← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 165

Sashe 121

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai ya sakar masa er sa" Shiru Umma tayi tana nazari, can wayar Umma ya fara ring ta bude jaka da sauri ta fiddo ganin me kiranta tace "Minti biyu Malam" Daga haka ta mike ta fita can tsakar gida ta daga wayar ta kai kunne tace "Malam barkanmu da safiya" Ta kara da cewa "Eh ba a dai samo sunan ba amma nan da awa daya za mu karaso in sha Allah, don Allah ka jira mu Malam kaga dai daga waje me nisa za mu zo" Hajiya Turai na kallon Mutumin dake gabanta tace "Kana ji malam? so muke shi Alhajin ya fita tsabgar daga shi dreban har yar tasa, sannan maganan gini da yace zai ma yar a Zaria a rushe zancen kwata kwata, malam gaba daya a sa yaji bai son su gaba daya, bai kuma son ganinsu, ita yar dama kawai ya sallama ma duniya ita, sannan abu na karshe ka saka ma shi dreban jin son zai koma inda ya fito wato kauyensu, ka sa zaman birnin ya gagaresa, idan ya so su koma can inda ya fito su ci gaba da zama shi da ita yarinyar" Umma ta shigo ta zauna, Hajiya Turai ta kalleta tace "Duk na gama gaya masa abinda zai yi" Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh shikenan" Dariya mutumin yayi sosai yace "Kudi... Aikinku aiki ne babba, kuma aiki dole sai da kudi, kinga kafin mu daura aiki a kansa dole za mu warware kadan daga abubuwan da aka masa sannan aikin mu xai samu shiga, ba a hada aiki da aiki ai, sai wancan aikin nasu ya lalata min nawa, wato ya ki barin nawa yayi wani tasiri, ko kuma nawa ya rage tasirin nasu, haka abun yake, yanzu dai nine xan rage tasirin na kansa sannan in dora nawa" Umma tace "Tohh mu dai koma yaya za ayi kawai mu ga mun ci nasara malam, sannan ya dai ci ace an saba yanzu Malam, abu dai shekara da shekaru ana tare ana harka, wannan karan a dubemu karba tsula mana kudi" Hajiya Turai tace "Ai kuwa dai malam, ayi mana sassauci gaskiya" Yana ta6e baki na wasu yan sakwanni sai kuma yace "Kawai ki dire dubu dari da hamsin idan aikinki ya ci ki cika dubu hamsin" Umma ta bude jakarta ta ciro zoben gwal ta ajiye masa tace "Gashi nan wannan dubu dari da tamanin ce, ka rike ka fara min aiki" Ya amsa yace "An gama" tace "Toh malam zuwa nan da yaushe za a fara aikin sannan za a fara ganin tasirin aikin?" Yace "Yanzu zan afka jeji in fara aikinku babu bata lokaci, gaba daya a yau xan yi duk abinda xan yi, zuwa gobe kuma aiki zai fara ci kamar yankan wuka" Umma na Murmushi tace "Toh mun gode Malam, Allah ya saka maka da alkhairi, aikin ka ai mun san ba wasa, mu yanzu za mu tafi sai na kira ka" Daga haka suka masa sallama suka kama hanyar wani kauyen daban. Nihad na ta zaune parlor har kusan sha biyu, can ta mike ta nufi dakin da yake kwance, a hankali ta murda kofar dakin tana kallonsa saman gado ta gansa yana bacci, ta rufo dakin sannan ta shiga dayan dakin tayi wanka ta dauro alwala ta shirya ta fito, sai da ta fara zagayawa ta kwaso kayan da Husnah ta wanke mata ta kai su daki ta linke daga nan ta dawo parlor ta shiga kitchen, kallon kitchen din kawai take, akwai kayan miya da komai a gidan kawai nama ne babu tunda babu fridge, ta fito ta tafi dakinsa, ta bude kofar trying to make no sound, gun Atm card dinsa ta tafi ta dauka da makullin mota da na gida sannan ta fito, cikin mintin da bai wuce talatin ba ta fita taje ta siyo frozen chicken guda biyu da few spices sannan ta dawo gida, ta sake daura alwala tayi sallah bayan ta idar ta koma kitchen din, sai kusan karfe biyu ta fito daga kitchen bayan ta gama duk abinda take, gaba daya ta gaji likis uwa wace tayi girkin mutane goma, ta fada kan kujera, har ta mance rabon da tayi girki don ko da wasa Umma bata sa ta wai saboda hayaki da warin gas, duk sanda taje gidan Aunty Jamila ne take girki don dama Aunty Jamila chef ce, tana gwada mata abubuwa da yawa na girke girke, saving grace din Nihad kenan da har Allah ya taimaketa ta iya girkin, tana ta zaune parlon sai kuma ta mike ta tafi dakinsa ta bude tana kallonsa, bata ga alamar yayi sallah ba, ta karasa ciki ta tsaya side din gadon ta bubbuga pillown da yake a kai tace "Baka yi sallah ba" Ya bude ido da kyar ya kalleta yace "Ina ruwanki?" Kyabe baki tayi tace "Toh don ma ka samu ina tashin ka?" Ta wani juya ido ta juya xata fita ya bi ta da kallo, sai kuma yace "Ina son ruwan zafi" Ta jefa masa wani kallo tace "Toh meye zaka gaya min? Ko house help dinka ce ni?" Daga haka ta fice daga dakin, lumshe ido yayi yana son tashi amma ba shi da enough strength din yin hakan, bayan kusan minti ashirin har wani baccin ya kara daukesa ta shigo dakin rike da kettle din ruwan zafi, ya bude ido da sauri jin sound din bude kofar, bandaki ta shiga ta dauraye bucket ta juye masa ruwan zafin a ciki tana fitowa kuma ta fita daga dakin ba tare da ta kallesa ba, ya yunkura ya mike zaune sannan ya sauka daga saman gadon ya shiga bandakin. Ko da ya fito yaga abinci ajiye a dakin, ya gama shiryawa yayi sallahn zuhur, yana ta zaune saman darduma yana kallon warmers din abincin, can ya jawo karamin warmer din ya bude aroma din miyan ya doki hancinsa, ya bude dayan ya ga shinkafa ce, kawai zuciyarsa ya basa ai aiko mata da abincin aka yi ya kulle ya matsar daga kusa da shi. Har aka yi la'asar Nihad bata sake shigowa dakin ba, zuwa lkcn he is feeling much better, fitowa daga daki yayi ya ganta kwance kan 2 seater tana bacci, ya karasa cikin parlon, a hankali ya kai hannu ya buga kujeran, ta bude ido da sauri zata kwala ihu ta gansa, don duk tunaninta aljanin daren ne ita ma ya zo mata, Ya dauke idonsa daga kallonta yace "Sallah" Tace "Ina ruwanka?" Bai ce komai ba ya juya ya koma daki, karamar wayarsa ya dauka ya zauna gefen gado yaga miss calls din Nadeeyah har hudu sai kuma miss calls din Abba biyu, sannan message na debit din dubu ashirin da biyar bayan debit din drugs da ta siyo masa da safe, yana ta kallon debit din sai kuma ya mike ya fita daga dakin tana zaune kan kujera yana kallonta yace "Me kika min da dubu ashirin da biyar?" Ta kyabe baki tace "Toh kaza naje na siya na dubu goma nayi girki don ni baxan dinga cin abinci lami ba, bayan nasan Abbana na baka har da kuɗin nama, dubu biyar kuma na siyo spices, dubu goma kuma na zuba mai a mota, idan ma kudin account din ne suka kare ai sai ka kirasa kace sun kare" Kallonta ya dinga yi, ta ɗan kallesa ta gefen ido, sai kuma ta turo baki ta mike ta wuce dakinta ya bi ta da kallo, komawa cikin dakin yayi ya kara bude abincin da tace tayi yana kallo, har cikin ransa bai yarda ita tayi girkin ba duk da bai ci ba, can dai ya dau spoon yayi tasting stew din, nan ya kara tabbatar ma kansa ba ita tayi ba, duk da yunwan da yake ji bai ci abincin ba. Da magrib bayan ya fito daga masallaci ya ga almajirai biyu ya tsayar da su sannan ya shiga cikin gidan ya fito da abincin ya juye masu ya koma kitchen ya wanke warmers din ya fito, daki ya shiga ya dauko makullin mota da atm card dinsa ya bar gidan, tana jin ya fita ta fito balcony da sauri ko gama goge jikinta bata yi ba don wanka take taji ya kunna mota ta kwara ruwa kawai ta daura tawul ta fito da gudu, Hijab dinta da ta fizgo ta saka a kan tawul din, duk a tsorace take da gidan tun da taga gari ya fara duhu dama hankalinta ya tashi, can saman dakalin da yake zama ta tafi ta zauna hawaye cike idonta, ta fi awa daya wajen zaune ga uban sauro dake ta cizonta har da guntun gyangyadinta, sai bayan isha ya shigo gidan, bayan yayi parking ya tafi ya kulle gate ya dawo yana kallonta amma bai ce mata komai ba, juyawa yayi ya shiga cikin gidan ta bi bayansa da sauri cikin kuka tace "Ni wallahi kar ka sake fita ka barni ni kadai cikin gidan nan da daddare, don baka ga abinda ya faru da Husnah bane har ta bar gidan shi yasa zaka wani tafi ka bar ni kadai kuma ka tafi da makulli" Ya juya ya kalleta yace "Wacece Husnah?" Ta hade rai tace "Kawata da ta zo gidan nan ta kwana mana" Yace "Ohhh ta tafi ne?" Nihad tace "Aljanun dare ne fa suka zaneta fuskarta duk ya kumbura shine ta gudu" Yace "Au haba?" Ta wani daure fuska tana kallonsa, yace "Toh Allah ya sa kar su dawo kanki tunda ita ta gudu" Yana fadin haka yayi hanyar dakinsa ta bi sa da gudu ta fashe da kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, me yasa zaka ce min haka? Me nayi masu ni za su dawo kaina?" Yana shiga dakinsa ita ma ta shige tana kallonsa tana maida numfashi hawaye cike idonta, duk a mugun tsorace take, yace "Malama kwanciya xan yi ki tafi dakinki sai da safe" Ta wani gwalo ido tana kallonsa, sai kuma kawai ta nufi can karshen gadon dakin ta zauna, ya tsaya yana kallonta sai kuma yace "Ohk, sai in bar maki dakin in koma wancan" Bata san sanda ta fashe da kuka ba tace "Don girman Allah kar ka barni ni kadai wallahi tsoro nake ji kuma
Chapter 121 · 0% Book details