Sashe 153
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
07087865788 [7/29, 6:34 AM] Abdulkarim Hauwau: Aunty Maryam na kallonsa tace "Saukan yaushe kJay?" Yace "Shigowata kenan, ina yini Aunty" Da murmushi tace "Lafiya lau, ya hanya?" Yace "Alhmdlh" Kallon Mami dake ta kallonsa yayi yace "Good evening Mami" Ta sauke ajiyar zuciya tace "Ka dawo lafiya?" Yace "Lafiya lau" juyawa yayi ya fita daga parlon, Aunty Maryam tace "Ni zan koma gida Mami, ana gobe xan tafi xan kawota nan din da kayanta" Daga haka ta mike tana gyara gyalenta ta nufi kofa tace "Sai anjima" Mami dake ta kallonta ta rasa ma me xata ce mata ta bi ta da ido kawai har ta fita daga parlon. Aunty Maryam na shigowa main parlor din gidan don ita bata yarda ta bi ta bayan bangaren Mami ba tunda ba shakkar yan gidan take ba, taga Aunty Hassana a parlon da er ta Farhana, Aunty Hassana tace "Ashe kina gidan Haj. Maryam" Aunty Maryam tace "Eh fa ina ciki, sannunku da shan AC" Daga haka ta nufi kofa, Aunty Hassana ta bi ta da wani shegen kallo tana kyabe baki, Farhana tayi kasa da murya xata yi magana kawai taga Khalil ya shigo parlon, ko kallon ita da uwarta bai yi ba ya bi bayan Aunty Maryam, Aunty Hasana ta rike haɓa tana biye da shi da ido, wato ya ma daina gaisheta kenan yake nufi??? Farhana ta tabe baki tace "Toh har Mum din Hanan fa baya gaidawa in gaya maki ba ke kadai ba" Aunty Hassana tace "Haka tace min ranan, ki kyaleni da ɗan iska, zan kuma sauke masa abinda ke kansa, shi din banza" Har Aunty Maryam ta shiga motarta amma ganin khalil ta jira har ya karaso, ya jingina da motar yana shafa kansa kafin yace komai tace "Shigo mu je can gidan kawai" Zagawa yayi ya bude daya side din ya shiga ta ja motar, Securities dake bakin gate suka yi saurin bude mata gidan, Sai da suka bar anguwan tace "Uhn na shawo kan Mami da kyar, ko jiran opinion dinta ban yi ba na fito" Yayi kasa da murya yace "Yanzu zata iya zama nan gidan ta dinga zuwa makarantar kenan?" Aunty Maryam tace "Kwarai kuwa, zata zauna nan guess room dake bangaren Mami, kaga bata shiga cikinsu ba ma balle su hantareta ko su tsangwameta, sai ta so ganinsu xata gansu, balle na lura ita ma miskila ce ta bala'i gashi ya hade mata da nukurci" Murmushi kawai khalil yayi, Aunty Maryam tace "Kaga ko Murja bata wani sake ma komin surutun da yarinyar take janta da shi, tana da aji sosai" Calmly Khalil yace "To ta fi haka da kika ganta, wannan abinda ya faru da ita ne ya ɗan fara koya mata hankali, dalilin sanyin nata kenan, but..." Sai kawai yayi murmushi bai ce komai ba, Aunty Maryam tace "Allah sarki, dama kace bakwa shiri ai duk zamanka gidan..." Yace "Yeah, ni kinsan bana daukan raini, so tana ji da girman kanta nima ina ji da nawa, i just use to forget she exit in the house, beside she's her dad's favorite" Dariya Aunty Maryam tayi tace "Ikon Allah, kai da kake ra6e gidansu kuma kake mata girman kai?" Er dariya Khalil yayi yace "I don't want to talk about that Aunty, amma da stepsister dinta kawai muke shiri, her name is Nihal she is nice" Aunty Maryam tace "Allah sarki, wato she being her dad's favorite shine aka hada mata wannan tuggun saboda bakin ciki" Khalil yace "Yea, tunda kinga ita kadai ke zuwa Maryam Abatcha a gidan, and komai take so shi ake mata komin tsadarsa, ban ta6a ganin mace me kissa irin stepmom dinta ba, she really got them, komin abunki baxa ki ta6a gano cewar ba sonta take ba, at first i thought ita ta haifeta yanda take tsaya mata a kan komai kamar gaske" Aunty Maryam ta girgiza kai cike da tausayin Nihad tace "Allah sarki, Allah Ubangiji ya gaggauta saka mata, Allah ya tona asirin duk masu hannu a wannan abun, Allah ya walakanta su tun a nan gidan duniya kowa ya shaida" Khalil dai bai ce komai ba, Aunty Maryam tayi shiru sai can tace "Dama akwai wata makociyarmu a can Yemen, nasan kai baxaka ganeta ba tunda yaushe rabonka da can ina jin tun kana 20 years, matar tana da wani yaro bai wuce ka a shekaru ba, yana fita kasashe ne, mugun mai kudi ne yaron, ya sha zuwa Nigeria kuma idan ya zo har nan gidana yana zuwa, bai ta6a shigowa kasar nan bai zo gidana ba, mun dai zama kamar yan uwa, wajen Mami ne kawai baya zuwa saboda securities din nan naku na jaraba tun daga farkon unguwa, wallahi yaron nan Ayman a ko da yaushe burinsa in samar masa mace yar Nigeria Hausa fulani ya aura, gashi fa ko hausar ma shi baya ji sai turanci da larabci, da nayi ma Mami maganar Noor tace min a'a bata son tayi nisa da ita, ni kuma kaga su Zeenah basu isa ayi xancen aure ba su ma kuma babansu naga kamar baxai so suyi nesa da shi ba, banda haka da xan basa su koma can gida tunda kakarsu na can ai, ai sun ma fi rike aure, To kuwa wallahi tun da aka yi haka xan hadasa da Nihad in sha Allah, a can kasar waye xai wani san abinda ya sameta ko wani xancen video dinta can?" Kallonta kawai Khalil yake, can yayi dariya yana girgiza kai bai dai ce mata komai ba, tace "Au dariya ma na baka, u think i am joking right? Wallahi i am very serious, kuma ina me tabbatar maka zai aureta saboda ya kwallafa rai sai bahaushiya zai aura, yana aurenta su bar kasar kawai tayi komawarta can gaba daya, dama ita ma tana zubi da larabawan ai" Khalil na Murmushi yace "Gaskiya ne, Allah ya rufa asiri" Aunty Maryam tace "Ameen, ina komawa gida da daddare xan yi chatting dinsa up, har hotonta idan ya kama sai in tura masa gobe, ai ɗa na kowa ne bawa sai mai shi, in sha Allah sai Allah ya daukakata ko don saboda wannan jarabawan da take kan ci" Khalil ya kalleta yace "Toh amma ai kya bari ta samu karatu ko Aunty?" Aunty Maryam tace "Aa xata yi karatunta confirm, idan kuwa ya shirya auren yanzu kawai ya aureta idan sun je can ya samar mata makaranta, mu ma duk ba can muka yi karatun ba" Khalil na gyada kai yace "Haka ne" Aunty Maryam tace "Yauwa, kaga ta haka har zuciya sai stepmom din nata ta hadiya saboda bakin ciki, bayan asirinta ya tonu kenan a idon duniya" Khalil dai bai kuma cewa komai ba har suka iso gidan Aunty Maryam, tana parking ta sauka shi ma ya sauka, Nihad ta fito tare da Mus'ab dake wajenta tun fitar mamarsa, tayi masa wanka ta canza masa kaya, yana jin motar uwarsa ya fito compound da gudu zuwa wajenta, Nihad dai na tsaye bakin kofar parlon, ko lura da Khalil din ma bata yi, shi ko tunda yayi mata kallo daya yaga wani haske da tayi, wanda dama shine ainahin haskenta, wahala da tashin hankali ne ya boyesa, Aunty Maryam na rike da hannun yaronta bayan ta tambayesa wa yayi masa wanka ta nufi kofar parlon, Khalil ya bi bayanta, sai a sannan Nihad ta gansa, Nihad na tsaye har Aunty Maryam ta Karaso ta yi mata sannu da zuwa, Aunty Maryam tace "Yauwa gwara da kika masa wankan kafin in dawo don da baxai yarda ba, hope kun gama girkin?" Nihad tace "Ehh mun gama" Aunty Maryam ta shiga parlon, Nihad ta kalli Khalil daga sama har kasa ta juya ta bi bayan Aunty Maryam, da mamaki ya bi ta da kallo yana tsaye, Aunty Maryam ta juya ta kalleta jin bata ji ta gaidasa ba tace "Kin gaishesa kuwa Nihad?" Ta ɗan yi yake ta juya da sauri ta kallesa tace "Ohh, ban gansa ba, ina wuni" tana fadin haka da sauri ta bar wajen ya bi ta da ido, Aunty Maryam dai ta zauna parlor tana amsa gaisuwar Murja, ya karaso cikin parlon ya zauna, tuni Murja ta tafi kawo masa ruwa da lemo, Nihad kuma dama dakin da take tayi wucewarta, Aunty Maryam na kallonsa tace "Wallahi har ka kara wani fresh fitar nan da kayi kwana biyu, halan sanyi ake a kasar?" Ya ɗan yi murmushi kawai ya dau bottle water ya bude yana sha, sai kuma ya ciro wayarsa ya shiga number Mumy yayi dialing, tunda suka zo Abuja yake kiranta baya samunta, luckily yanzu ya shiga, tana dagawa ya gaisheta, yayi mata ya jiki sannan ya tambayeta su Sudais, daga haka yace "Bari in ba Aunt dina ku gaisa" Mumy tace "Toh..." daga haka ya mike ya kai ma Aunty Maryam wayar, suka gaisa, nan Mumy tayi mata godiya sosai kamar tasan issue din da ake kai, Aunty Maryam tace "Ahh ba komai Hajiya ai ɗa na kowa ne, ke dai ki kwantar da hankalinki in sha Allah komai xai daidaita, kawai kiyi ta bin ta da addu'a domin kuwa addu'an ki gareta baxai ta6a faduwa kasa ba, Allah Ubangiji ya rufa mana asiri ya kara daura mu akan makiyyanmu" Mumy taji dadin wannan furucin na Aunty Maryam, nan kuma ta kara jin hankalinta ya kwanta ta samu relieve, suka yi sallama Aunty Maryam ta mika masa wayar, ya amsa Aunty Maryam tace "Ka ba Murja ta kai mata wayar su gaisa ko yau tayi trying kiranta da wayana bai shiga ba" Khalil ya mike ya nufi dakin da Nihad take, ko kwankwasa kofar bai yi ba ya bude, ta juya da sauri don ko Aunty Maryam kafin ta shigo tana mata Knocking haka ma Mus'ab ko mai aikin gidan, ta ci gaba da game din da take a Ipad din Mus'ab, ya karaso cikin dakin ya sake dialing number Mumy yana fara ring ya mika mata wayar, ta amsa tana kallon screen din ganin Number Mumy ta kai kunne da sauri, you can tell how happy she is da take magana da Mumy, Mumy ma ta kara samun nutsuwa jin how lively her daughters voice is, Nan dai Mumy ta kara mata