Sashe 26
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
downstairs ta fito compound, fuskar nan nata a murtuke ta nufi gate, mai gadi dai ya kauda kai da sauri don tare suke da Khalil, shi dai ya rasa kan wannan abinda ke faruwa tsakaninta da Khalil, yana mugun ganin karfin halin Khalil da baya nuna shakkarta kamar su, har ta fita gate ta dawo tana kallon mai gadi fuskar nan nata babu rahama tace "Kai in ji dai kuna kula min da tsuntsaye na? Don idan har wani abu ya samesu wllh kaf gidan nan duk sai kun raina kanku ban cire kowa ba kuma" Da ladabi yace "Ko daxu sai da naje can da kaina Hajiya" Ficewa tayi daga gate din bayan ta maka ma khalil da bai ma san tana yi ba harara, Mai gadi ya kalli khalil yace "Sai fargaba nake kar tace xaka kai ta wani waje" Khalil yayi murmushi yace "Meye a ciki, sai a kai ta ai..." Da yake babu wani nisa da kafa Nihad ta bi ta cikin anguwanni har ta isa gidan yayan Abbanta, Hamid na xaune compound tare da wani abokinsa, kallo daya tayi masu ta kara gaba abunta, Abokin nasa yace "Wannan ba cousin din nan taka bace, naga ta wuce bata ce maka komai ba, and kamar kuna good time da ita ai" Hamid yace "Noo, step sisters dinta ne muke good time, wannan ai yar iska ce" Abokin yace "Shit but sun yi kama sosai, kamar har ya wuce misali" Hamid yace "Toh wannan da kake gani ji take da girman kai da rainin wayo, sannan runz girl ce..." Abokin ya wara ido yace "Waow dai dai mu kenan, ka hadu mu to" Hamid ya masa wani shegen kallo yace "Ai da manyan mata ake runz ba kwailaye ba, kwailar ma fitsararriya irin wannan" Tuni Nihad ta shige gidan, direct part din Kakarta ta nufa, tana bude kofar dakin ta shiga, inna tace "Aa, daga ina haka, Ibrahim din ya shigo ne" Nihad tace "Ni kadai ce" Inna tace "Aa naga sai ya taso keyarki kike xuwa shi sa abun ya daure min kai, ina ce tare ku ke" Nihad ta nemi waje ta xauna, Inna tace "Baki da lafiya ne?" Nihad ta fashe da kuka kamar jira take tace "Inna wani sabon driver Abba ya dauka, yaron ba shi da kunya ya raina ni inna, ba irin rashin mutuncin da baya min" Inna da ta saki baki tace "Shi Dreban?" Nihad ta gyada mata kai tana goge hawayen idonta, Inna tace "Ko ba wani gansameme ba yana tafiya gansan gansan?" Nihad tace "Shi" Inna tace "Toh ai Ibrahim din ya kawo sa har nan ya gaisheni, amma ni na xata ɗan arxiki ne, don har kasa ya duka ya gaida ni" Nihad tace "Wllh na munafurci ne...." Nan ta labarta ma inna abinda ya faru kamar yanda ta gaya ma Umma, Inna tace "Ba lafiya, shi dreban??"