Sashe 157
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a airport" Yace "Allah ya kai mu" har ya tashi tace "And one last thing xan bata waya, kar kuma kace zaka amshe, kawai dai ka sa mata ido wajen ganin da su wa da su wa take communicating" Yayi shiru yana kallonta, tace "Sannan na ba Ayman layin da na sa mata a wayar da xan bar mata" Shi dai Khalil kallonta kawai yake, tace "Ka ji abinda nace?" Yace "Na ji" tace "Sai anjima" juyawa yayi ya fita daga parlon nata. Khalil na sauka downstairs ganin Zeenah a parlor yace "Ina Moon?" Tace "She is sleeping upstairs" Yace "Ohk, ya preparation din tafiya?" Tace "Mun gama tun jiya" yace "Good" Ya fi minti biyar tsaye a parlon, daga karshe kawai ya fita compound, nan gidan ya bar motarsa don akwai wani abokinsa a layin da xa su je wani wajen tare yanzu. Washegari da safe Khalil ya nufi airport tare da Mami da Mimi with Noor, Aunty Maryam ta tafi da motarta da yaranta uku da mai aikinta da Nihad, don tun da taga motar khalil a gidanta ta sanar masa xata taho da motarta airport sai ya maido mata gida ya dau nasa, Noor kuma tayi driving dinsu Mami su koma gida, har suka isa Airport Nihad bata daina kukan da take ba, she felt everything is over for her, it's just like they are sending her away from home for the second time, she felt insecure without Aunty Maryam, she won't have anyone to confide in anymore, bayan Aunty Maryam ta isa airport din tayi parking, har ma ta daina ba Nihad baki ganin ba sauraronta take ba, ta dau waya ta kira khalil, ya sanar mata sun kusa isowa, tana ta jira har ya shigo airport din with escort, murmushi tayi don tasan babu abinda ya tsana kamar wannan escort din, kawai dai babu yanda xai yi don escort din na Mami ne sae in ita tace masu bata bukata, wannan kuma sai in ba waje me nisa xa ta ba, tuni aka masu providing wajen parking babu 6ata lokaci, bayan few minutes Mami da su Mimi suka sauko daga motar, Aunty Maryam ma ta sauka ta tafi ta gaida Mami, yaranta ma duk suka sauka xuwa wajen, Noor ta rungume Aunty Maryam tace "Ohh i feel like crying Aunty, xa mu yi missing dinki sosai" Mimi ma ta marairaice tace "Me too Aunty" Mami na murmushi tace "Toh ba sai ku tafi gaba daya ba" Noor tayi dariya tace "We wish" Nan mai aikin Aunty Maryam ta durkusa ta gaida Mami, Mami ta amsa tace "Murja sai Uk ko?" Murmushi tayi tace "Za mu yi kewanku Mami" Mami tace "Toh Allah ya tsare, Allah ya kai ku lafiya" Nihad bata yarda ta sauka daga motar ba ta hade kai da gwiwa tana shesshekan kuka, Aunty Maryam bata yi forcing dinta ta sauko ba cause she feel sad seeing her cry that way, Mami tace "Toh ina yarinyar?" Aunty Maryam ta ɗan yi murmushi tace "Kuka take a motar shi sa ma ban bari ta sauko ba" Mami tace "Kuka kuma? Kukan me?" Aunty Maryam tace "Sabo mana Mami" Mami tace "Allah sarki" Tuni aka sauke kayansu zuwa cikin airport din, Khalil dai na tsaye ya jingina da motarsa ya rungume hannu, lkci lkci yake kallon motar Aunty Maryam, Sai da xa su shiga cikin airport din bayan sun yi sallamar karshe da su Mami Aunty Maryam ta koma gun motarta ta bude back seat ta dafa shoulder din Nihad a hankali tace "Be a good girl dear, Allah ya tsare ki, Allah kuma yayi maki albarka, in sha Allah xa mu dinga waya sosai duk abinda ya dameki kar ki boye min ki dinga gaya min kin ji, kuma kar ki fasa addu'a da tashin daren da kike kamar yanda kika saba in sha Allah xaki ga sakayya cikin gaggawa, sannan ki dinga daukan kiran mutumin da na ba numberki banda walakanci my dear, he is a good guy, and u will enjoy communicating with him" Nihad ta kasa ce mata komai sai kuka take, Aunty Maryam ta juya cike da karfin hali ta bar wajen duk Khalil na kallonsu, Ta mika masa makullin motarta yace "Allah ya tsare Aunty" Ta gyada masa kai ta nufi cikin airport din su Mami na daga masu hannu, Khalil ya mika ma Noor makullin motar Mami dake wajensa, Ta amsa tace "Till we meet home yayanmu" Juyawa yayi ya nufi motar Aunty Maryam ya bude driver seat ya shiga ya tada motar, ya riga su Noor fita daga airport din, har sannan Nihad bata daina kukan da take ba kamar ranta zai fita, shi ma kuma bai ce mata komai ba, har ya isa gidan Aunty Maryam, bayan an bude masa gate ya shiga yayi parking motar a parking space, Nihad ta kasa dago kanta, ya sauka daga motar ya jingina jiki, bayan few minutes ganin ba bude motar xata yi ta sauko ba ya bude mata, da kyar ta sauko daga motar xata bar wajen tana harde kafa tana kokarin danne kukan da ya taho mata taji ya jawota kusa da shi, lkci daya ta fashe da kukan ta rufe fuskarta a jikinsa, drawing her more closer to himself yayi kasa da murya yace "Da kin bi ta ai" Ya bar ta ta ci kukanta bai hanata ba, har ta gaji tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya, sai kuma ta rufe ido tana shaƙar daddadan kamshin jikinsa, tana kuma jin yanda zuciyarsa ke bugawa. They stood in that way for almost 5 minutes, lokaci daya yaji ta sakar masa duk jikinta, yayi saurin rungumeta sosai kar ta zame kasa, he could feel her breathing calmly, kamar kuma warce aka tsikara ta bude ido da sauri ta janye jikinta shi ma yayi saurin saketa, ta koma gefe tana murza ido, shi kuma yayi keeping straight face.... she is so sleepy don jiya ba wani baccin kirki da tayi, ya ciro makullin motarsa ya bude tasa motar, ya shiga yana warming dinsa tana kallonsa tace "Kayana" Ya daga kai ya kalleta, ta koma gun motar Aunty Maryam ya bude booth din da makullin, ta ciro jakunkuna biyu, daya na wasu kaya da Aunty Maryam tayi mata, daya kuma wanda ya siya mata, ta zuba kayan a booth dinsa ta kulle sannan ta shiga back seat, bayan ya gama warming motar suka bar gidan, Nihad ta ɗan shinshina Hijab din jikinta jin kamshin dake tashi a jiki, a hankali ta kwanta jikin motar ta lumshe idonta, har suka isa gidansu bata sani ba tana bacci, bayan yayi parking ya kashe motar ya sauka still Nihad bata farka ba, ya bude back seat din yana kallonta, patting din kujeran motar yayi still bata bude ido ba, sai kuma ya kai hannu jikinta yana tashinta, sae a sannan ta bude ido da sauri tana bin inda suke da kallo, ganin compound din jikinta yayi sanyi, ya zaga ya bude booth ya fiddo jakunkunanta, ta sauko daga motar tana kallon securities din bakin gate din, ya kulle motar yana rike da jakunkunan nata biyu ya fara tafiya, ta bi bayansa tana jan kafa tayi kalan tausayi da fuskartar, ta inda ya shigo da ita gidan ranan farko da suka zo ya bi da ita yanzu ma, har suka isa bangaren Mami, ya kai mata kayanta guess room dake bangaren, tana tsaye bakin kofar har ya karaso ya shiga parlon Mami sannan ta bi bayansa, Mimi ce kadai zaune parlon, Mami kuma na bedroom dinta, ya zauna saman kujera Nihad dai ta koma gefe ta tsaya, kana ganinta kasan she isn't happy being here, ya ɗan hade rai ya nuna mata kujera, ta sauke kanta kasa ta zauna saman kujeran, Mimi na kallonta tace "Hi" Nihad ta daga kai ta kalleta, Mimi na murmushi tace "I am Mardiyya, and you?" Nihad dai sai kallonta take jin yanda tayi pronouncing R din sunan alamar dae bata cikakken R 😜, Khalil ya juya ya kalli Nihad jin tayi shiru, Nihad ta kalli Mimi tana ɗan murmushi tace "I am Nihad" Mimi ta wara ido tace "Waow, You have a nice name, ina da wata fwend with ur name" Khalil na kallon Mimi yace "Hey take her to the guess room ta kwanta, she is sleepy" tashi Mimi tayi tace "Ohk mu je" Nihad ta tashi tana kallonsa, sai kuma ta bi bayan Mimi har zuwa dakin, babba ne dakin sosai sai kace ba guess room ba, furnitures din dakin ma kadai abun kallo ne, sannan ga bandaki shi ma babba a ciki, har da kayan kallo akwai a dakin, Yanda aka gyara dakin kuwa ga zanin gado sai sheki yake kai kace akwai mutum a ciki ne, Mimi tace "An wriga an gyara dakin yau, so za ki iya kwanciyarki" Nihad tayi murmushi cause her intonation and most especially how she pronounces her letter R is very funny to her, can dai tace "Thank you" daga haka ta kwanta saman gadon, Mimi ta juya ta fita, nan da nan bacci ya dauke Nihad... After sleeping for many hours ta bude ido a hankali, tsaye ta ga Khalil a dakin yana jera mata kayanta a press din dake dakin, Kallonsa take kawai don bai san ta tashi ba, duk Abayas din ya jera su waje daya, haka Hijab da atamfofi da Aunty Maryam tayi mata kusan kala takwas, tana ganin xai ta6a inner wears dinta ta sauko daga kan gadon da sauri ta turo baki tace "Ka bar min xan yi kayana da kaina" ya juya ya ɗan kalleta, sai kuma ya kwashi duk inners din ya mayar da su cikin jakar ya koma gefe ya tsaya yana kallonta, taki Kallonsa, a takaice tace "I need space" Daga sama har kasa ya kalleta sai kuma ya juya ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita daga dakin, duk sai da tayi seperating inners din nata, sannan ta koma ta kwanta tayi lamo saman gadon tana tunanin Mumy.