihad tace "Mumy me ya faru?" Mumy tace "Yanxu Jamila ta kirani wai kanwar mijinta ta rasu" Nihad ta dafe kirji tace "Kaddai Aunty Salma?" Mumy tace "Ita" Salati Nihad ta saki tace "Allah sarki, Allah ya ji kanta, Mumy in sa Hijab mu je" Mumy tace "Ki sameni a waje, drivern bai fita ba dai ko?" Nihad tace "Mumy kiyi driving din mana ko kuma ni inyi" ko tanka ta Mumy bata yi ba ta dau handbag dinta ta fita, bangaren Umma ta fara shiga ta sanar mata rasuwan, Umma tace "Allah Ubangiji ya ji kanta, in sha Allah idan xaki koma gobe sai mu je muyi gaisuwa mu ma, Allah ya ji kan musulmi" Mumy tace "Ameen, Allah ya kai mu goben" Part din Abba ta nufa, shi ma ta sanar masa rasuwan daga haka ta fita compound, Mai gadi yayi kasa da murya yana ma Khalil magana yace "Yauwa kaga Hajiya Mumyn ita ce uwar Nihad, ina ga fita xata yi" Muryar Mumy suka ji tana cewa "Aminu Drivern ya fita ne?" Mai gadi ya mike da sauri yace "Aa gashi nan Hajiya a kusa da ni" Khalil ya mike ya gaisheta da ladabi, Mumy ta amsa cikin mutuntawa tana kallonsa daga sama har kasa, sai kuma tace "Shi ne Drivern?" Khalil yace "Ni ne Hajiya" Mumy tace "Don Allah xaka ajiye ni nan Hotoro ne idan ba damuwa" yace "Toh Hajiya" Makullin motarta ta mika masa, ya amsa da ladabi Aminu ya nuna masa motar Mumy, gun motar ya nufa, Mumy ta daga wayarta dake ringing ta kai kunne, Nihad ce ta fito ita ma sanye da Hijab har kasa, tana ganinsa cikin motar Mumy ta wani daure fuska, bayan yayi warming motar ya karaso da motar har inda Mumy take ya tsaya, Mumy ta bude bayan motar ta shiga, Nihad ma ta bude baya xata shiga mumy tace "Baxa ki xauna a gaba ba" Without looking at her mum tace "No, i will be more comfortable at the back" Kulle motar tayi ta bude handbag dinta ta ciro tsadadden shade dinta ta saka, Khalil ya ja motar Mai gadi na daga masu hannu har suka fita compound din ya kulle gate, cike da nutsuwa Khalil ke driving din xuwa hotoro da Mumy tace daga Nasarawa GRA. Suna isa dai dai family house din mijin kanwarta Jamila ta sa yayi parking, Mumy ta fara sauka daga motar tana kallonsa tace "Ko xaka je ka dawo xuwa bayan magrib ka daukemu, kar a bar ka kayi ta jira a nan" Yace "Aa babu komai xan jira daga can tsallaken in sha Allah" Jin haka Mumy tace "Toh shkkn" Daga haka ta juya ta shiga gidan rasuwar Nihad na biye da ita a baya. Nihad bata yarda ta xauna cikin jama'a da suka fara taruwa gidan ba ana koke koke, ta nemi waje at the far end of the compound ta inda generator din gidan yake ta xauna ita daya a wajen, Iphone dinta ta ciro a jakarta, taga missed calls din Husnah da Naf, da sauri tayi dialing Number Husnah, yana fara ring Husnah ta daga tace "Ina kika shiga ne babe" Nihad tace "Wllh mun fita tare da Abba ne, and i left my phone at home, what's up kun fitan ne?" Husnah tace "Tun yaushe, ke in gaya maki akwai labari wllh" Nihad tace "Yanxu dai kuna ina?" Husnah tace "Tahir guest palace, kiyi kokari ki taho yanxu kar ayi ba ke" Nihad tace "Husnah Hijab fa ne a jikina, mun xo wani gaisuwa da Mumy a hotoro" Naf ta amshe wayar don a handsfree Husnah ta sa, tace "Haba dai minti nawa kin shiga boutique Nihad" Nihad tace "Toh shkkn bari in amshi makullin motar Mumy a hannun driver in taho kawai, nasan before magrib xata koma gida kafin nan na dawo" Naf tace "Shkkn xa mu jira ki a Tahir din be fast pls" Katse wayar Nihad tayi tana bin compound din da ido trying to figure out where her mum is, har ta kare xaga tsakar gidan da idanuwanta bata ga mumy ba alamar dai ta shiga cikin gidan, tashi tayi da sauri ta nufi gate ta bude ta fita, nan ma ta dinga waige waigen inda xata hango drivern, tun da ta fito ya ganta, don yana xaune daga tsallaken bakin titi wajen mai siyar da Fruits, hada ido suka yi ta tsallaka da sauri ta nufesa babu yabo babu fallasa tace "Hey ka bani makullin mota xan mika sako in dawo yanxu" Kallon me siyar da fruits din yayi kamar dai da shi take, nan da nan Nihad ta harxuka cikin tsawa tace "Malam da kai nake fa kake kallon wani" Ya kalleta sai kuma ya kara kunnensa gaba yace "Na'am?" Nihad was soo mad at him, xuciyarta ya dinga tafarfasa ta rasa abun ce masa, shi ma kuma bai kuma cewa komai ba sae ma dauke kansa da yayi, ruwan da ta gani cikin roba gun me siyar da fruits din ta fixgo a fusace ta juye masa gaba daya tun daga saman kansa, duk mutanen dake wajen suka kame a inda suke baki bude suna kallonta da mamaki, Tana huci cikin bacin rai tace "Kai din banzaaa kana driver din gidanmu har xan dinga maka magana kana mayar ni mahaukaciya, who do u think u are?? Waye kai??"
Chapter 13 · 0% Book details