← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 148 OF 165

Sashe 148

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read

gwara ya dauwama babu auren har ya mutu, yanzu in zai yi auren ai dukiya ne ba ta wasa ba yaya xai kashe, don har lefe shi xai yi masa, toh kiyi imagine nawa xai basu su yi lefen, ai miliyan 10 ma albarka" Hajiya Amina tace "To ke yanzu baxa ki yi ma Malam magana ayi duk yanda xa ayi ya auri ko Farhana ko Sajida ba? Ai gwara yan gida su mora da yan waje" Aunty Hassana tayi wani dariya kawai ta kyabe baki bata ce komai ba, Hajiya Amina tace "Allah kuwa da dai ya auri yarinyar nan gwara anyi haka kawai mu san har yanzu mu ne" Aunty Hassana na girgiza kafa tana wani Murmushi tace "Ke kin zata a banza ne har yanzu ba ayi auren nasa da Nadeeyah ba, sai yayi ta ce masu ba yanzu ba har ya bar gidan nan?" Hajiya Amina tace "Toh yanzu gashi ya dawo ga kuma uwar yarinya har ta fara mana sintirin gida" Aunty Hassana tace "Xata yi ta gama, baxai auri er ta ba, balle wata kuma can"
Chapter 148 · 0% Book details