← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 147 OF 165

Sashe 147

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba, Aunty Maryam tace "Me yasa kace admission letter xata amsa a garin nan bayan ba haka bane?" Sai da khalil yayi stiff a inda yake zaune, Aunty Maryam tace "She told me her dad sent her away from his house" Sosai gaban khalil ya fadi jin abinda Aunty Maryam ta kara cewa, shikenan ya ma san ta riga tace an masa aure da ita tunda har ta iya buda baki tace an koreta a gida, jin tayi shiru Khalil yayi karfin halin cewa "Sai me kuma ta gaya maki Aunty?" Aunty Maryam tace "Iya abinda ta sanar min kenan, sai kuma wanda kai zaka kara min, sannan tace video dinta bata san garin yaya aka mata ba har ya fita.... Na kuma yarda da ita don babu alamar karya a duk zantuttukan ta" Khalil dai kallonta kawai yake, can ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya da ya fahimci iya abinda ta sanar ma Aunty Maryam kenan da gaske, yayi kasa da murya yace "Haka ne Aunty, but bansan ta ina xan fara gaya ma Mami all this ba, ni kuma mahaifinta yayi min halaccin da baxan iya kyaleta ta shiga duniya ba bayan ya koreta gidansa saboda offense din da ba yin kanta ba, her stepmom is behind all that happened to her amma bata sani ba ta kuma ki kwantar da hankalinta ta gano hakan, makira ce matar kuma azzaluma, ta lalata mata rayuwa ta dora ta a kan abubuwa da yawa da basu dace ba, wanda ita nata yaran bata basu wannan tarbiyar ba, duk nutsattsu ne babu na banza a yaranta, farkon faruwan incident din ai mahaifin nata bai koreta daga gidan ba amma matar nan ta san yanda tayi har ya koreta after almost one month da faruwar incident din, and i am telling you ba directly take abubuwanta ba, ni nasan mahaifinta baya cikin hayyacinsa ya koreta daga gidansa, coincidentally kuma nima na masu sallama xan bar gidan kenan in taho Abuja bayan Abba ya kirani, kawai naga baxan iya barin ta tafi wani wajen ba, And you know what Aunty.... bamu ta6a shiri da yarinyar ba duk tsawon xamana a gidan, amma sbda kirkin mahaifiyarta na tausaya mata muka taho nan Abuja tare" Aunty Maryam ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Dangin mahaifiyarta fa?" Ya girgiza kai yace "Babu su a nan" Aunty Maryam tayi shiru cike da tausayin Nihad, can tace "Kai yanzu menene next plan dinka Khalil?" Ya girgiza kai yace "I don't know Aunt, i am confuse, ban san ta yanda xan yi convincing Mami har ta zauna nan zuwa sanda mahaifinta xai huce ba, gashi jiya da daddare ma sai da tace min ta amshi abinda xata amsa yau ta tafi sbda gobe weekend" Aunty Maryam tace "Kar ma kace mata komai don ba lallai ta fahimta ba, kawai dai ko da zata sake maganar admission letter din kace still fa ba a samu ba.... Nihad have to stay here kafin a samu wani solution din gaskiya, she is too young for this trauma at her age, kishiyar uwarta bata mata adalci ba, gashi ni kilan nan da sati biyu xamu yi tafiya" Khalil yayi shiru sai kuma a hankali yace "Aunty to me yasa baxan samar mata admission din ba kawai, sai ta zauna Abujan a zuwan dai karatu take" Aunty Maryam tace "Eh wannan ma shawara ce mai kyau kuwa, amma wani makarantar xaka samar mata?" A hankali yace "Nile or Baze University...." Buda baki Aunty Maryam tayi tana kallonsa da mamaki tace "Did you know the tuition fees of those Universities kuwa?" Ya ɗan yi dariya yace "Ohhh nawa ne ma?? shi su Mimi ke zuwa i think?" Tace "In ba dai ko Abbanku ya hada har ita ya dinga biya ba, tunda kowa ma biya ma kudin makaranta yake ai naga" Khalil yayi murmushi yace "I will process the admission for her as soon as possible in sha Allah" Aunty Maryam tace "Toh Allah ya rufa asiri, kaga dai dai kenan ma tunda sabon session xa su shiga" Bai ce komai ba, Aunty Maryam tayi shiru tana ta nazarin abubuwa iri iri, can ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Yanzu duk wani hanya da xa a bi a gano ta inda wannan video din nata ya fita babu shi kenan? Ai bai kamata ayi shiru babu bincike ba, kamata yayi anyi ta bincike har Allah ya sa a gano wanda yayi wannan ta'asar, duk da babu tantama ni nasan da sa hannun matar ubanta, sannan ina zargin kawayenta ma, don ta gaya min ko su waye" Khalil dai bai ce komai ba, Aunty Maryam tace "Amma tunda har ta iya tashi cikin dare ta kai ma Allah kukanta ni nasan komin daren dadewa wataran gaskiya zai bayyana, ta yanda komai ya faru duk Allah xai nuna ya tona asirin koma wanene, Allah Ubangiji ya kare mana zuri'a ya sa mu fi karfin zuciyarmu" Sai wajen karfe goma Khalil ya sauko downstairs daga parlon Aunty Maryam, Babu kowa parlon kasa ya nufi guess room da Nihad take, ya bude kofar dakin a hankali ya shiga ya ganta kwance tana bacci, for almost 4 days sai yau take bacci peacefully kuma me nauyi, ya karasa cikin dakin yana kallonta, juyawa yayi daga karshe ya fita ya kulle dakin. Ba laifi throughout ranan Nihad ta saki jikinta a gidan Aunty Maryam she really felt at home, Aunty Maryam bata barta ta zauna ita kadai ba, har fita suka yi tare da yamma ta rakata xata yi siyayya a shopping mall sae dai ta bata nikaf ta saka saboda yan kwakkwafi masu gane mutum farat daya, Aunty Maryam ta bata baki sosai a kan kar ta wani damu kanta in Allah ya yarda asirin wa enda suka mata haka zai tonu, kuma xata ga yanda Allah xai yi da stepmom dinta, hakan yasa damuwan Nihad ya ragu sosai ta samu relieve, bayan sun dawo daga shopping Mall din Aunty Maryam ta ware mata nata abubuwan da ta siyo mata ta bata, Nihad ta amsa a hankali tace "Nagode Aunty, Allah ya saka da alkhairi" Daki ta kai ta dawo ta zauna parlon, Aunty Maryam na ba Mus'ab dinta abinci Nihad tayi kasa da murya tace "Aunty don Allah xaki iya ara min wayarki in kira Mumyna?" Aunty Maryam ta dau wayar ta mika mata, Nihad tayi dialing number Mumy sannan ta kirata, lkci daya jikinta yayi sanyi jin wayar a kashe, ta mayar ma Aunty Maryam tace "Wayar a kashe yake" Aunty Maryam tace "Anjima sai ki sake trying" Nihad tace "Toh" Wayar Aunty Maryam ya fara ring ta dauko ganin Mami ce ke kiranta ta daga, bayan sun gaisa Mami tace "Ya ake ciki ta amsa kuwa Maryam?" Aunty Maryam tace "Kinsan sabon session ne Mami, so ina jin sai zuwa next week xa su fara badawa gaskiya, har yanxu bata samu ba kam" Mami tace "Wai wani makaranta ne?" Aunty Maryam tace "Toh ban dai sani ba gaskiya" Mami tace "Toh Allah ya kyauta, amma na so ace ko yau ko gobe ta koma gida" Aunty Maryam tace "Toh tunda Allah bai nufa ba sai mu saurari yanda ya tsara" Mami tace "Yana nan gidan naki ne Khalil din?" Aunty Maryam tace "Aa" Mami tace "Ohk tun safe ya fita naga kuma bai dawo gida ba" Aunty Maryam tace "Kilan yana can gidansu budurwarsa" Mami tace "To a gaida Mus'ab" Aunty Maryam tace "Xai ji" Daga haka suka yi sallama ta katse wayar, Aunty Maryam ta dinga tunanin ta yanda xa su bullo ma yayartata. Aunty Hassana ce xaune bangaren Hajiya Amina tana kallonta rai a dagule tace "Yanzu dai kin kara tabbatar da cewar bayan malaman da fatima ke bi na kasar nan har kasansu ma malamai yi mata aiki suke ko?" Da sauri Hajiya Amina tace "Aa na yarda wallahi...." Aunty Hassana tace "Wai ni yau yaya zai buda baki yace in bar masa parlonsa sbda na kawo masa shawarar kar ya tura Khalil Zanzibar, yaushe har ya dawo gidan balle a san ko ya sauya hali ko bai sauya ba, har zai kara yarda da shi ya daura sa kan miliyoyin kudinsa, kar ki dada kar ki raga shine yaya ya hayyako min har yana cewa in bar masa parlonsa cikin tsawa" Hajiya Amina tace "Toh wai yanzu me malamin yace maki da ku ka yi waya" Aunty Hassana tace "Ta lalata mana aiki, kuma da tsafi aka lalata aikin" Hajiya Amina ta rike ha6a tace "Aikin kusan miliyan daya fa?" Aunty Hassana ta sauke ajiyar xuciyar takaici tace "Wato an bata sa'ar dai dai sanda xata gaya masa ya shigo gidan babu wanda xai hanasa, shine ya shigo kansa tsaye asiri kuma yayi tasiri aka xuba masa ido babu wanda ya dakatar da shi, uban ma ya kasa cewa komai har yanzu shine ya billo da turasa Zanzibar yayi masa business" Hajiya Amina tace "Toh ni ance ba shi kadai ya dawo ba, kuma har yanzu ban ga yarinyar da aka ce ya dawo tare da ba, kinga ai ko yau naje bangaren, kuma har dakin Hajiya Fatiman na shiga kai tsaye ko yarinyar na ciki amma ban ganta ba" Aunty Hassana tace "Farhana tace fa bata gidan, tun da suka gane ita ce me wannan video din na kwanaki ya fitar da ita wai daga gidan, kinga tabbacin tsiyarsa kawai yaje ya tsula a duniya ya dawo, babu tantama kuma karuwarsa ce" Hajiya Amina tace "Wai daxu baki ga uwar yarinyar da ake son makala masa ta zo ba kuwa??" Aunty Hassana tayi wani dariya tace "Ai ko zata mutu baxai auri er ta ba sai dai in har ba Hassana sunana ba, Nadiya take ko wa? Toh wallahi baxai aureta ba, ba dai dukiyar yayana ake hari ba? to sai dai su gani su hanga daga nisa, ita fatima ta zaci ta fi kowa wayo shine take kokarin xata makala masa yar aminiyarta tunda kasarsu daya su hadu su wawushi dukiya ta ko ina su ci karensu ba babbaka, su yi wandaka son ransu su gayyato jajayen danginsu da abokai ayi biki a ci uban kudi, to kuwa xan ga ta yaya, don da dai in bari ya auri yarinyar nan
Chapter 147 · 0% Book details