Sashe 124
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Join my WhatsApp group for beautiful samples. https://wa.me/c/2349090591769Duk a zaton Nihad aljanin daren ne ke tattaba ta cikin Hijab, tunda dama da shi ta kwanta a rai, a rikice take tattaba jikinsa tana kokarin cire hannunsa daga bakinta ta kara kwala wani ihu kamar xata shide, bayan ta gano shine ta fada jikinsa da sauri ta rufe fuskarta a kirjinsa tana kuka sosai tace "Don Allah kace Abba ya canza mana gidan nan ni baxan iya zama ba wallahi, wayyo Allah na shiga uku" Ya rike ta very tight shi ma ya daura fuskarsa saman kanta, tana jin yanda yake sauke numfashi still holding her tightly, kamshin turarensa shi ma ya taimaka wajen kara kwantar mata da hankali, sun fi minti goma a haka, jin ya ki saketa ta dago a hankali har lkcn gabanta na faduwa tana kallonsa cikin duhun, a hankali taji ya saketa ya koma ya kwanta a bit relieved, tana ganin haka tayi saurin kwanciya bayansa tana kuka a hankali, ko minti biyar bai kara ba bacci me nauyi ya daukesa, Nihad kuwa bata sake komawa baccin ba, don duk tunaninta kilan shi ma ya ga aljanin daren ne shine ya ji tsoro ya riketa haka, toh shi ma ya ji tsoro ina ga ita, hakan ya kara daga mata hankali ta dinga shige masa tana shesshekan kuka ta takure cikin hijab dinta, raba daren Nihad tayi tana masu gadi, duk motsin da taji sai ta kara makale masa, sai kusan karfe hudu da rabi bacci barawo ya saceta. A hankali khalil ya bude ido ta dalilin tada sallah da aka yi, ya mike zaune da kyar ya kunna switch din dakin dake bangaren da yake ya juya yana kallonta, baccinta kawai take, ya kalli towel dinta dake can side din sai kuma ya sauka daga kan gadon ya shiga bandaki, Har ya dawo masallaci Nihad bata farka ba, kallo daya yayi mata ya dauke kai da sauri, ya dau karamar wayarsa ya fita daga dakin. Sai karfe bakwai saura Nihad ta bude ido a hankali, bin dakin tayi da kallo sannan ta kalli gefenta towel dinta ta gani a yashe ta zaro ido ta kalli jikinta da sauri ta mike zaune tana gyara hijab dinta, kaddai ya ganta haka? Tunanin hakan yasa ta rufe fuskarta da pillow tana kara rufe jikinta da hijab dinta a kunyace, daga karshe dai ta mike ta shiga bandaki, bayan ta idar da sallah tana ta zaune saman darduma har gari ya waye gaba daya sannan ta mike ta fita ta koma dakinta, wanka tayi ta shirya ta fito parlor, bata gansa a parlon ba sai wayarsa dake saman kujera, ta kalli kofar kitchen din alamar yana kitchen, ringing wayar ya fara yi ta kalli kofar kitchen din da sauri, da ta ga kamar bai ji ba tunda bai fito ba tana tafiya a hankali ta karasa gun wayar ta dauka tana kallon me kiran, Father ta gani a screen din, dai dai nan ya fito daga kitchen din ta mayar masa da wayar ta ajiye, kamar yanda ta ki kallonsa shi ma haka bai yarda ya kalleta ba, ya tafi gun wayar ya dauka, kallon screeen din yake ko kiftawa babu, yana ta kallo har kiran ya katse, ta ga ya zauna without knowing he did so, still kuma idonsa na kan screen din, he looks a bit baffled, sake kiransa aka yi, ya daga kai ya kalleta suka hada ido, sai kuma ya dauke kansa ya mike ya nufi kofar ya fita compound, bayan ya fita still bai daina kallon wayar ba kuma ya ki dagawa, zaunawa yayi a saman dakalin da ya saba zama ya daga kiran tare da sallama, he wasn't given the space to even greet or say anything, ya dai yi shiru yana sauraronsa har ya gama fadin abinda xai fada ya rufe ido a hankali yace "Gobe in sha Allah" yana fadin haka yaji an katse wayar ya kalli screen din, sai kuma ya jinginar da kansa da bango, and he sat there for more than an hour ya kasa shiga cikin gidan, Nihad dake ta zaune parlor ta mike ta shiga kitchen din taga shayin da ya hada a mug har ya huce. Har Nihad ta iso inda yake bai sani ba, shadow dinta da ya gani ya sa ya daga kai, ta jingina da bango tace "Me yasa ka bar shayin a kitchen a bude kuma?" Bai ce mata komai ba, ta tsaya for almost 2 mins, can ta juya ta koma ciki, dafe kansa yayi, a karo na farko yayi regretting barin wayarsa a kunne, yawanci sai xai yi waya yake kunna wayar yana gamawa kuma zai kashe but for almost 3 months now ya daina kashe wayar. Tashi yayi daga karshe ya shiga cikin gidan, tana zaune saman kujera ta bi sa da kallo kamar ya sani ya juyo ya kalleta, ta dan turo baki ta ci gaba da kallon tv da take, har bayan azahar khalil na daki, Nihad ta ji ana kwankwasa gate, ganin bata ga alamar zai fito ya bude ba ta mike ta tafi dakinsa, murda kofar tayi ta shiga ciki, a rufe taga idonsa, ta karasa inda ya ajiye makullin ta dauka ta fita, tana bude gate din gidan taga Naf da zully a tsaye, ta ɗan buda ido cike da fara'a tace "Lahhh, sannun ku da zuwa" Naf tace "Nihad, yaushe Husnah ta bar gidan ki?" Nihad da gabanta yayi mugun faduwa don suna cewa Husnah aljanun daren da ta manta ne suka fado mata, cike da karfin hali tace "Jiya da safe" Naf ta kalli Zully, sai kuma ta kalli Nihad tace "Toh lafiya qlau ta bar gidan ki?" Nihad ta marairaice tace "Ni dai da safe na ganta jikinta wani iri kamar an zaneta, fuskarta duk ya kumbura haka ma bakinta da idonta shine tace min wai aljanun dare ne suka mata haka" Naf da zully suka kwashe da wani dariya barin Naf da sai da ta kai kasa sbda dariya, Naf ta dago bayan tayi dariyarta me isarta tace "Halan ku biyu kadai ne a gidan?" Nihad ta girgiza kai tace "Aa shi ma yana nan ai" Zully tace "Ke kuma kina ina sanda aljanun daren yayi mata haka?" Nihad tace "Ni dai bacci nake, kuma ai kun san anyi ruwan sama, kawai na tashi da safe na ganta a kitchen duk an zaneta, tace in miko mata jakarta da wayarta" Dariya kawai su Zully suke har da kyakyatawa, Nihad dai sai kallonsu take with confusion, Naf tace "Toh sai ku daure ku zo dubata a asibiti don tana can rai a hannun Allah an bata gado, mu kuma ce mana tayi bata kwana a gidanki ba hatsari tayi xata tafi kaduna jiya da daddare an kirata mamarta ba lafiya" Nihad ta gwalo ido tana kallonsu, Naf tace "Ai kam dai tana asibitin da aka ta6a kwantar da kawar zully nasan kin gane asibitin" A hankali Nihad tace "Na gane" Naf tace "Sai ki gaya masa ya kawo ki ku dubata, don da aiki ma ake da niyyar mata a idonta daya daga baya kuma idon ya ɗan bude kadan" Nihad tace "Toh xan gaya masa" Naf tace "Mu yanzu akwai inda za mu, amma xa mu hade a asibitin anjima in ya kai ki kenan" Nihad tace "Toh" Daga haka suka koma motar Naf ta bi su da kallo, sai da suka bar layin sannan ta juya ta koma cikin gidan, tsaye ta gansa bakin kofar parlor, tana karasawa balcony ya hade rai yace "Wa ye ya Kwankwasa gate din?" Babu yabo babu fallasa Tace "kawayena ne, sun zo su ce min Husnah tana asibiti bata da lafiya wai har xa ayi mata aiki a idonta daya, ni dai wllh ka kai ni in dubata tunda a nan gidan aljanun daren suka mata haka" Kamar xata yi kuka ta kare maganar, ya dinga kallonta, can ya juya ya koma ciki. Bayan la'asar taga ya shirya yana rike da mukullin mota ta mike da sauri kafin tace komai yace "In kin shirya ina jiranki idan kuma baki shirya ba inyi tafiyata" Da sauri ta tafi daki ta dauko hijab din ta ta saka, bayan sun bar gidan taga sun hau saman titi tace "Asibitin xa mu je?" Yace "Ohk" Nan ta gaya masa asibitin, tana ganin sun kusa asibitin tace "Baxa mu siya mata wani abu ba?" Yace "Ohk za ki siya mata wani abu kenan?" Tace "Ehh" Yace "Me zaki siya mata?" Tace "Ga wasu masu fruits can kawai ka tsaya mu siya mata" Parking yayi dai dai wajen ta bude motar ta tafi tace su hada variety of fruits na 10k, suna hadawa ta shigo motar tana kallonsa tace "Dubu goma ne" Yace "Ohk, ki basu" Tace "Toh ina atm card din?" Yace "Atm din wa?" Ta wani kallesa tace "Naka mana?" Yace "Ni nace maki ina da kudin siyan fruits?" Ta marairaice tace "Toh amma ba sai da na tambayeka ba?" Yace "Bani da kudin biyan fruit din kawarki" Kamar zata yi kuka tace "Na shiga uku, bayan kasa nace su hada fruits din, ni yanzu ya zan ce masu?" yace "Ke ina atm card din ki?" Tayi narai narai da ido tace "Bama ni da shi ni, kuma wllh babu ko sisi account dina tunda Abba ya dai a bani kudi" Yace "Sauka kice masu su mayar da fruits dinsu kin fasa siya" Ta gefen ido take kallon alamar atm card din nasa dake aljihun rigarsa, can ta zura hannu da sauri ta cafki atm din, rike aljihun yayi yace "Keee" Ta hade rai tace "Idan baka sake ba zan karya wallahi" sai kuma ya cire hannunsa a hankali, ta turo baki ta zare atm card din ta sauka daga motar ya bi ta da kallo, ta basu suka cire kudinsu ta koma mota da fruits din ta saka atm card din a handbag dinta ta kulle, bayan few seconds kawai ya tada motar suka bar wajen. Suna isa asibitin Nihad bata taba tunanin zai shiga dakin ba, amma sai kawai ta ga ya shiga, Husnah na hada ido da shi sai da ta firgita, Su Naf da Zully da wasu frnds dinsu biyu dake dakin