← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 165

Sashe 56

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba, ko da shi ka zo?? kuma ashe kasan aiki kake gidanmu amma kake min rashin kunya iri iri saboda kai fitsararre ne, banda rainin hankali ma yanxu lokacin shigowa daki a kwanta ne? Shi kansa mai gidan naga yana wajen aiki yanxu haka, to idan ka ga dama ka fito Mumy tana kiranka, sako ne dama aka bani in isar maka kuma na isar, idan kuma baka ga dama ba sai ka shanya bakin ka ci gaba da baccin..." Jin motsi a parlor ta juya ta ga su Husnah bakin kofar duk sun shigo, alama tayi masu da su karaso, Khalil dake ta lura da ita ya karasa bakin kofar dakin bata ankara ba kawai gani tayi yayi banging kofar dakin almost on her face sannan ya sa makulli ya kulle, buda baki tayi da shock tana kallon kofar su Husnah suka karaso da sauri, tana zaro ido tace "Kun ga abinda yayi min yanxun nan" Naf ta kwankwasa kofar da karfi tace "Ashe dai kai karamin ɗan iska ne mahaukaci tunda har ka kulle kofar, da ka jira mu karaso kaga ikon Allah mana, wallahi da sai mun ji uban da ya tsaya maka yau kafin mu bar nan, kuma wallahi kaji kunya tunda har mata suka tsorata ka ka kulle kofa da sauri" Nan duk suka hau gaggayan bakaken maganganu marasu dadi a bakin kofar dakin, ita dai Nihad mamakin abinda yayi mata ya sa ta kasa cewa komai sai kallon kofar take, suka kare masa zagi na cin mutunci tass sannan Husnah na huci tace "Mu je, ai akwai wani lokacin, ni ban san shegen matsoraci bane ba ma ai...." Duk Khalil na jin su, and he was calming himself and controlling his mood at the same time, duk da it's too much and too heavy for him, lokaci daya launin idonsa ya canza, daga karshe ya daina juyo muryarsu gaba daya, Mikewa yayi walking slowly ya tafi bakin window ya tsaya yana kallon waje ko kiftawa baya yi, tunda ya xo gidan sai ranan ya ji da gaske he truly hate the sight of Nihad, at first he was trying his best not to hate her sbda bai iya tsanar mutum, shi yasa yake kokarin ganin bai tsane mutum ba no matter what, but he now realized he hate everything about her, da ya san xai zo gidan nan har ya hadu da ita da ya hakura da zuwan nasa no matter what and he is going to loose nothing, juyawa yayi ya tafi jakarsa ya bincika har kasa ya fiddo wani abu me kamar diary da pen dinsa, ya bude plane page yayi rubutu da bai wuce layi uku ba ya ajiye pen din yana kallon takardan, rufewa yayi ya mayar karkashin jakar ya kulle sannan ya mike ya koma gun window din ya tsaya, he is so hurt, it's been long he felt this way, but they can't just come and insult him then go scot free, wayarsa dake vibrate saman gado ya karasa kamar bai son tafiyar ya daga pillown ya dau wayar, Nihal ce ke kiransa, ya ajiye wayar ya zauna gefen gado har ya katse, sake kira tayi hakan yasa ya dauka ya daga ya kai kunne cikin low voice yace "Barka da yamma Hajiya" Nihal ta gaishesa tace "Friend dita fatima tace min ka amsar min sakon nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Gently yace "Ameen, ya karatu?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Allah ya bada sa'a" Tace "Ameen nagode" Yace "Ki turo number Tailor din naki" Tace "Toh xan tura maka, nagode" Yace "Yauwa sai anjima" Daga haka ya katse wayar ya ajiye gefensa. Da daddare Nihad ta shiga bangaren Umma da sleeping dress dinta, zama tayi a bedroom dinta har ta fito daga bandaki tace "Ya aka yi Nihad?" Nihad tace "Umma dama wancan drivern xaki taya ni yi ma magana gobe da safe xai kai ni can gidan Aunty Kamila da kayana idan ya so daga can sai Naf ta zo da mota ta kwasar min kayan mu tafi hostel" Umma tace "Toh ke me yasa baxa kiyi masa maganar ba, tsoronsa kike ko me?" Nihad ta wani zaro ido tace "Cabdi, inji tsoron wa? Ko Abbana bana tsoronsa sai wani mere Drivern gidanmu, kawai bana son ko wani magana ya sake hadani da shi har abada a gidan nan, don naga ba shi da manner sannan ya gama rainani, tunda Mumy ta mareni a gabansa shkkn ya daina respecting dina yana ganin dai dai muke, duk Mumy ce ta janyo min komai, to wannan yasa na yi vow har motar ma baxan dinga shiga tare da shi ba, wannan ma kawai dole ne ya sa don babu yanda xa ayi kayana ya dau adaidaita sahu" Umma tace "Balle ma shiga adaidaita Sahu ba girmanki bane, ita kuma Maryam in taga disgaki gaban ma'aikatan gidan shine dai dai sai ta ci gaba, shi yasa a rayuwa kar ki kuskura ki raga ma talaka ina maki wannan hudubar, don da ya ga fuska shikenan raini sai wanda ya manta, barin yan kauyen nan shi yasa ko kallon arziki kar ki yarda ya hadaku ma" Nihad tace "Ai ni dama bana masu kallon arxiki Umma" Umma tace "Ya dai fi miki, ajin ki daban da nasu, shkkn ki je ki kwanta goben xan masa magana idan Allah ya kai mu" Nihad tace "Nagode Umma" Zata fita dakin Umma tace "Kuna dai waya da Aliyun ko?" Nihad ta juyo tace "Ehh muna yi, yanxu ma da shi muka gama magana na fito" Umma tace "To madallah, yaushe xai kara zuwa?" Nihad tace "Umma kinsan akwai wani business din Abbansu a can kasar waje shi ne manager so he is not always in Nigeria, though sauran business din Abban nasu na nan kasar ma duk shi ke running dinsu, haka ne ma yasa bayan watanni kadan yake shigowa Nigeria, amma yace min in a month time xai shigo in sha Allah" Umma tayi shiru, Nihad tace "His father owns a big company shi da wani White Man, so Aliyu is managing it for him in there" Umma ta ɗan yi murmushi tace "Ba shakka, Allah ya sanya Alkhairi, kice koman baban nasa a hannunsa yake" Nihad tace "Ehh, he is his dad favorite also" Umma tayi murmushi tace "Kamar ke kenan ko" dariya kawai Nihad tayi ta nufi kofa Umma ta bi ta da kallo har ta fita daga dakin sai kuma ta sauke ajiyar xuciya. Washegari Umma ta samu Khalil bayan ya dawo daga kai su Amina makaranta, da ladabi ya gaisheta fuskarta kamar bata ta6a dariya ba tace "Kai nan da karfe tara xaka kai Nihad gidan yayarta" Khalil da kansa ke kasa yace "Toh Hajiya" Juyawa tayi ta bar sa wajen a tsaye, ya daga kai ya bi ta da kallo. Kamar yanda Umma tace karfe tara saura Nihad ta fara fitowa daga akwatunan ta nan balcony ta ajiyesu ta tafi bakin gate tana kallon Khalil dake zaune, Ta ɗan tabe baki tace "Ga akwatunan da xa a sa a booth a can balcony" Ko kallon direction din da take tsaye bai yi ba, sai ma kara hade rai da yayi, tace "Malam magana fa nake maka fa" Still khalil yaki kallon inda take balle ta sa ran yace wani abu, Aminu ya mike da sauri ya tafi balcony din Nihad ta bi sa da kallo, sai kuma ta kalli khalil cike da takaici amma ta kasa ce masa komai, har Aminu ya gama kwaso kayan ya ajiye a garage, ya taho gun khalil yace "Ɗan bude booth din a xuba su" Mikewa Khalil yayi ya tafi gun motar bayan ya bude booth ta makullin ya shiga driver seat, Nihad ta bi sa da wani shegen kallo, tana mamakin irin wannan feeling din da yake, sai kuma ta ji haushin kanta da bata sa Aminu ya kwaso akwatunan ba tayi ma wannan banzan magana ya kyaleta, bayan ya tada motar ta tuna bata ma Mumy sallama ba, komawa cikin gidan tayi ta tafi bangaren Mumy, khalil ya fi minti sha biyar a kofar gida yana jiranta cikin mota, tana sane tayi xamanta cikin gida don yayi ta jiranta a mota, sai da taga ta 6ata minti ashirin sannan ta mike ta fita tana rike da handbag dinta, back seat ta zauna ta kulle motar tana kallonsa, ya ɗan kwantar da driver seat ya rufe idonsa kamar mai bacci, da har xata masa magana ta tuna sabon vow din da ta dauka na cewar ba maganar da xai sake hadata da shi, yau ne last. Har bayan minti biyar bata ga ya bude ido ba balle ya tada motar su bar wajen, ta wani hade rai tana kallonsa, wasa wasa har sai da aka yi minti goma suna nan a haka, tana ta control din kanta kar tayi masa magana, Aminu dai sai lekosu yake yana dariya kasa kasa, wato sai ya rama shanyasa da tayi cikin mota, tana ta xaune motar ta cika tayi fam amma taki cewa komai kuma bata sauka ba har sai da aka yi minti ashirin da biyar sannan ya bude ido ya gyara zamansa ya kunna motar suka bar wajen, da yake ya ta6a kai Nihal gidan yayarsu kamar yanda ta ce masa, saboda shi ma baya son wata magana ta hadasa da Nihad direct gidan ya nufa ba tare da ya damu can din ne ko ba can ba, the ride was so silent, ko wannensu fuska a tamke, lkci lkci take satan kallonsa sai kuma ta kyabe baki ko ta ja tsaki can kasa kasa, har yayi parking dai dai gate din gidan kamila ya kashe motar, Nihad ta bude ta sauka ta tafi ta kira mai gadin gidan tace "Don Allah ka zo ka sauke min kayana a mota" Ya fito daga gate din ya bude booth don khalil ya riga ya bude, nan ya ciro mata akwatunan ya kai su bakin gate, kafin ya ciro na karshen tana kallonsa tace "Don Allah ka je kace ma wancan drivern nace ba sai ya wani zo yana kai ni makaranta ba don bana bukatarsa kwata kwata" Mai gadin ya tafi yana kallon Khalil bayan sun gaisa yace "Wai Hajiya tace ba
Chapter 56 · 0% Book details