Sashe 10
Ni haad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
aka sake bude kofar, har sannan Abba na tsaye speaking with the man, su uku ne duk sanye da hijab din islamiyya har kasa, Abba ya kallesu, sai kuma yace "Ke xaki yi driving din?" Tace "Eh Abba ga makullin" Amsa yayi ya mika ma mutumin dake durkushe gabansa yace "Ka ajiyesu a makaranta, xan jira ka har ka dawo" Ya amsa da ladabi yace "Toh Alhaji" shi ya fara sauka Balcony din, Autan Mumyn Nihad da ake kira da Sudais yace "Abba is he our new driver" Abba yace "Yes he is sweetheart" Duk suka yi ma Abbansu sallama suka sauka xuwa parking lot, sai da suka tsaya dai dai motar xuwa makarantarsu sannan drivern ya nufi motar shi ma, bayan ya bude duk suka shiga back seat, ya shiga ya tada motar yana warming, shi dai Abba na tsaye balcony har sannan yana kallonsu, Drivern na warming motar yaji ance "Ina kwana" ya daga kai yana kallonta ta madubi da mamaki, sai kuma yace "Ina kwana" Bayan wasu yan mintuna ya ja motar suka bar gidan xuwa islamiyyan nasu with Fadil and Sudais directing him. Parking yayi bakin gate din islamiyyan, Nihal ta bude motar ta sauka su Fadil ma duk suka sauka, bayan ta kulle motar ta kallesa tace "Sai anjima" Yace "Sai anjima Hajiya" Suka shiga makarantar, reverse yayi ya bar wajen har sannan bai daina mamaki ba. Yana isa gidan bayan mai gadi ya bude masa gate ya shiga yayi parking ya kashe motar ya sauka, gun mai gadin ya nufa ya xauna, Mai gadin yace "Inji ka yi kumallo dai?" Driver yace "Aa" Mai gadin yace "Toh bari inyi ma mai aikin gidan magana in amso maka" Daga haka ya nufi backyard din gidan xuwa kofar kitchen dake baya, Drivern dai na xaune yana ta juya makullin motar hannunsa sai ga mai gadin ya dawo da plate din dankali da kwai da kofin shayi, ya amsa yace "Nagode sosai" slice din bread ne biyar a gefen irish din da kwai wanda aka matsa ketchup a gefe shi ma, irish din ya fara ci yana dangwalawa da ketchup din, Mai gadi yace "Amma xaka dinga tafiya ne da daddare ka dawo da safe ko gidan nan xaka tsaya?" ya kallesa yace "A ina xan tsaya a nan din?" Mai gadi yace "Ka ji ka, Yo ai har Habibu ya gama yayinsa a gidan nan kafin Alhaji ya bude masa shagon da ya bude masa na tayoyi a gidan nan yake komai nasa, duk tare muke, ga can boyis kwata, su Saminu da Shafi'u masu gyaran pulawa da sharan tsakar gida da Isiya me wanki da guga ai a nan suke duk" ya dau cup din shayin ya kurba yace "Dakin babba ne?" Mai gadin yayi dariya yace "Wai daki, to har parlor akwai a ginin, sannan dakuna uku ne ko wanne da bandaki, kai har ma da kitchen a nan din" yace "To shikenan" Aminu mai gadi yace "Kai ma kayi xamanka kawai a nan xa ka fi gane kan albashin naka, kaga babu xancen kashe kudin abun hawa xuwa da tafiya sannan xa a ciyar da kai a nan ba sae ka siya komai da neran ka ba, duk abinda yan gida suka ci a nan shi mu ma muke ci" Shi dai bai ce komai ba ya gama cinye irish din tass sannan yace "Toh xan xauna nan din in sha Allah, nagode da kulawa" Ganin ya ajiye plate din Aminu yace "Ya haka, naga baka ci kwan ba? Yanxun nan fa ta soya maka" Ya girgiza kai yace "Bana so" Aminu ya dau plate din yana kokarin cin kwan yace "Allah sarki, wasu haka suke basa cin kwai sai suce yana masu karni, mu dai kam ko danyensa ne baxa mu ki ci sha ba, wa yaƙi dadi" Sai da Aminu ya cinye kwan ya mike yace "Mu je ka ga Boyis kwatan" shi ma ya tashi, yana biye da shi, suka tafi far end of the main building in which stood a Beautiful Chalet, mai gadi ne ya fara shiga, shi ma ya cire takalminsa bakin kofar shiga Chalet din kamar yanda mai gadin yayi sannan ya shiga ciki, ba laifi parlon na da girma, sannan ga kujeru har ma da tv, kaya ne ko ta ina a parlon ga wani tashi da parlon yake, everywhere looks very untidy, isiya ne tsaye parlon yana ta faman guga a ironing board, Aminu yace "Ashe kana ta guga shi yasa baka fito ba, ina Saminu?" Isiya dake ta kallon wanda Mai gadin ya shigo da yace "Suna can daki" Aminu yace "To ga bako, kun samu karuwa a nan, shine ya maye madadin Habibu a gidan nan yanxu" Mutumin ya gaida isiya, isiya ya amsa yana ci gaba da gugansa, Aminu na kallonsa yace "Mu je ka xabi dakin da xaka xauna ko" Isiya yace "Ka dai san dakin dake daga dama ni ne a ciki, na hagu kuma Saminu, wanda ke jikin na hagun Shafi'u ne a ciki" Shi dai kallonsa kawai mutumin yake, Aminu dake kallon Isiya shi ma yace "To ya xa ayi kenan" Saminu da Shafi'u ne suka fito daga dakunan su, Isiya yace "Toh ai parlon ma na da girma sai kawai ya maida nan din wajen kwanansa ko" mutumin ya gyada kai yace "Ohk to shikenan" Isiya yace "Yauwa" Aminu ya kalli su Saminu yace "Sabon direban gidan ne shi ma kuma nan xai xauna, sunansa Ibrahim kun ga sunan Alhaji ne...." Saminu yace "To sannun sa da xuwa" Tuni ya juya ya fita daga parlon ya bar mai gadi, Aminu na ganin haka ya bi bayansa da sauri... Suna tafe mai gadi yace "Amma kasan da nauyi mu dinga kiran sunan Alhaji gatsau, baka da wani sunan ko inkiya da xa mu iya dinga kiranka da?" kallonsa yayi yace "Khalil Mahaifiyata ke kirana" Aminu yace "Allah sarki, to ai mu ma sai mu ce khalil din, suna me dadi kamar na larabawa wllh" Bayan sun koma mazaunin mai gadi sun zauna, Mai gadin ya kallesa yace "Yanxu kawai kayayyakin ka xaka je gida ka debo, aikin naka ma fa ba wani me wahala bane, kaga yan makaranta motar makaranta ce ke xuwa daukansu da safe, Yan matan nan biyu kuma daya a zaria ma take karatu, dayar ce ke karatu a nan, ita warce ke karatu a nan din sai ta kai karfe biyu ma bata tafi makarantar ba, Alhaji kadai xaka ajiye karfe tara gun aikinsa, ban ki ba dae Nihad don gantali gareta kamar ta ci kafar kare, kuma sae ta fake da makaranta, a takaice dai kai Alhaji wajen aikinsa da safe shine ainahin aikinka sauran duk masu sauki ne" Khalil da har ya gaji da surutun Aminu ya gyada masa kai kawai, for the next 30mins Aminu bai yi shiru ba, Khalil har ya daina tanka masa don ya ma yi nisa a tunanin da yake, dai dai nan Alhaji ya fito, Mai gadi yayi kasa da murya yace "Da alama yau baxai je motsa jikin ba kenan tunda har gashi sha daya ta yi" Sai kuma ya mike, Khalil ma ya mike yana kallon Alhajin a bit surprised at who is standing next to him, Khalil yayi kasa da murya yace "Yan makarantar har sun taso ne?" Mai gadi ya kalli Khalil da sauri yace "Ka je yana maka magana ne" Khalill ya nufi Alhajin da hanzari, Alhaji yace "Mu je xaka ajiye mu 3 streets away from this" Khalil yace "Toh" Motar da yayi parking bayan ya ajiye yan makaranta ya nufa, Abba yace "Wancan motar ba wannan ba" Khalil ya tafi gun motar da Abba ya nuna masa, Bayan sun fita gidan Mai gadi ya kulle gate, driving Khalil yake a hankali, lkci lkci yake kallon Nihad dake zaune bayan mota da Abbanta tana danna wayarta. Ganin Khalil a layin da Alhajin yace ya ajiye su, Alhaji Ibrahim yayi mamaki sosai, don shi ya ma mance ba Habibu bane ke jan sa, bai yi masa kwatancen inda xai kai su ba ya dai ce masa 3 streets.... Ganin yayi slow down Alhaji Ibrahim yace "Noo ci gaba da tafiya, gida na uku xaka tsaya" Dai dai gidan Khalil yayi parking, Alhaji yace "Kayi horn kawai" yana yin horn mai gadi ya leko ganin motar ya koma ya bude gate din da sauri, Khalil ya shiga ciki ya samu waje yayi parking , Alhaji Ibrahim yace "Maa sha Allah, kayi jirana har in fito" Khalil yace "To Alhaji" Nihad ta sauka ta daya side din wayarta kare a kunnenta, Alhaji Ibrahim ya sauka ya nufi entrance din gidan, Ta side mirror Khalil ke kallonta amma sai yaga kamar wannan fara ce ai, Nihad dake ta xagaye da waya a kunnenta da sunan she is making call, whereas she is not kawai bata son Abba yace su shiga ciki tare ne, tana ganin Abban nata ya shiga gidan ta turo baki ta tafi can karkashin wani Thatch dake compound din wanda aim dinsa wajen shan iska, xaunawa tayi a wajen. Khalil ya sauka daga cikin motar ya tafi gun mai gadin gidan suka gaisa, Mai gadin na kallonsa yace "Ko kai ne madadin Habibu" Khalil yace "Eh nine" Mai gadin yace "Maa sha Allah" Xaunawa khalil yayi yana bin compound din da kallo, wanda shi ma yayi haduwan karshe, ya d'an juya ya kalli Side din da Nihad take, she was so engrossed with what she is doing on her phone....