← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 165

Sashe 116

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

https://wa.me/c/2349090591769Nihad ta fito daga wanka bayan ta gama shafe shafenta ta zauna tana tunanin abinda xata sa yau ta kwanta don dama kayan baccin biyu ne kawai ya rage mata kuma duk ta sa su bata wanke ba, ita tunda take ma ta ta6a wanki a rayuwarta banda pant da bra, Husnah tayi mika tana kallonta tace "Ke kuma tunanin me kike haka?" Nihad ta kalleta a sanyaye tace "Toh kayan baccin nawa duka duka biyu ya rage fa a gidan nan gashi nan kuma duk na sanyesu ba a wanke ba" Husnah ta mike zaune tace "Toh ke garin yaya kika zo da kayan bacci kala biyu kawai?" Nihad tace "Ko ba can kauyensu na rabar ba, da tsummokara fa mutanen kauyen ke yawo wallahi" Dariya Husnah tayi tace "Toh kawai ki saka undies dinki sai ki saka hijabi ki kwanta" Nihad tace "Kin ta6a ganin na kwanta haka?" Husnah tace "Yanzu ma dai ina kayan wanki naki yake?" Nihad ta nuna mata inda ta ajiye su har da hijab kala biyu, Husnah ta mike tace "Nasan ko tsutsa xa su yi a nan ba wanke su xa kiyi ba bari in wanke maki su in samu ladanki" Daga haka ta kwashi kayan ta shige bandaki, Nihad ta mike ta dau Hijab dinta kawai ta saka don dama akwai sanyi sanyi garin alamar hadari, tana ta zaune tana game da wayar Husnah, sai ga Husnah ta fito rike da bucket tace "Can waje zan je in shanyasu ko?" Nihad tace "Ehh ta baya xa ki ga wajen da xakiyi shanyan" Daga sama har kasa Nihad ke kallonta don wani skimpy night wear ne a jikinta, gashi ko bra bata saka ba, Mikewa Nihad tayi tace "Bari kawai in shanya" Husnah tace "Ka ji ki, Aa wllh gwara in cike ladana, da me ya hanaki wankewa balle ki shanya, kawai ni bari in je inyi shanyana" Daga haka ta nufi kofa, Nihad ta kwashe gwangwanin maltina da suka sha da bottle wata ta bi bayanta, Yana zaune parlor hannunsa rike da remote, ga ledan abincin nasa har sannan bai ta6a ba, Husnah sai satan kallon ledan take har sai da ta buge da kujera ta kusa faduwa, da ido ya bi ta, ta nufi kofa da sauri, Nihad dake kallonta har ta fita ita kuma tayi hanyar kitchen taje tayi disposing thrash din hannunta a dustbin sannan ta fito parlo, ta koma kamar xata shiga daki sai kuma ta tsaya bayan 2 seater dake side din tana kallonsa, shi dai idonsa na kan tv, ta yanda xata fara masa tambayar da Umma tace tayi masa kawai take tunani, Ganin bata da alamar barin wajen can dai ya daga kansa ya kalleta yace "Lafiya?" ta jefa masa wani kallo tace "To banda ina son inyi maka tambaya ance maka xan tsaya nan ne" Ya ɗan yi shiru sai kuma yace "Wa za ki yi ma tambaya?" A takaice tace "Kai" Yace "Ohk, ni za ki yi ma tambaya kenan" Hararansa ta dinga yi wato har wani feeling kanshi yake zata masa tambaya, ya kafeta da ido yace "Yi tambayar ki" Babu yabo babu fallasa tace "Dama baka gaya min sunan gwaggwonka ba a can garin, har da babanka ma duk baka gaya min sunansa ba" Ita kanta tasan she sounds stupid, sai kuma ta fara sosa kai, kallonta kawai yake ba ko kiftawa, can yace "Tun a garin baki tambayeni ba sai yanxu da daddare?" A takaice tace "Ehh saboda sai yanxu na tuna" Yana gyada kai yace "Ohk!! To wa ya aikoki ki tambayeni sunan su?" Ta wara ido kamar munafuka tace "Aa fa, ba wanda ya aikoni yace in tambayeka nice kawai na tambayeka ina son sani" Yana kallon kwayar idonta yace "NIHAD" ta kara buda ido a ɗan rikice tace "Na'am" Yace "Sunanta kenan" Lokaci daya ta hade rai tace "Ban gane Nihad ba, sunanta ne sunana?" Yace "Ehh" Ta dinga masa wani mugun kallo, can tace "Toh don baka da kunya sai ka wani kira sunana gatsau wai Nihad, sunan nawa ka raina haka? waye ma ya gaya maka sunana? Aminu me gadi ko???" Khalil bai kuma ce mata komai ba ya bude ledan dake ajiye gabansa ya ciro drink din, dai dai nan Husnah ta shigo parlon ganin lemon a hannunsa wani farin ciki ya mamayeta tana kallon Nihad tace "Ke an fara yayyafi fa, kije ki rufe windows ko" Khalil ya ajiye kwalin lemun hannunsa ya mike ya shiga kitchen xai dauko glass cup, wajen lemon Nihad ta nufa da gudu, Husnah da ke kokarin shiga daki tana ta murmushi ita kadai kamar ance ta juya taga Nihad ta kinkimo lemun ta taho da gudu xata shige daki, cike da zafin nama Husnah ta fixge lemon daga hannunta tace "Meye haka sai kace mayunwaciya Nihad, bai siyo ya baki ba sbda rashin hankali kin wani dauko masa abinda kika fi karfi, me xa ki yi da abin hannunsa, bayan kudin ma kinsan na wanene ya ke ci, a'a wllh kin bani mamaki" Bata jira cewar Nihad ba ta koma da sauri sauri ta ajiye masa lemon ta bar wajen sai gashi ya fito kitchen, tuni Husnah ta figi hannun Nihad ta shige daki da ita ta kulle kofar tace "Wallahi kin bani kunya, me xa kiyi da lemonsa ke da ko ni kika ce in kawo maki carton din lemon can tsaf xan siyo in kawo maki, balle Umma ma kina gaya mata xata bayar a kawo maki har gida? Me ya kai ki? Ke fa har yanxu yarinta na damunki wllh, banda yarinta meye kike abu haka babu class, yanzu na gano dalilin da yasa yayi mugun raina ki" Nihad dai bata ce komai ba, Husnah ta sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, dai dai nan aka fara ruwan sama kamar da bakin kwarya, Husnah ta zaro ido tace "Lahh ga ruwan ya sauko, ki kulle windows din dakunan ni kuma bari inje in kulle na parlor" Daga haka ta fice da sauri zuwa parlor, Nihad ta bi ta da kallo sai kuma ta bi bayanta, farin ciki bai kara lullube Husnah ba sai da tagansa rike da lemon a glass yana sha, ta kasa daina murmushi ta tafi ta kulle windown parlon ta shiga ma kitchen ma ta kulle sannan ta fito tana kallonsa tace "Sai da safe" Bata damu da ta ji ya amsa ba ta nufi daki tana jijjige inda ya kamata a jikinta, Tana kallon Nihad dake bakin kofa tace "Wai duk kika ga na fito sai ki biyoni" Nihad tace "Aa ni kitchen xan tafi ne" Husnah bata ce mata komai ba ta shige daki, Nihad ta shiga kitchen ita kanta tasan babu abinda xata yi a kitchen din bayan ta gama zagaye zagayenta ta fito ta nufi dakinta, da ido khalil ya bi ta har ta shiga dakin, makulli ta saka ta zare makullin, Husnah dake kwance tana danna waya tace "Kamar da wasa fa sai ga ruwa ko ba komai garin yayi sanyi naturally ayi bacci me dadi" Nihad dai bata ce komai n a ta hau saman gado daga daya side din ta jawo pillon ta jefa makulli a ciki Husnah dai na ta kallonta da gefen ido, Husnah ta mike zaune tana kallonta tace "I want to take malt but gaskiya baxan iya shanye daya ba, idan na rage maki xa ki sha ai ko?" Nihad ta girgiza kai tace "Aa na koshi" a hankali Husnah tace "Toh shikenan, bari in bari kawai kar ayi asaran sa" Nihad tace "Ki sha ki rage ki ajiye mana" Husnah tace "Aa ni kinsan bana son almubazzaranci ke kuma dama kin iya walakanta abinci, da dai kuna da fridge ne sai in je in ajiye sauran amma idan aka bar shi haka ai lalacewa xai yi, ba fa wai da yawa xan rage ba ni nasan gejin cika na, kadan zan rage wllh" Nihad tace "Wa yace maki malt na lalacewa??" Husnah tace "Ke dai tunda baxa ki sha sauran ba shikenan sai in hakura in kwanta da craving dina" Nihad tace "Ni wallahi ban ta6a jin inda malt ya lalace ba sai a bakin ki, ki sha kawai ki rage yayi ta lalacewan mana" Husnah bata kuma cewa komai ba ta kwanta, bayan kusan 10 mins ta mike zaune tana kallon agogo dake nuna karfe goma da rabi ta jawo malt daya kawai ta bude ta fara sha, kallon Nihad tayi ganin kamar ta fara bacci ta tasheta, Nihad ta bude ido a hankali Husnah tace "Wai kin daina alwala ne idan xaki kwanta?" Nihad na lullumshe ido tace "Zan yi" Husnah tace "Aa tashi kije kiyi gaskiya kafin bacci me nauyi ya dauke ki" Sai da ta tashi Nihad kusan sau uku sannan Nihad ta tashi da kyar duk da tunda ta xo gidan nan bata ta6a alwala idan xata kwanta ba amma dabi'arta ce yin hakan tun bayan da taje tayi wani hutu wajen Aunty Jamila na sati uku, Aunty Jamila bata ta6a barin ta kwanta bata yi alwala ba, kuma bayan ta dawo gida kawai training din ya zama jikinta, in dai xata kwanta sai tayi alwala wani lkcn Umma tayi ta mata fada idan taga tayi tace so take sanyi ya shiga jikinta, Nihad na shiga bandakin Husnah ta jawo jakarta da sauri ta bude wani abun maye ta zuba kusan quarter a cikin ɗan malt din ta rage sannan tayi saurin mayar da shi cikin jaka ta ajiye jakar, har ta dauko pillown Nihad xata cire makulli sai kuma ta fasa ta mayar da sauri, Nihad ta fito daga bandakin bayan tayi alwalan ta nufi inda xata kwanta Husnah tace "Don girman Allah ki shanye guntun malt din nan saura kadan, ta6a ki ji" Nihad ta girgiza kai tace "Aa baxan sha ba kawai ki ajiye" Husnah ta dinga kallonta sai kuma tace "Ohhh sai yanxu ma na gane, wai kyankyami yasa baki son ki sha kamar warce ta zuba na bakinta a ciki?" Nihad ta kalleta tace "Ni nace maki haka?" Husnah tace "Aa haka ne mana, banda haka meye don na sha malt na rage maki ki ki shi Nihad?" Nihad tace "Ke dai kin san yanda xa ki bi ki
Chapter 116 · 0% Book details