← Book details Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 165

Sashe 106

Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ledan dake saman gado ta dinga yi, kafin ta karasa ta bude ledan, abaya ta gani masu ɗan karan tsada sun kusa kala goma, da mamaki ta dinga kallonsu tana warwaresu, sannan ga undies da cream din shafawa da turarurruka duk a cikin katon ledan, da sauri ta fito parlor tana kallonsa tace "A ina ka samu kudi ka siya min abayan nan?" Ya kalleta a takaice yace "Kudin babanki mana" Nihad tace "To amma wa ya zabo abayan?" Yace "Ni ɗan aike ne, kasuwa kawai aka aike ni naje na amso" Ta kyabe baki tace "I thought as much" Daga haka ta juya ya bi ta da kallo har ta shiga daki, wani Murmushi yayi ya maida idonsa kan tv da yake kallo. Bayan ta yi wanka ta shirya cikin daya daga abayan, sosai yayi mata kyau ya amshi fatarta, ba laifi haskenta ya fara dawowa amma ramar na nan, ta fito parlor, kallo daya yayi mata ya dauke idonsa, ta wuce kitchen sauran abincin da Nihal ta dafa daren jiya ta kara dumamawa ta xuba ta koma daki ta ci, har kusan la'asar Nihad na ta xuba ido taga ko Umma xata zo yau din ko sai gobe, amma bata zo ba, wajen karfe biyar ya bude kofar dakinta yace "Ki sameni a mota" Da ido ta bi sa har ya bar wajen, sai kuma ta mike ta dau mayafinta ta bi bayansa, duk da yana cikin motar ta ki shiga, she can't take that risk anymore, tana kallonsa da kyau tace "Ina za mu je?" Yace "Gidanku" Ta ɗan yi jim, sai kuma dai ta shiga bayan motar ta kulle, suna barin gida taga sun dau hanyar gida, ta ma rasa ko farin ciki xata yi ko akasin hka, the only good thing of going to that house is that xata ga Umma bayan nan ita bata marmarin ma zuwa gidan.... Sai da suka kusa yace "Ki bude kunnuwanki ki saurareni da kyau, zan kai ki gida ba don komai ba sai don ki gaida mahaifiyarki da bata da lafiya, idan Abba na nan shi ma ki gaishesa, bayan haka xa mu fito daga gidan..." Da mamaki Nihad tace "Kana nufin sai in shiga har gidanmu in fito ban je bangaren Umma na gaidata ba??" Dai dai nan suka shigo layin, yana kallonta da kyau ta madubi yace "Ba don ki je bangarenta ki gaidata na kawoki gidan ba, a duk inda kika hadu da ita a nan xaki gaisheta babu xancen xuwa ɓangarenta, idan kuwa kika ce baxa ki bi umarnina ba, Billah na maki alƙawarin muna fitowa daga gidan xan maida ke garinmu da zama na har abada" Shiru Nihad tayi bata ce komai ba, bayan yayi parking yace "Kin ji ko baki ji ba?" Ta hade rai tace "Na ji" Bude motar yayi ya sauka ita ma ta sauka fuska daure, har sannan dingishi take, Aminu kamar xai goya Khalil tsabar farin cikin ganinsa, Nihad ta kara tsuke fuska ko kallonsa bata yi ba ta shige cikin gidan, Aminu yayi kasa da murya yace "Ciwo ta ji a kafar take dingishi?" Khalil yace "Zan fito yanxun nan" Daga haka ya bi bayan Nihad, Umma ta fito daga bangarenta kenan ganin Nihad ta hau tafa hannu tana cewa "Oyoyo oyoyo" Nihad ta ɗan saci kallon Khalil dake bayanta yana kallonta, ta sunkuyar da kai a hankali tace "Umma ina yini" Umma tace "Karaso mu shiga ciki daughter" Nihad tayi karfin halin cewa "Xan shiga wajen Mumy ne tukunna" Umma ta saki baki tana kallonta, tuni khalil yayi part din Mumy, Nihad ta bi bayansa kamar xata yi kuka, haka Umma ta bi su da kallon mamaki, kai ko makaranta Nihad ta dawo ba wani lallai taje bangaren Mumy ta gaidata ba, Umma kuwa dama kafin ta fita sai ta shiga ta gaya mata ga inda xata, haka kuma idan ta dawo, abinda Nihad tayi yanxu sai yayi mugun daure ma Umma kai. Nihad ta kasa hada ido da Mahaifiyarta bayan sun shiga parlon, Mumy ta amsa gaisuwar khalil da fara'a, Yace "Ya karfin jikin?" Tace "Alhamdulillah jiki da sauki" Nihad na wasa da veil dinta tace "Mumy ya jikin?" Mumy dake kallonta tace "Alhmdlh" cousin din Mumy ce ta fito daga bedroom suka gaisa da khalil cikin mutuntawa, Nihad dai sae kallonta take, ganin ta juya ta koma daki ba tare da ta bi ta kanta ba, Nihad ta mike a sanyaye ta bi bayanta, gaisheta tayi, maimakon ta amsa sai ta hau ta da fada, tace "Ban kara tabbatar da cewa ke mahaukaciya bace shashasha sai yanxu, ace uwarki ba lafiya tun da kika bar gidan nan amma kika rasa inda xaki samu wayar kiranta? nan kuwa a duk sanda matar nan Umma ta shigo sai tace ai kunyi waya, anya kina son gamawa da duniya lafiya kuwa Nihad? Kullum bawan Allahn nan sae ya shigo gidan nan gaida uwarki amma sbda ke ba yar halaq bace baki ta6a cewa xaki biyosa ki duba jikinta ba, to duniya ce dai wanda bai zo ba ma jiransa take, idan kuma Umma ce tayi nakudarki ta haifeki xa mu ji" Nihad ta zauna hawaye na sauka idonta tace "Aunty ni tsoro nake ji shi yasa ban kirata ba, kuma wallahi bai ta6a ce min xai zo nan ba ban biyosa ba" a fusace Aunty Zulai tace "Sai yace maki xai zo?? Shashasha kawai kin bi kin ja mana abun kunya a duniya wanda har yanzu kukan wannan mugun abun naki muke, wallahi sai nan gaba xaki yi kukan gaske da hawayenki a kan wannan video din Nihad, nan gaba xaki san illar da kika ma kanki a duniya a kan video din nan, kuma yau da ace wannan mijin naki iyayensa da danginsa yan boko ne ko a cikin gari suke wllh baxa su ta6a bari ya aureki ba ko da kuwa shi ya ganki yace yana so balle wannan manna masa ke kawai aka yi sbda babanki ya yaba da hankalinsa, amma da ace ɗan birni ne wllh gori wajen danginsa da yan uwa ma kawai ya isheki ki hadiye xuciya ki mutu wataran, kina ganin kamar abu ya lafa ai shkkn an manta, yarinya sai nan gaba xaki gane abinda nake gaya maki ba yanzu ba, don haka in zaki rungumi mijinki ki bisa ki masa biyayya ki lallaba aurenki, to gatanki, idan kuwa kin ce ba haka ba kika kuskura kika bari aurenki da bawan Allahn nan ya samu matsala to idan ba kauyen ubanki xai sake komawa ya samo maki wani mijin ba ina me tabbatar maki babu wanda xai aureki don ma in gaya maki ki ji da kyau" kuka kawai Nihad take tana kallonta, Aunty Zulai tace "Shikenan ni abinda xan gaya maki kenan, tashi ki bani waje" Nihad ta mike tana goge hawayen da ya ki tsaya mata ta fito parlor kanta a kasa, zaunawa tayi saman Carpet ta dago kai a hankali ta kalli Mumy taga kallonta take, cikin sanyin murya tace "Mumy ina su Sudais" Mumy tace "Sun tafi makaranta" Nihad bata kuma cewa komai ba, bayan few minutes Mumy tace "Kin ga wancan bawan Allahn dake zaune?" Nihad ta daga kai ta kalli Khalil da Mumy ke nuna mata bata dai ce komai ba, Mumy tace "In har kina son gamawa da ni lafiya to ki zauna lafiya tare da shi, idan kuwa kince ba haka ba, ba baki na maki ba amma baxa ki ta6a ganin daidaituwar lamarinka ba, don haka kika kuskura kika kashe auren nan naki sae dai ki nemi warce ta haifeki ba ni ba" Nihad ta fashe da kuka sosai tana kallon Mumy, shi dai Khalil bai iya ya daga kai ya kallesu ba, Mumy ta kallesa tace "Ku gaida gida Ibrahim.... nagode sosai, xan shiga ciki" Yana kallonta cikin sanyin murya yace "Allah ya kara lafiya" Ta amsa da Ameen ta mike ta shiga dakinta, kuka kawai Nihad take kamar ranta xai fita a parlon, bayan few seconds Khalil ya mike ya fita daga parlon, mikewa ita ma tayi tana kuka ta bi bayansa.
Chapter 106 · 0% Book details